Gidauniyar mu za ta riƙa yaye matasa 1500 a duk shekara---Sameer Salihu

Gidauniyar mu za ta riƙa yaye matasa 1500 a duk shekara---Sameer Salihu
 
 
Gidauniyar SAARG FOUNDATION wadda aka samar domin tallafawa mata, samari da marayu da tsoffi da 'yan makaranta domin samun sana'o'in dogaro da kai ta shirya domin fara koyar da matasa a yankin garin Argungu da Augie ganin yadda akwai giɓi a haujin.
Shugaban Gidauniyar Alhaji Sameer Salihu  a hirarsa da manema labarai ya ce an kirkiro  Gidauniyar ne don samar da aikin yi ga mata da matasa, a kasashen da suka cigaba sun fi mayar da hankali ga cigaban matasa sosai ta hanyar samar musu da sana'o'in dogaro da kai domin bunƙasa tunaninsu ya zama mai amfani.
"Na yi nazari in ba a samu Gidauniyar da za ta yi tsaye kan buƙatun matasa,  aiyukkan laifi za su ƙara  tsananta a cikin al'umma, ganin yadda lamurran rashin tarbiya suke a yanzu cikin Arewacin Nijeriya, aikin yi ne kawai zai rage kaifin aiyukkan ɓarna a cikin al'umma.
"Gidauniyar mu ta samar da cibiyar koyar da sana'a a garin Argungu in da za mu koyar da sana'o'i da dama, mun lura baiwa mutane kuɗi da abinci ba taimako ba ne domin suna ƙarewa a ƙaramin lokaci saɓanin ilmin sana'a da yake cikin kan mutum da zai riƙa samun amfani a kullum har ya baiwa wani tallafi," kalaman Sameer Salihu.
Ya ce sun samar da kayan gudanar da cibiyar a wurin koyar da sana'o'in da za su yi tafiya da zamani a fasali mai tsari, Gidauniyar nada hanyar sayar da kayan da cibiyar ta samar a jihohi da makwabtan ƙasashe.
"A hasashen da muke da shi a duk shekara za mu yaye matasa 1500 a ɓangarori daban-daban na sana'o'in dogaro da kai hakan zai rage fatara a yankinmu.
"Kafin samar da cibiyar mun yaye matasa da yawa a kamfanina dake nan Sakkwato, mu ba mu saka son rai da yaudara da ƙarya hakan ya sa sai da muka shirya tsaf kafin samar da cibiyar," a cewar Sameer Shugaban SAARG FOUNDATION.