Gishirin lalle ya yi sanadin mutuwar   mutum 22 a Sakkwato 

Gishirin lalle ya yi sanadin mutuwar   mutum 22 a Sakkwato 

Gishirin lalle ya yi sanadin mutuwar   mutum 22 a Sakkwato 

 

Daga Nasiru Bello
 
A ranar Assabar data gabata mutanen kauyen Danzange a karamar hukumar Isa dake jihar Sakkwato sun hadu da waki'ar rasa mutum 22 a lokaci guda bayan sun ci abinci mai guba.
Matar aure biyar  da kananan yara 18 ne suka rasu dukkansu iyalai daya ne, mahaifan  yaran su hudu ne suka rasa su a cikin waki'ar.
Kansilan Mazabar Bargaja Mu'azu Kabiru Lugu amadadin iyalan mrgayan musamman wanda ya rasa matarsa da yaransa hudu waton Hamidu Makeri ya sanarwa Aminiya yanda lamarin ya faru ya ce a ranar Jumu'ar data gabata Matar Hamidu tana dafa abinci a lokacin da take yin miya ta debo gishirin lalle ta zuba a miyar da nufin kara gishiri a miyar ba ta san gishirin kunshi ne ba.

A haka ta kammala abincin ta baiwa yaran gida da matan gida suka ci tare da ita, bayan kammala cin tuwon suka kamu da ciwon amai wanda ya yi sanadin rasa rayuwarsu domin sun ci guba.
"Yankinmu na cikin annobar zawo da amai a lokacin da mutanen suka fara amai muka zaci annobar ce ta kama su, tunaninmu ya sauya a lokacin da suka rasu su 22 dukan a gida daya a lokacin aka bincika aka samu bayanin margayiya ce ta sa gishirin kunshi a cikin abincin da ta dafa abinda ya yi ta rasa kanta da 'ya'yanta hudu da matan aure hudu da sauran yara." a cewarsa.
Ya ce akwai damuwa ga wannan lamarin da bai taba faruwa a yankinmu ba sai yanzu.
"Abubakar Hamidu da Hamza Hamidu da Babba Hamidu da Babba Hamidu ne suka rasa 'ya'yansu, abin da damuwa sosai, sai abu ne da za ka dogara da Allah don shi ne ya kawo waki'ar." in ji Kansila.
Ya godewa shugaban karamar hukumar Isa Alhaji Yusuf Dan'Ali da gwamnatin Sakkwato kan gudunmuwar da suba bayar ga rashin da suka yi na al'ummarsa.

Hamidu Makeri ya ki aminta ya yi magana da wakilinmu domin ya ce ba abin da zai ce kan abin da Allah ya yi shi dai ya dogara ga Allah.
Ya rasa matarsa daya da 'ya'yansa a halin yanzu baya da jini a ban kasa.