Gangamin APC a Yobe: Mohammed Gadaka Ya Jagoranci Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Cikin Nasara
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Masu hikimar magana sun bayyana samun nasara wajen aiwatar da kowane abu, ta hanyar kyakkyawan jagoranci daga shugaba nagari, wanda ya san makamar aiki, ya san mutanen da yake jagoranta, kana ya san hanyoyin da suka dace wajen tafiyar da wadanda yake shugabanta, a dukanin al'amurran yau da kullum a rayuwar dan Adam. Yayin da akasin hakan ke haifar da tazgaro da rashin dacewa ga inda aka sa a gaba.
Alhaji Mohammed Gadaka, shi ne shugaban Jam'iyyar APC a jihar Yobe, mutum ne wanda ya dade a fagen siyasar jihar, saboda yadda ya rike mukamai ddaban-daban, sannan kuma ya san yadda ake mu'amala da jama'a. Shugaba ne wanda yake da masaniya kan ingantattun hanyoyi da matakan da suka dace abi wajen samun nasara a siyasance da a gwamnatance.
Bisa ga wadannan dalilai na kyakkyawan shugabanci nagari, shugaban jam'iyyar APC a jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka ya shafe ambaton jam'iyyun adawa a duk fadin jihar Yobe. A sauye-sauyen da ya kawo a tsarin tafiyar da APC a Yobe sun yi tasirin da ya rufe bakin tsirarun yan adawar da suka yi saura, inda ciwon mashako ya kama muryoyin su, hasken tauraruwar sa ya shafe nasu- a halin yanzu sun kasa yin katabus, balle wani tasiri.
Tun bayan zabarsa a matsayin Shugaban Jam'iyyar APC a jihar Yobe, Alhaji Mohammed Gadaka bai zauna ba, kullum aikinsa shi ne ina ne ake tsammanin matsala ko damuwa; nan take zai yi hanzari ya tosheta tun kafin ta bayyana. Matakan da suka bashi cikakkiyar damar hada kan ya'yan Jam'iyyar a matsayin tsintsiya madaurinki daya a tafiyar APC a Yobe.
Ba abin mamaki bane dangane da irin jajircewar Shugaban jam'iyyar APC a jihar Yobe yake yi, a matsayinsa na hannun daman Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni; saboda Hausawa sun ce sai hali ya zo daidai a kanyi abota- sanin kowa ne Gwamna Buni hazikin shugaba ne kuma abin koyi a siyasance da salon mulkin al'umma. Wanda sakamakon iya shugabanci ake masa lakabi da 'Limamin Sulhu' a siyasar Nijeriya.
Bisa kyakkyawan jagorancin Alhaji Mohammed Gadaka, a halin da ake ciki yanzu, jam'iyyar APC bata taba samun hadin kai irin wannan lokaci ba, wanda shugabanni da mabiya kowa ya shaidi sauyi da salon da Shugaban ya fito dashi wanda ya hada kan dukanin bangarorin jam'iyyar; shugabanni a matakin unguwanni, kananan hukumomi da na zartaswa a matakin jihar Yobe. Al'amarin da ya gamsar da shugabancin jam'iyyar a kasa baki daya.
Shugabancin Gadaka ba na zaunawa a ofis ba ne ya harde kafa, ko nuna isa da kafafa ga mabiya bane, tsari ne na jin ra'ayoyin kowane dan jam'iyya, tare da bi gida-gida don neman hadin kai ayi aikin da zai kai ga Jam'iyyar ga gagarumar nasara a babban zabe mai zuwa a 2023 tare da dora ingantaccen ginshikin da zai dada karfafar jam'iyyar a matsayin mafi karfin fada aji a Afrika.
Wadannan suna daga cikin sirrin da ya bai wa Hon. Mohammed Gadaka gagarumar nasara wajen gudanar da babban taron gangamin yakin neman zaben da APC ta shirya, wanda ya samu halartar duk wani mai karfin fada aji a jam'iyyar a kowane mataki. A lokacin taron gangamin, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, Shugaban Jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, dan takarar Shugaban Kasa a jam'iyyar, Sanata Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa; Sanata Kashim Shettima hadi da Shugaban Kungiyar gwamnoni jam'iyyar, sun ga abin mamaki, yadda taron ya gudana cikin tsanaki babu wata hayaniya.
Ana iya cewa, Alhaji Mohammed Gadaka ya kafa tarihi a jam'iyyar APC a jihar Yobe, saboda yadda ya hada kan ya'yan ta, a karkashin inuwa daya kuma cikin annashwa da alfahari da salon jagorancin da yake yiwa jam'iyyar, wanda ya zama yar manuniya ga samun gagarumar nasarar zaben 2023- wanda zai zama irinsa na farko a jihar.
managarciya