Home Rahoto EFCC ta kama wata ƴar Tiktok a Borno kan zargin wulakanta Naira

EFCC ta kama wata ƴar Tiktok a Borno kan zargin wulakanta Naira

7
0

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed a Maiduguri, jihar Borno, bisa zargin wulakanta kudin Najeriya.

A cewar hukumar, an kama matar ne bayan wani bidiyo da ya yadu a TikTok inda aka gan ta na goge majina da takardar kudi N500. Jami’an EFCC sun ce sun gano ta tare da cafke ta a cikin garin Maiduguri.

Yanzu haka ana tsare da ita yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a kotu bayan kammala binciken.

Hukumar ta ce laifin ya sabawa dokar Babban Bankin Najeriya (CBN), wadda ta haramta lalata ko amfani da kudin kasa ta hanyoyin da ba su dace ba, tare da tanadin hukuncin tara ko dauri.

Lamarin ya biyo bayan irin wannan hukunci da aka yanke wa wata jarumar Kannywood kwanan nan kan makamancin laifi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here