Ganduje Da  Kwankwaso Sun Haɗu A Wurin  Ta'aziya A Kano

Ganduje Da  Kwankwaso Sun Haɗu A Wurin  Ta'aziya A Kano
A wani yanayi na ban al'ajabi a siyasar Kano, a yau Talata, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya kaiwa abokin burmin sa na siyasa, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ziyarar ta'aziyar rasuwar ƙanin Kwankwaso, Inuwa Musa Kwankwaso.
Tun da fari, Ganduje ya yi tattaki har zuwa Ƙaramar Hukumar Madobi domin yi wa dangin Kwankwason ta'aziya.
Da ga nan ne kuma, Ganduje bai zame ko ina ba sai gidan tsohon gwamnan da ke titin Miller a unguwar Bompai da ke birnin Kano, inda nan ma ya yi masa ta'aziya.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a Madobin da gidan Kwankwason na titin Miller,  Ganduje bai yi wani jawabi ba, sai dai kawai ya yi addu'a ga mamacin.
Za a iya tunawa cewa, a jiya Litinin ne  dai Ganduje ya aikawa Kwankwaso saƙon ta'aziya ta sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu.