DUHU DA HASKE: Fita Ta Tara
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 9*
~Kullum tare suke fita aiki saiya ajeta kafin yake tafiya aiki, komai yana tafiya daidai, shine yake fitar da sabbin style's a kullum yana basu, zuwa yanzu ya saba da kowa na wajen banda manal wacce take aika mishi harara a duk lokacin da suka haɗa ido, kamar kullum yauma shida Ameesha da Imran da kuma fahad ne a cikin motar, tayi kyau sosai cikin black dress dogon riga tasa hula sannan tayi rolling siririn mayafi akai, tayi kyau sosai kamar sarauniyar kyau, fatar ta duk da bata cikin wani daɗi amma yana glowing sosai, tace "Imran kasan me?"
girgiza kai yayi fuskanshi ba walwala da alama yana cikin fushi dan tunda suka fara tafiya baiyi magana ba, a hankali ta juyo tana kallonshi, murmushi tayi tasa hanu ta shafa gefen fuskanshi sannan tace "Imran a koda yaushe idan na ganku cikin fushi baku san yadda nake ji bane a zuciyata, ko kaɗan banason ganinku kuna fushi, dan Allah kayi murmushi kaji?"
a hankali yace "ni ki kyaleni"
cikin son neman tsokananshi tace "to shikenan na barka amma ka tuna wancan beb ɗin?"
alama ya fara mata tayi shiru yana nuna mata man, dariya ta fara tana cewa "a,a barni na faɗa wancan kyakkyawar beb ɗin da tace tana san...."
da sauri ya rufe mata baki, shiru tayi yana sakinta yayi murmushi yace "gashi nayi"
man yana jinsu baice komai ba har ya ajesu a school, jakan fahad ta bashi tace "kaga an canja maka school ka dawo school ɗinsu Imran yanzu ba kai kaɗai bane kaida yayanka ne duk abinda kayi na rashin ji Imran zai faɗa mana"
kanshi ya sunkuyar yace "to"
karɓan jakanshi yayi tana ɗaga musu hanu har suka shiga ciki, juyowa tayi daga ɗaga musu hannun da murmushi akan fuskanta kamar kullum haɗa ido sukayi da man ya ɗaga mata gira, taɓe baki tayi tareda yin alaman "what?"
girgiza kai kawai yayi yaja motan suka tafi, driving yake ita kuma ta zuba mishi ido, juyowa yayi yaga ta ɗauke kai, baiyi magana ba, lips nashi na kasa a bakinshi yana tsotsa a hankali yake kallon titin, kara juyowa yayi suka haɗa ido da sauri ta ɗauke kai, murmushi yayi yaci gaba da driving, saida suka isa wajen aikinta ya juyo zasuyi sallama yaga ta zuba mishi ido da sauri ta ɗauke kai, zata fita taji ya rike hanunta, shiru tayi batayi magana ba, yace "meesha meyasa kike satan kallona?"
ji tayi gabanta ya faɗi, murza yatsunta yake a hankali cikin nata yace "kalleni"
kin kallonshi tayi
yace "kalleni mana meesha"
da sauri ta juyo ta maida fuskanta kamar na yara tace "gashi na juyo na kalleka me aciki? ban isa na kalleka bane? ko so kake na daina kallonka? gani kake kamar kana da kyau ko?"
murmushi kawai yayi ganin ta maidashi yaro, sakin hanunta yayi yace "kiyi aiki lafiya"
tace "bye"
hanu take ɗaga mishi har ya tafi bata daina ɗaga mishi hanu ba, juyowa tayi zata shiga ciki da sauri tayi baya tana waro ido ganin wannan katon yana kallonta yana huci, hannaye ta haɗa alaman roko tace "please please please"
cikin shaƙaƙƙen muryanshi yace "kullum sai kinzo late sai shegen bada hakuri da wannan karamin bakin naki kamar na kifi"
tace "dan Allah"
yace "yimin shiru kina wani kallona da wannan idanun naki kina ganin zaki iya tsoratani ne dasu?"
kanta ta sunkuyar kasa yace "wuce"
da sauri harda ɗan gudu ta wuce tana cewa "wayyo Allah wannan ƙaton ya samin ido da murya kamar an shaƙe mage"
zama tayi akan kujeranta ta fara rubuce rubucen duk abinda ya faru kafin tazo da wanda yake faruwa yanzu, satan kallonshi tayi taga yana kallon wayarshi, ciro wayarta tayi ta kira numbern man, yana ɗauka tayi kasa da murya tace "ka isa?"
