EFCC Na Binciken Gwamnan Zamfara Kan Amfani Da Kuɗin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja

EFCC Na Binciken Gwamnan Zamfara Kan Amfani Da Kuɗin Al'umma Wajen Siyan Gidaje a Abuja

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tace tana binciken gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle bisa zargin almundahana. 
EFCC tace ta fara binciken gwamnan ne sakamakon bayanan da ta samu na cewa yana amfani da dukiyar al'ummar jiharsa wajen mallakan kadarorin biliyoyi a Abuja. 
 
Hukumar tace binciken da ta fara gudanarwa ya nuna cewa gwamnan ya sayi gida mai lamba 729, Cadastral Zone C16, Idu Industrial Estate, Abuja. 
EFCC ta bayyana hakan a karar da kamfanin Fezel Nigeria Limited ya shigar da ita kotu kan kwace ofishinta karfi da yaji, rahoton TheNation. 
Kamfanin Fezel yace ginin da ake zargin gwamnan da mallaka na sa ne kuma ya sayarwa kamfanin Beisha Printing Press Limited. Amma EFCC tace karya kamfanin Fezel keyi, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ne ya sayi dukiyar ta kamfanin Beisha Printing Press Limited. 
"Daya daga cikin dukiyoyin da infoma ya sanar da mu shine Plot 729, Cadastral Zone C16, Idu Industrial Estate, Abuja, da aka saya N1,200,000,000.00, wanda Dr. Bello Matawalle ya biya kudi a hannu da sunan kamfaninsa (Beisha Printing Press Limited),” 
EFCC ta kara da cewa ta samu labarin an fara kokarin kwashe manyan na'urorin biliyoyi daga gidan bayan gayyatar kamfanin da tayi. 
"Yayinda muka samu labari, muka gaggauta damke masu kokarin kwashe kayayyaki daga gidan." 
"Mun musu tambayoyi kuma muka basu beli, kuma daya daga cikinsu. Evelyn Odagundoye, da farko ta karyata yiwa Dr Bello Matawalle aiki amma daga baya da aka gudanar da bincike kan wayarta sai aka tabbatar Dr Bello Matawalle take yiwa aiki."