A karo na Tara, Farfesa musa Garba maitafsir, ya sake bada Tallafin Gurabun karatu ga matasan jihar Sokoto,Kebbi,Zamfara dss. masu son suyi karatun N.C.E kuma ba su da Zarafi.
Daga Mukhtar Haliru Tambuwal Sokoto
Farfesa Musa Garba mai tafsir, kuma Shugaban Hukumar malanta ta kasa, a kokarin bada tashi gudun mawar tallafawa yunkurin habaka ilimi, wannan ne karo na tara tun daga shekarar 2014 yana bada irin wannan gurabun ga yan Asalin Jihohin Sokoto, Kebbi ,Zamfara da sauran su.
Farfesa, Wanda a yanzu shine Shugaban Maaikatar Malamta ta kasa (National Teachers Institute) da ke a kaduna, kuma Tsohon Kwamishinan lamurran Addini na jihar Sokoto,kana Wanda ya rike Hukumar Bada Ilimi na Bai daya ta jihar sokoto (U.B.E) A duk shekara ya na bada wadannan gurabun dan zakulo wadanda suka cincinta dan su amfana, kamar kowace shekara, a bana ma insha Allahu Daukacin kungiyoyin Addinin musulunci da ke fadin jihar Sokoto,kebbi da zamfara za su amfana, da kuma Wasu Masallatayyen jimua da cibiyoyi da zaurukkan Daukar karatu na sanannin malamman addini musulunci da ke anan sokoto.
Tuni aka soma baiwa shugabannin kungiyoyin wadannan takardun cikawar, dan haka ga duk wanda ke da bukata zai iya tuntubar kungiyar Addinin musulunci mafi kusa da shi.
Tun daga na Majalisar sufayen Dariku, majalisar Izala,Dalibbai (MSSN) Mata (Fomwan,WID,MSO,AKH,I.ET,JNI,JTI,COUNCILOF ULAMA,NASFAT,ANSARUDDEEN) Kungiyoyin matasa irin NACOMYO, IPPS, ALYATEEM,) KUNGIYOYIN LIKITOCI MUSULMI (IMAN) Da sauran su.
A bana akwai tsarin biyan kudin Jamb, Wanda sai da su ne zaayi jarabawar baya ga kudin jarabawa da ake biya. Zaa biya #16,000 na Shekarar farko (N.C.E 1 )da suka hada da kudin jarabawa,Rijista,da Jamb, sai shekara ta biyu (.C.E 11 ) da ta ukku ( N.C.E 111 ) zaa biya Naira Dubu goma #10,000 kowanen su.
Kuma duk wadan da suka cika su kai ga makarantar ,zaayi Jarabawar tantancewa farkon wata mai kamawa,insha Allahu, Dan neman karin bayani
Zaaiyan kiran Mukhtar A Haliru Tambuwal 07087770003, Murtala St 08033998533,Abubakar Gagi 07036259526 Muntaka Bello 09039567221 ko Husaini A Ahmad da Nura imam, dan karbar na wadan da aka lissafa a sama ga wadan da ba su amshi na su ba.
Dan neman karin bayanin akan makarantar da tsarin zaa iya kiran Registrar a lambar 08061636630. Kuma wadan da ba su iya amsa ga kungiyoyin za su iya zuwa makarantar su karba,
Muna fatar Sauran Yan kasuwa,Yan siyasa,maaikatan Gwamnati da su yi koyi da wannan talikin Tilo da ya dage da wannan aikin jinkai.
Farfesa muna fatar Allah ya biya ka da Alkhairi da duk mai hannu a cikin wannan Aikin. Amin.