yace "yes princess"
hamma yayi tace "yunwa kake ji?"
gyaɗa kai yayi tareda shagwaɓe fuska yace "yunwa meesha banci komai ba"
da sauri tace "sorry"
kashe wayan tayi ta ɓoye a aljihu, a hankali ta tashi taje wajen mutumin, kanta a kasa tace "sir inaso naje gida na ɗau wayata sabida na manta kuma rubutun jiya duk na tura a wayan"
cikin masifa yace "ban taɓa ɗaukan unserious yarinya kamar ke ba, bakida kokari shashasha jeki ɗauko ki dawo da wuri"
cikin sauri ta fita tana rufe ido kamar yara irin basu son a gansu ɗinnan, cikin kasa da murya tace "niba shashasha ba, nama fika wayo"
napep ta shiga zuwa gida da gudu ta fita a napep ɗin ta shige gida, Anty ta dafa kirji tace "Ameesha lafiya? ba dai wani laifin kikayi aka koreki ba?"
tana tafiya da saurinta kamar kullum tace "ba laifin da nayi na dawo na dafawa man abinci ashe da yunwa ya tafi kuma nasan wannan muguwar boss ɗinshi ba zata barshi yaje ya siya abinci yaci ba"
kayanta ta cire tasa riga da wando, wandon kamar three quarter a buɗe sosai pink, man ne ya siya mata da riga baƙi me faɗi, ta shiga kitchen ta fara dafa mishi shinkafa, cikin sauri take yi bata bari ruwa ya tafasa ba ta zuba kawai ta zuba gishiri me yawa da magi, ɗanawa tayi tace "gishiri ya ɗan wuce kaɗan"
da haka ta gama girkin, karamin mayafi tasa a kanta sannan tasa takalmi canvas wanda sukayi anko da fahad fita tayi daga gidan tana cewa "Anty na tafi"
napep ta shiga zuwa m.u.m"
Manal zaune take a office nata cikin riga da wando na suit fari, tayi parking gashinta da farin ribbon tasa hulan net ganin a mota take zuwa yasa bata damuwa da mayafi, takalmi me tsini ne a kafanta ta ɗaura glass nata baki a saman hulan, kafa ɗaya kan ɗaya ta ɗaura tana kallon laptop na gabanta duk abinda yake faruwa a cikin company tana gani, ido ta zuba mishi lokacin da taga yana knocking, a takaice tace "come in"
shigowa yayi, kamar kullum ya zauna kafin tace ya zauna, ɗago kai tayi daga kallon laptop ɗin yayi mata murmushi tareda cewa "gani"
tace "tashi"
tashi yayi ta ɗau takadda plain ta mika mishi tace "yanzu aka kirani anason zanen sabon motan da zasu fitar dashi a wannan shekaran sunce nan da minti goma suke bukata domin jirgi zai tashi nan da minti goma kuma kasan idan muka rasa wannan opportunity mun rasa babban aiki, samun wannan aikin zaifi mana duk aikin da mukayi a baya, na zana ɗaya tun jiya sai yau na gama, bansan biyu suke so ba sai yanzu suke faɗamin, nasan kai kaɗai ne zaka iya a cikin minti goma, daga yanzu na fara irga lokacinka, ɗauka yayi yace "an gama"
fita yayi da sauri ya zauna akan kujeranshi ya ɗau kaloli ya fara zane, tana zaune akan kujeran tana kallonshi yadda yake aiki da kwarewa, murmushi tayi ta gyara zama daga kan kujeran, wayar office aka kira ta ɗauka tasa a kunne tayi shiru, saida akayi magana kafin cikin muryanta me sanyin gaske tace "hello aiki zai kare nan da minti goma driver ɗinku ya tsaya a bakin kofan"
shiru tayi sai kuma tace "kun san bana karya alkawari"
katse wayan tayi tana kallonshi tana irga lokaci tasan zai gama a cikin minti goman, camera ta juya zuwa waje taga driver ɗinsu yana tsaye a bakin kofa, komar da camera ciki tayi idonta akan Abdul saura kaɗan ya gama, wayarshi ne yayi kara da sauri ya ciro daga aljihu ya amsa kiran ganin sunan da yayi saving da my meesha, sawa yayi a kunne yana cigaba da zanen yace "ya akayi?"
