Gidauniyar Sarkin Musulmi ta raba Magani ga asibitocin Sakkwato da Kebbi

Gidauniyar Sarkin Musulmi ta raba Magani ga asibitocin Sakkwato da Kebbi

Gidauniyar zaman lafiya da cigaba ta Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ta raba magani domin taimakon talakawa. Kodinetanta na gidauniyar  Sarkin Kabin Argungu Alhaji Muhammad Sama'ila Mera ya raba maganin kawar da ciruta ga asibitocin Sakkwato da Kebbi a wani ɓangare na ba da kulawa ga mabuka.
Sarkin Argungu a wurin kaddamar da rabon maganin a Sakkwato a satin da ya gabata ya ce an samar da magani na miliyan 7.6 don karfafa kiyon lafiya a Sakkwato da Kebbi.
Ya ce Gidauniyar na karkashin kulawar Sarkin Musulmi an samar da ita ne don tallafawa mutane a bangarori daban daban.
"Samar da magani da aka yi domin ganin an cika burin ma'aikatar lafiya ta Sakkwato da Kebbi a ƙoƙarin da suke yi na inganta lafiya musamman mata da kananan yara.
"Mun samu tallafin ne daga MAP International dake Amerika tana ba da gudunmuwa a duk duniya."
Kodinetantan ya godewa gwamnatin tarayya da ta yafe wa gidauniyar harajin shigo da kaya da kuɗin suka kai naira miliyan 254, ya kuma roki jihohin su raba maganin a asibitoci da dakunan shan magani don amfanin wadanda aka yi don su.
Amadadin Gwamnatin Sakkwato babban Darakta a hukumar  kula da harkokin magani da raba su ta jiha Umar Attahiru ya nuna farincikinsa ga abin da gidauniyar ta yi tare da ba su tabbacin yin abin da ya dace da maganin don hanya ce da gwamnati take samanta.