Fargaba ta mamaye jam'iyar PDP a tsakanin mambobin jam'iya kan maganar karba-karba a shekarar 2023 yankin da shugaban kasa zai fito shi ne ake ta yin turka-turka kansa.
Jagororin jam'iyar sun yi taro a tattaunawa in da za a cigaba da zama domin samar da bakin zaren lamarin ba tare da hatsaniya ba.
Fargabar ta karu ne a lokacin da ake ta ganin masu ruwa da tsaki a PDP suna dira Abuja domin sanin halin da ake ciki a maganar karba-karbar.
Tambayoyin da ake ta yi kan karba-karbar shin wane yanki ne zai samu nasarar yi wa jam'iyar PDP takara, Arewa ko Kudu ba a san wanda zai yi nasara samun tikitin jam'iyya ba.
Tattaunawar ta soma a tsakanin shugabanni da jagorori da shugabanni tun a jiya(Litinin) kan cimma matsaya guda kafin taron majalisar zartrwar jam'iya don a zaman ne za a kai karshe in da shugaban kasa zai fito.