yace "Man fito waje ina jiranka yanzu a kofan company ɗinku*
da sauri yace "are you serious?"
tace "yes fito da wuri"
zaiyi magana ta katse, aje kalan yayi ya ture takaddan ya tashi da sauri ya fita, kallonshi take ta cikin computer ganin ya ture takaddan ya fita taji zuciyanta yana zafi, dunƙule hanu tayi ganin ya fita wajen wannan yarinyar da suke tafiya kullum tare, ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya, take idanunta suka sauya zuwa jajur, dunƙule hanu tayi ganin ameesha ta buɗe flaks na abincin ta ɗibo a spoon tasa mishi a baki, kallon agogo tayi taga saura minti huɗu, gani tayi ya rike hanun Ameesha sun samu wajen zama sun zauna tana bashi abincin a baki yana ci, da haka har minti goma ya cika, dunƙule hanu tayi ta buga jikin computer ta tashi a fusace zata fita, wani tunani tayi a hankali ta dawo ta zauna kan kujeran tana kallonsu, man yana jin gishiri har kwalwalwan kanshi amma yayi murmushi yace "my meesha abincin yayi daɗi naji daɗi sosai"
tace "amma gishiri ya ɗan wuce min ɗan kaɗan"
murmushi yayi yace "ba abinda ya wuce yayi daɗi"
tashi tayi tace "zan tafi"
kallon kayan jikinta yayi sannan yace "my meesha wannan wandon ai yayi guntu"
kallo tayi tace "guntu kuma? kaifa ka siyamin kuma kasan na saba"
cire rigan saman nashi yayi me ɗan tsayi yasa mata yace "ko kefa"
kuɗi ya ciro a aljihu ya bata yace "hau napep ki koma wajen aiki dan nasan karya kikayi"
tace "kamar ka sani nifa yunwa wannan lukutin ya dami rayuwata"
yace "karki damu zaki samu aiki anan very soon kinji?"
gyaɗa kai tayi, yayi mata kiss a gefen kumatu yace "bye?"
tafiya tayi yana kallonta har saida ta fita ya koma ciki, rufe ido manal tayi lokacin da taga yana mata kiss, gani tayi ya koma ya zauna yana aikinshi, kiran wayarta akayi, tana ɗauka sukace "mun fasa wannan aikin dake, yau kin karya alƙawari"
zatayi magana suka katse wayan, a fusace ta tashi zuwa waje, direct wajenshi taje tasa hanu duka biyu akan table na gabanshi ta zuba mishi manyan idanunta da suke cike da ɓacin rai, huci take tana kallonshi, da mamakinshi yake kallonta, ganin kallon yayi yace "me kuma nayi..."
cikin tsawa tace "rufemin baki"
shiru yayi, tace "meyasa baka gama zanen ba har saida sukace sun fasa? kasan wannan aikin shekara nawa nayi ina jiran samunshi?"
ganin baiyi magana ba tace "banza useless"
shima cikin ɓacin rai zaiyi magana ya tuna da maganan ameesha "koda me za'a maka ka danne zuciyarka ka dubi halin da muke ciki"
a hankali ya sunkuyar da kanshi, a fusace ta koma office nata tana bubbuga hanu kaɗan kaɗan akan table ɗin, koda aka tashi ameesha tana jiranshi a kofa kamar kullum, hanu ta ɗaga mishi yayi mata dariya kafin ya buɗe mata marfin motan tazo da sauri ta shiga, shima shiga yayi suka tafi.
washe gari sun aje fahad da Imran a school suna tafiya, ya kalleta yaga tayi shiru ba kamar kullum ba, baiyi magana ba har sukayi nisa batayi magana ba itama, a hankali yace "meesha me yake damunki?"
a hankali tace "dama dama akwai abinda nakeso na faɗa maka"
murmushi yayi yace "to meesha yaushe muka fara haka dake? inace kullum magana kawai muke kai tsaye bama ɓoyewa juna komai ki faɗamin menene?"
kanta kasa tana wasa da hanunta tace "dama...dama...dama....ni ina so...."
