El-Rufa'i ya bada hutun kwana uku  domin yin katin zaɓe

El-Rufa'i ya bada hutun kwana uku  domin yin katin zaɓe

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu domin samun damar kammala rajistar masu zabe.

Gwamnatin jihar ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su yi rajista kafin ranar Lahadi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa ya fitar a yau Talata a Kaduna.

Gwamnatin ta kuma bukaci dukkan mazauna garin da su yi amfani da wannan dama su yi rijista domin su samu damar nuna ƴancinsu na kada kuri’a a zaɓe.

 Adekeye ya ce gwamnati ta bukaci daukacin ma’aikatan jihar da su rika tallafa wa ma’aikatansu don yin rajista kafin INEC ta rufe rajistar masu zabe a  ranar Lahadi.