EFCC Ta Gano Miliyan $72.8 Da Ke Da Alaƙa Da Tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani
EFCC Ta Gano Miliyan $72.8 Da Ke Da Alaƙa Da Tsohuwar Ministar Man Fetur Diezani
Daga: Salisu Idris Waziri
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta sake gano dala miliyan 72.8 da ke da alaƙa da tsohuwar ministar mai ta ƙasar Diezani Alison-Madueke.
Gidan talabijin na Channels a ƙasar ya ruwaito cewa an gano kuɗaɗen ne a wani asusu na bankin Fidelity da ke ƙasar.
Bayan haka kuma an kama tsohon daraktan bankin Nnamdi Okonkwo wanda a yanzu yana ɗaya daga shugabannin First Bank wanda a baya ya sha tambayoyi kan dala miliyan 153 da kuma dala miliyan 115.
Duk da cewa EFCC ta karɓi dala miliyan 153, har yanzu batun dala miliyan 115 da ke da alaƙa da zargin ba hukumar zaɓe cin hanci na wasu kotunn ƙasar ana ta shari'a.
A yanzu dai Mista Okonkwo da Charles Onyedibe na hannun EFCC inda suke shan tambayoyi kan batun miliyan $72.8.
managarciya