wayarshi aka kira yace "two minutes"
yana dubawa yaga sabon number ɗauka yayi yasa a kunne tareda cewa "salam"
muryan manal yaji cikin rashin son magana tace "yau bazanzo office da wuri ba, kafin nazo ka bawa kowa ya zana new dress guda biyar kai kuma guda goma sha biyar sauri ana buƙata da wuri"
kafin yayi magana ta katse wayan, bin wayan yayi da kallo ya maida muryanshi kamar nata yace "sauri dan ana buƙata da wuri, kamar wata uwata yadda take bani umarni"
ameesha a hankali tace "wacece?"
yace "boss ɗita ce"
gabanta taji ya faɗi tayi shiru shima bai kara ɗago maganan data fara ba harya ajeta a bakin kofan ta fita, gani tayi yaja motan da gudu ya bar wajen, yana zuwa ya sanar musu abinda zasuyi shima ya fara nashi.
manal ta fito daga ɗakinta sanye da rigan bacci tana mika, cikin takunta me cike da class ta isa kofan ɗakin ammi knocking tayi sannan ta tura ta shiga, ammi zaune akan gado tana kuka hankalinta ma baya nan tana kallon zoben dake sanye a ƙaramin yatsan ta, cikin kuka tace "ka tafi ka barni umar banajin daɗin wannan duniyan nafi son kana kusa dani"
harɗe hanu tayi a kirji ta jingina da jikin kofan tana kallonta, cikin kuka ta ɗago zata share hawaye ido huɗu sukayi da ita, da sauri ta share hawayen tace "ma..ma..manal yaushe kika shigo?"
murmushin gefen baki tayi mata kafin ta kame gashinta daya zubo ta fuska ta mayar bayanta hanunta ta zuba a cikin aljihun rigan baccin sannan ta karaso inda take, ɓoye hanun dake ɗauke da zoben ammi tayi, zama tayi a gefenta ta rungumeta tashi shiru kanta a kafaɗarta, a hankali ta ɗago ta kamo hanun dake ɗauke da zoben, cirewa ta fara ammi ta fara girgiza kai tana janyewa, saida ta cire zoben ta tashi ta fita, cikin gidan taje ta ɗauko wani katon dutse, ammi tana zaune taga ta shigo da dutsen, idanunta s waje take kallonta ganin ta nufota ta fara yin baya tana shigewa kan gadon sosai, murmushi manal tayi sannan ta aje zoben a kasa, dutsen ta ɗaga ta buga akan zoben saida ya tarwatse domin da karfi ta buga dutsen kuma manal tanada karfi sosai, ammi a tsorace take kallonta, ɗaukewa tayi ta fita dasu duka batayi magana ba, zubarwa tayi sannan ta koma ɗakinta, wanka tayi tazo ta shirya cikin dark green na shadda dogon riga anyi zubi da light green na zare, ba karamin kyau tayi ba bayan ta ɗaura ɗankwali ta rike siririn mayafi light green a hanunta, takalminta me tsayi da tsini sosai tasa baƙi sannan ta rike jaka baƙi, kamar kullum batayi kwalliya ba lipstick fari kawai ta shafa sannan ta fesa tsadadden turarenta ta rike makullin mota da kuma car key tana fito ta fara tafiya.
Ammi wayarta aka kira ta ɗauka tayi shiru, ji tayi ance "muna magana da matar marigayi Alhaji umar maidawa?"
tace "eh nice"
yace "idan ba damuwa mu jami'an ƴan sanda ne muna kofar gidanki zamu iya shigowa?"
da sauri tace "okay ku shigo"
tashi tayi tasa dogon riga na atamfa da mayafi babba ta fito jin anyi sallama a falon, hankalinta a ɗan tashe ta kallesu su uku babu uniform a jikinsu, ID card nasu suka nuna mata kafin ta nuna musu wajen zama tace "bismilla"
zama sukayi suka gaisa da ita kafin ɗaya daga cikinsu yace "sunana ispector faruk munzo ne domin neman wasu taimako a wajenki"
tace "to Allah yasa zan iya"
yace "zaki iya idan kinason mijinki kuma kinaso ki wankeshi daga kallon da mutane suke mishi bayan ya mutu"
tace "to ina jinku"
yace "bincike muke akan mutuwan mijinki shin zaki iya gaya mana ko sau nawa ya taɓa yamiki karya da har kikayi saurin yadda da abinda ya faru?"
buɗe baki tayi zatayi magana karan sautin takalmin manal suka ji, tafiya take tana hura fito tana juya makullin a ɗan yatsanta tun daga kan stair take kallonsu tana takowa a hankali tana cigaba da kallonsu, saida tazo last step tace "wani magana ake a gidannan babu manal aciki?"
ammi tace "yawwa manal idan kina kusa dani ina samun kwarin gwiwa kinga su police ne sunzo akan maganan mutuwan dadynki"
gabanta ne ya faɗi kirjinta ya fara duka da sauri da karfi, takowa tayi tana kallonsu tace "akan wani dalili?"
