Home Siyasa Gabatar da rahoton almundahar biliyan 117 da Tambuwal ya yi ya haifar...

Gabatar da rahoton almundahar biliyan 117 da Tambuwal ya yi ya haifar da cece-ku-ce

4
0

Gwamnatin jihar sakkwato a hukumance ta karvi rahoto na kwamitin binciken gwamantin Sanata Aminu Waziri Tambuwal da ta kafa domin tabbatar da adalci da amana da biyar doka.

Kwamitin binciken da gwamnan jiha Ahmed Aliyu kafa ya gudanar aikinsa kusan shekara uku ya yi kiran mutane don gabatar musu qorafin da ake yi kansu da duba qa’idojin harkokin kuxi da aiyukkan gwamnatin da ta gabata ta Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Shugaban kwamitin Alqali Mu’azu Pindiga ne ya gabatar da rahoton bayan shefe tsawon watanni da dama ana sauraren qwaqwaf da binciken muqaraban tsohuwar gwamnatin kan abubuwan da suka yi wanda ya savawa qa’idar dokar jiha da qasa.

Gwamnan Sakkwato amadadin gwamnatin jiha ya karvi rahoton ya yabawa kwamitin kan abinda ya kira adalci da baiwa kowa haqqinsa a lokacin da suke aikin da aka xaura musu.
“Mun samar da kwamitin ne ba don cin zarafin kowa ba, ko don ganin an walaqanta wata jam’iya ko wani mutum guda ba.”
“Lokacin da Allah ya ba mu mulki mun samu kundin bayanai a cikin wani hali da baka iya samun makamar aiki a bisa tsari na aikin gwamnati, ya zama wajibi mu kafa wamnnan kwamitin domin ya duba ya kuma ba da rahotonsa.
“Wannan kwamitin an kaf shi ne domin ya tattaro bayanai ya duba yanda aka yi tu’amali da kuxaxen al’umma, ya haxa kundin tsarin aiki don a fito da sahihiyar gaskiya na yadda aka kashe kuxin al’umma a gwamnatin da ta gabata.
“Wannan rahoton da aka bayar ina da tabbacin yayi daidai da ra’ayin al’ummar Sakkwato, bayan mun karvi wannan rahoton za mu kafa kwamitin amintattu don aiwar da shi bisa qa’ida.
“Ina son na sanar da al’ummar Sakkwato alqawalin da muka xauka tsakaninmu na yin gwargwadon abin da muke iyawa na riqe amanar dukiya yana nan bai canja ba, kuma wannan gwamnatin ba za ta amince don wadda ta gabata ta yi rashin gaskiya ba, kuma ita ma ta yi hakan ba, duk wanda ya yi rashin gaskiya ko a tare da mu yake zai haxu da fushin hukuma.
“Dogon lokacin da kwamitin ya xauka yana aikin ya faru ne don mu tabbatar ya baiwa kowa damar da tsarin mulki ya ba shi,”kalaman gwamnan Sakkwato.
Da farko Alqali Pindiga ya bayyana cewa sun karvi takardun qorafi 31 a tsakanin hukumomin gwamnati da qungiyoyi da xaixaikun mutane a lokacin aikin, sannan sun kira shaidannu 246.
“Kwamitin ya yi aikinsa da adalci da kiyayewa da kaffa-kaffa kan nauyi da aka xaura mana, rahoton mun kasa shi gida biyar don tabbatar da daidaito da ba da haqqi,” a cewarsa.
Ya ce “kowane vangare muka xauko sai mun yi masa qwaqwaf cikin tattaunawa har a yi matsaya kan abin da muka gano ga shedu.”
Ya bayyana kwamitin ya gano akwai zargin almundahana ta kuxi sama da biliyan 117 a shekara takwas na mulkin tsohuhuwar gwamnati, sun gano savawa qa’ida a wurin mu’amala da kuxi da bayar da kwangila ba tare da bin doka ba, yin gwanjo da sayar da kadarorin gwamnati da wasu harkokin kuxi ba tare da bin doka ba, duk waxannan sai da suka qididdige kuma suka bincika tare da tabbatar da sabawa dokar da gwamnatin Tambuwal ta yi.
Umar Abdullahi ya nuna kwamitin zai qarfafa riqon amana da samar da tsarin gaskiya.
“A halin gaskiya ina fatan rahoton zai bayar da gudunmuwa ga cigaban jihar Sakkwato zai kuma kawo mata mutunci a tsakanin hukumomi,” ya ce.
Kabiru Muhammad na kallon wannan lamari ne kawai na siyasa “siyasa ce gwamnatin Sakkwato ke yi da wannan lamari kuma ba za su yi nasara ba domin suma ba kan gaskiya suke ba, yakama mu wuce haka gwamnati ta riqa kallon cigaban jama’a ba cin zarafin ‘yan adawa ba.”
Muhammad Sani a yanda yake kallon lamarin ana yi ne don biyar buqatar kai ba don jiha da al’ummarta ba.
“Wane irin bincike ne da ba a kammala ba tun farkon kwana 100 na farkon mulki sai yanzu da siyasar 2027 ta kunno kai, ana yi ne don a baiwa ‘yan adawa tsoro a kuma yi masu tabon da zai sa talakawa su guje su, don kar su yi tasiri.
“Ya rage ga talakawan Sakkwato su yi wa kan su matsaya kan gwamnati da gabata da mai ci a yanzu.”
Kwamishinan Muhalli a lokacin Gwamnatin Tambuwal Honarabul Abdullahi Hassan ya ce ana shi sani kwamitin ya qi ba da damar kare kai daga wurin Sanata Tambuwal
“Shari’a za’a yi ma, doka ta ba da dama a saurare ka, kuma ba a saurare ka ba, tau wace shari’a za a yi maka.
