Gobara Ta Halaka Miji Da Mata A Jihar Kebbi

Gobara Ta Halaka Miji Da Mata A Jihar Kebbi

Daga Sani Twoeffect Yawuri

A daren laraba data gabata ne  aka sanu tashin gobara a wani gida dake tashar Kattai a  cikin garin yawuri dake jihar kebbi, wanda yayi sanadiyar mutuwar miji da mata, kuma Allah ya tseratar da Ɗan ƙaramin yaron su.

Gobarar dai ta tashi a dakin marigayi malam Babangida da matar sa Balkisu a tsakiyar dare, misalin karfe 02:00Am na dare,  inda shida mai ɗakin sa sukayi kokarin fita daga Cikin wannan dakin, sai dai wutar ta rinjayesu, Amma cikin ikon Allah da yardar sa sun samu nasarar kuɓutar da ɗan karamin yaron su inda suka turo shi ta tagar dakin da yakama da wutar 

Tuni dai akayi Jana'izar su kamar yadda addinin musulunci ya tanadar anan Garin Yawuri dake jihar kebbi.