Fashewar bama-bamai ta kashe mutum ɗaya da raunata wasu su huɗu a Jihar Neja

Fashewar bama-bamai ta kashe mutum ɗaya da raunata wasu su huɗu a Jihar Neja

Wani manomi, Dauda Haruna, ya rasa ransa yayin da wasu mutane hudu, ciki har da ‘yan uwa uku, suka samu munanan raunuka a wani fashewar bama-bamai da ake zargin sun faru a al’ummar Bassa da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

Daily Trust ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne tsakanin al’ummomin Bassa da Gwadara a safiyar ranar Alhamis yayin da wadanda abin ya shafa ke kan hanyarsu ta zuwa gona don girbe amfanin gona.

Wasu mazauna yankin sun shaida wa Daily Trust cewa fashewar farko ta faru ne lokacin da ‘yan uwan guda uku, Mali (mai shekara 20), Nehemiah (mai shekara 14), da Jona (mai shekara 15), ke kan babur. Fashewar ta biyu kuma ta faru ne lokacin da babur din wadanda suka je ceto ya taka bam din, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin masu ceton, Dauda Haruna.

Mahaifin yaran guda uku, Mista Enoch, ya ba da labarin abin da ya faru ga wakilin majiyar mu a Asibitin Kwararru na IBB da ke Minna, inda ake jinyar wadanda suka ji rauni.

Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da bam ya fashe a wannan wata a Bassa.

Enoch ya ce yaran suna gaba a kan babur yayin da shi kuma ke tafiya a kasa tare da matarsa, sai suka ji wata fashewa mai karfi.

DAILY TRUST ta ce da ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin samo bayanai sannan ya bada bayani.