Fusatattun matasa sun yiwa gangamin yakin neman zaɓen APC a-ture a Yobe 

Fusatattun matasa sun yiwa gangamin yakin neman zaɓen APC a-ture a Yobe 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Daruruwan yan dabar siyasa sun kawo cikas a yakin neman zaben jam'iyyar APC na shiyya ta uku (Zome C), da yammacin ranar Asabar, a garin Gashuwa, shalkwatar karamar hukumar Bade dake jihar Yobe- mahaifar shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya. 

An tsara aiwatar da taron gangamin yakin neman zaben ne bayan bude sabuwar kasuwar zamani wadda Gwamnan jihar, Hon. Mai Mala Buni ya gina a garin Nguru, inda daga bisani aka hallara a Filin Agric dake unguwar Katuzu a Gashuwa. 

Bugu da kari kuma, tun a garin Nguru aka fara ganin alamun yiwa tawagar yan siyasar a-ture, kana kuma kafin shiga garin, da zuwa inda aka shirya gudanar da taron, wasu gungun fusatattun matasa ne suka tsaya kan hanya suna yiwa tawagar yan siyasar a-ture da ihu tun a kan hanya. 

Abin ya kara kamari ne a lokacin da shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan yake kokarin mika abin magana ga Gwamna Mai Mala Buni, wanda yake tare da Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, inda kan ka ce kwabo, fusatattun matasan suka rinka shewa da ihun: ‘ba ma yi, ba ma yi, ba ma so’ tare da jifar kan mai uwa da wabi kan dandamalin da manyan baki suke tsaye a kai.

Haka zalika, an sha dage ranar da za a gudanar wannan yakin zaben a jihar, sakamakon rashin tabbas da rudanin da APC ta shiga a jihar. Al'amarin da ya samo asali daga rikita-rikitar da ta dabaibaye zaben fidda-gwanin da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar, kana da hukuncin da kotun koli ta yanke kan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa; duk suna daga cikin abubuwan da suka tunzura wasu matasa. 

Har wala yau, wannan gangamin taron yakin neman zaben ya samu halartar dubun-dubatar magoya bayan jam'iyyar APC a fadin jihar, wanda ya kunshi jiga-jigan mutane, wadanda suka hada da shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, Gwamna Mai Mala Buni tare da Mataimakin sa, Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya da shugabanin jam'iyyar APC a jihar Yobe hadi da kwamitin yakin neman zaben 2023 da makamantan su. 

Ganin irin yadda filin ya yamutse da ihun a-ture ya tilasta wa jami'an tsaro dole suka gaggauta arcewa da Gwamna, aka fita dashi daga wajen taron, al'amarin da ya jawo dole aka hakura da ci gaba da taron, kowa ya kama gabansa.