Ganduje Ya Ba Da Kyautar Miliyan 10 Don Gina Makarantar Islamiyya

Ganduje Ya Ba Da Kyautar Miliyan 10 Don Gina Makarantar Islamiyya
Dr Ganduje

Ganduje Ya Ba Da Kyautar Miliyan 10 Don Gina Makarantar Islamiyya

 Gwamnan Jihar Kano, Drakta  Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci bikin saukar karatun Al-Qur'ani Mai Girma na dalibai 235 na Madrasatul Babban Malami na Madabo har ya ba da tallafin cigaba da aikin makarantar.

Bukin  wanda aka gudanar a dakin taro na GSS Gwammaja dake karamar Hukumar Dala a birnin jiha.
 
Mai Girma Gwamnan ya ba da tallafin kudi Naira miliyan Goma domin cigaba da ginawa makarantar  mazaunin ta na dindindin.
 
Shugabanni da daliban makarantar sun yabawa Gwamnan bisa y dawainiya da harkokin addinin Musulunci musamman a wannan makaranta in da suka masa karramawa ta musamman.