Ganduje Ya Sanar da Ranar Babban Taron APC, Tinubu da Buhari za Su Halarta 

Ganduje Ya Sanar da Ranar Babban Taron APC, Tinubu da Buhari za Su Halarta 


Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Satumba. 
Dr. Ganduje ya bayyana cewa za a gudanar da taron NEC a ranar 12 Satumba, 2024, kuma ana sa ran shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaba Muhammadu Buhari za su halarci taron.
Arise TV ta wallafa cewa Abdullahi Ganduje ya ce ana sa ran dukkanin gwamnonin APC za su halarci taron saboda muhimmancinsa.
Duk da Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai bayyana takamaiman abubuwa da za a tattauna a babban taron ba, amma ya ce batutuwa ne masu muhimmanci. Shugaban ya shaidawa manema labarai a Kano cewa muhimmacin abubuwan da za a tattauna ne ya sa jagororin jam'iyyar za su halarci taron, This day ta wallafa labarin. 
Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa akwai alamun samun nasara a zaben gwamnoni da za a gudanar a jihohin Edo da Ondo.
Ya ce duk da rasa kujerar gwamna da suka yi a baya saboda rikicin cikin gida a Edo, sun yi kyakkyawan shirin kwato jihar.