Farashin Siminti da kayan gini sun yi tashi Gwauron Zabo
Kayan gini ya yi tashin gwauron zabo a Nijeriya abin da zai shafi gine-gine wannan kalubale ne ga gwamnati kan samar da gidaje masu saukin kudi.
Wannan lamarin zai shafi masu gina gidaje na kasuwanci in da kamfuna da daidaikun jama'a ke ta yin mita kan tsadar.
Masu kawo kayan gini sun ce yanayin kasuwa na rashin tabbas ya kara jefa jama'a cikin halin tsada.
Farashin siminta ya tashi daga 4000 zuwa 8,800 ga kowane jikar siminti, karin kenan kashi 100 ne.
Bulo da ake sayarwa 250 a shekarar data gabata yanzu ya koma 600 ya danganta da girmansa.
managarciya