Falana ya caccaki alkalan tirabunal da suka yanke zaɓen gwamnan Kano

Falana ya caccaki alkalan tirabunal da suka yanke zaɓen gwamnan Kano

Lauyan kare hakkin dan Adam, Femi Falana, SAN, ya caccaki hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke na soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Da yake magana a shirin Channels TV na Sunrise a yau Juma’a, Falana ya ce soke kuri’u dubu 165,000 saboda basa ɗauke da tambari bai dace ba.

A cewarsa, bai kamata alkalan su hukunta masu kada kuri’a ba akan kura-kuran da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi.

Falana ya ce: “Ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba. Abin da ya faru kwanan nan kenan a Kano, inda aka ce kuri’u dubu 165,000 ba da dauke da sa hannun da jami’an INEC.

“Muna rokon alkalan mu da su rungumi adalci da gaskiya, ta yadda ba za ku iya hukunta masu kada kuri’a kan kura-kuran da INEC ta yi ba.

“Ba za ku iya kalubalantar ingancin katunan zabe ba.

“Don haka, ina ganin wadannan su ne wuraren da alkalan mu za su koma kan tebur su yi nazari,” Mista Falana ya jaddada.