Gaskiyar Magana Kan Shari’ar Mainasar Da APC a Kotun Koli----Injiniya Aminu Ganda

Jigo a APC ya zanta da Managarciya  kan dambarwar shari'ar APC da Mainasara Sani da aka kammala a kotun koli a satin da ya gabata da kuma yadda karfin jam'iyarsa ta APC yake a jihar Sakkwato.

Gaskiyar Magana Kan Shari’ar Mainasar Da APC a Kotun Koli----Injiniya Aminu Ganda

 

Injiniya Aminu Ganda mutumin Sakkwato ne jigo a jam'iyar APC kwamishina a hukumar da ke nemawa wadanda ruwa suka yi wa barna tallafi a jihohin da suke da Dam Mai samar da wutar lantarki,  tsohon shugan kasa Buhari ne ya samar da hukumar don tallafawa wadan da suka samu jarabawar.

Jigo a APC ya zanta da Managarciya  kan dambarwar shari'ar APC da Mainasara Sani da aka kammala a kotun koli a satin da ya gabata da kuma yadda karfin jam'iyarsa ta APC yake a jihar Sakkwato.

Aminu Ganda kan maganar kotun koli ya ce “a zahirin gaskiya dai wannan karar da aka yi a farko dai wasu ‘yan jam’iya sun so su yi amfani da ita don kawo tashin tashina a APC sai suka tayar da tsohuwar karar da muka  yi watsi da ita bayan uwar jam’iya ta bayar da shedar ba ta san wani shugabanci ba sai na Achida, a wannan lokcin muka ce kowa ya koma gida a yiwa jam’iya aiki a samu nasarar zabe, sai wasu suka bi ta baya suka sanya kara a kotun koli aka fita batunta har ta lalace, da aka sabunta karar a yanzu kuma, kotun ta yi watsi da ita kan haka an kai karshe a shari’ar APC da Mainasara,” a cewar Injiniya Aminu.

Da ya juya kan maganar karfin jam’iyar APC a jiha  ya ce “wanda yake a Sakkwato ya ga canji domin in da aka fito kamar babu gwamnati an ga canji tsakanin jiya da yau ko’ina anata aiki.

“Magoya bayan jam’iyar PDP masu ganin kudin shiga ne ya karu a jiha ake ta yin aiki su fito da alkalumma a gani don a san kudin da Tambuwal ya karba mi ya yi da su rashin abin cewa ne kawai ake nadin tabarmar kunya da hauka.

“Sakkwato gidan jam’iyar  APC ne a tun farko kuma kowa ya san da haka balle yanzu da suka gani a kasa gwamnatin Sakkwato tana aiki tukuru domin samar da cigaba mai dorewa a jiha,” Aminu Ganda ke magana.