Home Labarai FBI Ta Gargadi Kotun Amurka kan Bayyana Sirrin Tinubu kan Miyagun ƙwayoyi

FBI Ta Gargadi Kotun Amurka kan Bayyana Sirrin Tinubu kan Miyagun ƙwayoyi

31
0

FBI Ta Gargadi Kotun Amurka kan Bayyana Sirrin Tinubu kan Miyagun ƙwayoyi sunce yin hakan Na Iya Jefa Rayukan Wasu iyalai Cikin Haɗari.

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta gargadi wata kotun tarayya a Amurka cewa, bayyana wasu daga cikin takardun da suka shafi Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, na iya jefa rayuwar wasu mutane ko lafiyarsu cikin haɗari.

FBI ta bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ta gabatar wa Kotun Gundumar Amurka ta District of Columbia a ranar 20 ga Agusta, 2026, inda ta nemi izinin kotun domin gabatar da bayanan da za ta bayyana dalilin da ya sa ta ke riƙe da wasu daga cikin bayanan.

Hukumar ta ce ba za ta iya bayyana cikakken dalilin riƙe wasu takardun a fili ba, saboda hakan na iya tona asirin wasu dabaru da hanyoyin binciken jami’an tsaro.

Saboda haka, FBI na neman kotun ta amince mata ta gabatar da bayanan a ɓoye kuma ƙarƙashin hatimin kotu, domin alkalin kotun kaɗai ya duba su.

Bayanan da ake magana a kansu na cikin takardun da wani ɗan Amurka mai rajin neman gaskiya, Aaron Greenspan, wanda ya kafa PlainSite, ya nema ta hanyar dokar Freedom of Information Act (FOIA).

Daga cikin abubuwan da Greenspan ya nema akwai cikakken fayil ɗin FBI da ya shafi Tinubu, da kuma wasu bayanan tambayoyin da aka yi da shi dangane da wani binciken FBI.

FBI ta ce ta yi amfani da wasu tanade-tanaden dokar FOIA wajen hana fitar da wasu bayanai, ciki har da waɗanda suka shafi kare sirrin mutane, majiyoyin bayanan sirri, dabarun binciken jami’an tsaro da kuma bayanan da bayyana su ka iya jefa rayuwar mutum cikin haɗari.

Hukumar ta kuma ce idan kotu ta amince da buƙatarta, za ta gabatar da wannan bayanin na sirri kafin ranar 28 ga Agusta, 2026.

Wannan sabon matakin na cikin doguwar shari’ar da Aaron Greenspan ya shigar, wadda ta shafi neman wasu bayanan gwamnatin Amurka dangane da binciken da aka gudanar a shekarun 1990, ciki har da wani bincike da ya shafi Chicago.

A watan Afrilun 2025, Alƙaliya Beryl Howell ta umarci FBI da DEA da su ƙara bayyana dalilansu kan ƙin tabbatarwa ko musanta kasancewar wasu takardu da Greenspan ya nema, bayan ta ce hukumomin ba su gamsar da kotu da dalilan da suka bayar ba.

A halin yanzu, batun na ci gaba da kasancewa a gaban kotun Amurka, yayin da ake ci gaba da samun sabbin matakai kan ko wane ɓangare na takardun za a iya bayyana wa jama’a.

Rahotanni sun nuna cewa Tinubu ya musanta aikata laifin da ake danganta shi da binciken na shekarun 1990, kuma batun da ake shari’a a kai ya shafi bayanan tarihi da aka nema ta hanyar FOIA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here