Home finannai Fitacciyar mawakiyar addinin Musulunci, Ruqayya Gawat ta rasu

Fitacciyar mawakiyar addinin Musulunci, Ruqayya Gawat ta rasu

1
0

Fitacciyar mawakiyar nan ta addinin Musulunci, Rukayat Gawat Oyefeso ta rasu.

Mawakiyar ta yi shura da wakokin ta a cikin al’ummar Musulmai a kudancin Nijeriya.

Jaridar PUNCH ta rawaito cewa fitaccen Malamin nan na Ilori Alfa Aribidesi At-Tawdeeh ne ya bayyana rasuwar ta a shafin sa na Facebook a safiyar yau Talata.

Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan rasuwar ta ba.

Rasuwar mawakiyar ta haifar da jimami ga masoyan ta inda ake ta yada labarin rasuwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here