Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta koyawa mata Sana'o'in da ba su kayan Sana'a

Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta koyawa mata Sana'o'in da ba su kayan Sana'a

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.

Kwamitin Maida Alkhairi da Alkhairi na Gidauniyar Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Dr Attahiru Bafarawa Garkuwan Sakkwato ta tallafawa Wasu mata da aka horas da Sanaoin daban daban,
Kimanin mata 30 ne Aka Horas da Sanaoin daban daban musamman yadda ake Tuyar kosai, Awara/Akwai da kwai, da Sauran toye toye....

Haka Kuma, an rabawa wasu mata guda Goma Awaki 30 kowacen anbata   Akuya Biyu da bunsuru Daya, da Naira Dubu Goma na Shiga Mota.

 Hon. Sagir Attahiru Bafarawa,  Wanda Alh Ahmad Gyrafshi ya wakilta shine ya kaddamar da rabon kayan inda ya bayyana cewa kowa ce mata zaa bata Awaki 2 da Bunsuru Daya da Dubu Goma yayin da aka baiwa mata 30 kayan Aikin Toye toye da kudin Mota da na Somawa Naira Dubu 20
Hon Sagir yayi bayanin dinbin Ayukkan Kwamitin da manufar Bada Tallafin.

Sarkin Malamman Sakkwato,Prof. Malami Umar Tambuwal,Hon. Maniru Gidan Iguiwa, Shugaban Nacomyo na Sokoto, Hajiya Saudat Ahmad da Abdurrauf Umar duk Sun yabawa Tsohon Gwamnan ,sunyi kira ga Matan da su yi amfani da Tallafin dan inganta Rayuwar su.

Wasu da suka Amfana sunyi Godiya ga duk Mai hannu Wajen wannan Aikin Alkhairi Sun yi Alkawalin baiwa marada kunya.