GASASHEN KIFI:Mai Tsinke Yawun Magidanta

A kalla dai an samu mintuna 30 ke nan. Sannan a bude a ci daɗi. Za a iya yi wa maigida irin wannan girkin ko don more rayuwa.

GASASHEN KIFI:Mai Tsinke Yawun Magidanta

BASAKKWACE'Z KITCHEN

13122021

GASASHEN KIFI

 
INGREDIENTS
• Kifin karfasa/tarwaɗa
• Attarugu
• Magi
• Takaddar ‘foil’
• Tafarnuwa
• Albasa
• Man gyada
• Kori


 

Yanda ake haɗawa:
A samu kifin tarwaɗa sannan a wanke da ruwan kanwa, ta yadda ƙarnin zai fita tsaf. Sannan a wanke da ruwa. A kunna mukubur (rishon garwashi) ya yi zafi sannan sai a dauki karfen gashi a ɗaura akai.

A yayyyanka albasa da jajjaga attarugu sannan a zuba a daura kifi akan takardar ‘foil’ a daka magi sosai yadda zai ratsa cikin kifin a zuba. Sannan a zuba jajjagen attarugun tare da yankakkiyar albasa a ciki. a barbada garin tafarnuwa kadan a ciki da dan kori. A shafa man gyada kadan a takardar ‘foil’ din kafin a zuba sauran kayan hadin a ciki.

Sai a nada takardar kamar sau biyu zuwa uku. Sannan a ɗora akan wutar garwashi. A bari ya gasu na tsawon mintuna 15 sannan a sake juya ɗayan gefen shi ma ya gasu na tsawon mintuna 15.

A kalla dai an samu mintuna 30 ke nan. Sannan a bude a ci daɗi. Za a iya yi wa maigida irin wannan girkin ko don more rayuwa.

Wannan girkin yana cikin girkin da yakamata mace ta riƙa yi a gidanta domin burge mai gida ta hanyar ƙayatar da kichin naki.



Daga MRS BASAKKWACE