“Kamata ya yi a bari ya zo ya zauna ya yi bayani, tun da an aika masa goron gayyata, tun da in ba da shi ba ai ba za a aika masa ba, tun da an gayyace shi, sai a jira a ji daga gare shi, ko zai yiwu a yi wa na qasa da shi hukunci a qyale shi, abin da kowa ya yi sai da umarninsa.”
“Ni nasan an gayyace shi amma bansan an saurare shi ba, ya zo suka gaya masa ba su shirya ba za su qara gayyatarsa, ban san lokacin da ya koma ba.”
Abdullaahi Yusuf Hausawa tsohon kwamishinan cikin gida a lokacin mulkin Tambuwal ya ce “yana da kyau a yi bincike ba mu ce kar a yi ba,amma duk wanda za a yi tau a yi bisa ga amana da gaskiya domin shugabanci amana ce kuma kowa na fatar ya tsare al’umma da amana wanda bai tsare ba ana fatan a bincike shi sai a hukunta shi amma kar a sanya cuta da yin bita da qulli,
“Maigidanmu(Tambuwal) yana goyon bayan bincike, gwamnatin da muka jagoranta an kamanta gaskiya ga dukiyar al’umma an yi abin da ya dace wurin kashe dukiyar jama’a, an bi doka da oda, baya aminta a yi ba daidai ko qin bin qa’ida ban zaton akwai wani abu na rshin gaskiya don haka ba mu da haufi a binken da aka yi da ikon Allah.”
Kan jan qafar kwamitin ya yi, ya ce “wannan gwamnati(APC) daga sama har qasa ta nuna tana biye da qafafun ‘yan adawa don haka duk abin da ya zo ga ‘ya adawa ba zai ba mu mamaki ba, abu ne da muka san za mu samu irin wannan bita da qullin na siyasa in ka lura an kafa kwamiti an shekara biyu zuwa uku ba a bayar da rahoto ba sai a wannan lokaci hakan ya savawa hankali da duk wani kwamiti da ake kafawa irin wannan domin kowane kwamiti yana da lokacin da aka qayyade masa don ba da rahoto.
“In ka lura ai bai kamata EFCC ta gayyaci Tambuwal ba sai wannan kwamiti ya ba da rahotonsa ga gwamna amma gwamnati ta yi daban sun yi daban muna da irin wannan tunani shi yassa bai zo mana da mamaki ba.”
Malami Ahmad Basakkwace tsohon jagoran masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Sakkwato a zamanin mulkin Tambuwal kuma yanzu shugaban jam’iyyar PDP a qaramar hukumar Sakkwato ta Kudu ya ce lamarin da gwamnatin Sakkwato take ciki nada matuqar tayar da hankali kan haka take son voye kasawarta, “a gaskiya yanayin da muka samu kanmu a Sakkwato akwai ban tausayi don in da ana kuka rashin kuxi ba a yi wani abu ba za mu yarda, amma tun sanda aka qirqiro Nijeriya jihohi ba su tava samun kuxi kamar yanzu ba ka ga jiha ta karvi kuxi sama da kashi 70 na kasafinta, kamar jihar Sakkwato in da na sani ya yi kasafin kuxin na shekarar 2025 sama da biliyan 500 amma ko da aka kai watan shida ya karvi kuxi sama da biliyan 250, daidai da kashi 47 na kasafin kuxin 2025 a rabin shekara, ba kamar yadda muka yi ba sai mun yi aro a banki ko mu jira kuxin shiga na jiha, amma abin tausayi da tsoro babu wani aiki babba dake da tasiri ga rayuwar talaka jiha.
“A yau Sakkwato ba ta da cikakkiyar asibiti dake da komai na aiki wadda Gwamna ko Kwamishina da masu kuxi a jiha in rashin lafiya ta kama su ba wata fargaba a tafi da su can, babu guda ta gwamnati anan, da waxannan kuxi da muka samu babu ta a birni balle a yi maganar qauyukka, aikin gwamnati ne ta kare lafiya da dukiyoyin al’umma, ga kuxi an samu amma gwamnati ba ta yi ba don rashin iya jagoranci babu tausaya wa ga mutanen Sakkwato.
“Babban abin da ke damunmu a Sakkwato shi ne abin da jama’a ke buqata a yi masu ba shi ne gwamnati ke mayar da hankali kansa ba, yau da talaka ya samu ruwan sha da ingantattun wurin kiyon lafiya, qaramar asibiti matakin farko a yanzu ko wanki qurji ba ka aminta a yi maka wurin yanda abubuwa suka lalace.
“Sakkwato da muke mafi talauci a Nijeriya dake kashi 92 a qididdigar talauci amma gwamna ya ware biliyan 13 domin ya saye jirgin sama mi za mu yi da shi, a baya ya ware biliyan 30 akan wayoyin qawata gari,duk wani abu da ke bunqasa tattalin arzikin Sakkwato yana qasa.
“Waton wannan gwamnati ba su san qa’idar kasafi ba, doka ta hana sauya kuxi daga wani wuri zuwa wani amma tun sanda aka rantsar da gwamnatin nan sau xaya ne ta nemi majalisar dokokin jiha kan lamarin wanda ya sava doka , abubuwa ne ake yi ido rufe, ba su bin qa’ida a wurin kashe kuxi wannan abin juyayi ne ga mutanen Sakkwato,” kalaman Malami Basakkwace.
Magoya bayan Sanata Tambuwal suna kallon gwamnatin Ahmed Aliyu ita ce ta yi laifin da take zargin su da aiwatarwa su ne ke sava doka a wurin mu’amala a da dukiyar al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here