Ganduje ya tsayar da Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a APC

Ganduje ya tsayar da Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a APC

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tsayar da Mataimakin sa, Nasir Yusuf Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano a jam'iyar APC a zaɓen 2023.

Ganduje ya zaɓi Gawuna ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta jiyo.

Jaridar ta jiyo cewa masu ruwa da tsakin kuma sun amince da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, Murtala Sule Garo, ya zama mataimaki a takarar ta Gawuna.

Majiyar mu ta jiyo cewa da ƙyar masu ruwa da tsaki da wasu manya a jihar su ka shawo kan Garo ya amince da yi wa Gawuna mataimaki a takarar.

Ana ganin cewa Garo, wanda ya ke da iko da jam'iyar a matakin Kananan Hukumomi, shi ne ɗan takarar da mai-ɗakin gwamnan, Hafsa Ganduje ta zaba a matsayin ɗan takarar APC a jihar.