ɗaya daga cikinsu yace "hajiya kece mukeso mu yiwa tambaya ba ƴarshi ba"
ammi tace "ni banida amsan da zan iya baku akan umar banason ina tunashi zan iya kamuwa da cutan damuwa"
cikin tsawa yace "amsa zaki bamu dole"
manal dake tsaye ta kalleshi tace "dole?"
gyaɗa kai yayi, ya kalli ammi ya ɗaga murya kamar zai mareta yace "ki bamu amsa"
a firgice ammi ta kalli manal sannan jikinta ya fara rawa, cikin ɓacin rai manal ta isa inda yake ganin haka ya tashi shima yana kallonta, takalmin kafarta me tsini ta ɗaura akan kafarshi ta taka da karfi tana ciza leɓenta na kasa, kara yayi yana runtse ido, duk suka kalleta a tsorace, cikin idonshi take kallo, jini ne ya fara fita daga kafarshi yana ɓata tiles ɗin, ammi ta tashi da sauri tace "ma....."
hanu ta ɗaga mata alaman dakata, shiru tayi ta rufe baki da hanu tana kalonsu a mugun firgice, cikin kakkausan murya tace "wannan sabida tsawan daka yiwa Ammi na nayi maka, kafin nayi maka na shigowa gidanmu da tambaya akan mahaifina ina fatan zaku bar gidannan cikin ruwan sanyi"
ɗaya daga cikinsu yace "binciken mutuwan umar maidawa fa?"
tace "ba ita ya kamata ku bincika ba karuwar da suke tare ya kamata ku bincika domin ita batasan komai akai ba"
yace "to ai ta mutu"
tace "saiku bita idan kunason samun amsan"
kallon juna sukayi ta nuna musu kofa tace "get fu*king out"
duk suka fita da wuri, a hankali ta kalli ammi wacce tayi shiru tana hawaye, zuwa tayi ta riketa ta zaunar da ita akan sofa itama ta zauna tareda jawota jikinta, a hankali take shafa bayanta tace "kar kiyi kuka ina tare dake ammi"
jijjiga kai tayi, ta jima a wajen saida ammin tayi kamar tana bacci kafin ta kwantar da ita akan sofan ta shiga ciki ta ɗauko bargo tazo ta rufata dashi a hankali tace "sleep well"
fita tayi daga ɗakin ta shiga motarta sai company, tana shiga taga duk suka tashi harda man dake zanen karshe, kallonshi tayi ganin a tsayen ma yana cigaba da zanen saida ya gama ya aje, tace "kun gama?"
duk suka amsa da "eh"
tace "man kawo"
ɗauka yayi duk yaje ya mika mata, duddubawa ta fara, gani sukayi tayi murmushi abinda basu taɓa ganin tayi ba kenan, tace "yayi kyau sosai amma waya nuna muku wannan zanen?"
duk suka nuna man, tafiya tayi bata kara magana ba, cikin rashin sa'a taji kafanta ya juya zata faɗi man dake kusa da ita ya tiketa, rufe ido tayi dan tayi tsammanin ta faɗi ma, a hankali ta buɗe idon da sauri ta kwace jikinta daga nashi zata tafi yace "madam"
tsayawa tayi yazo da sauri ya durkusa a gabanta, gani tayi ya ɗaga kafarta ɗaya yana ɗaure mata igiyan takalmin ashe fita yayi ta taka shiyasa zata faɗi, saida ya gama ya tashi, murmushin da suka saba shida Ameesha shi yake yi, ɗauke kai tayi ta wuce office, komawa yayi ya zauna suna chatting da Ameesha yace "jibi zan karɓi albashina fa"
ta tura mishi emoji na tsalle alaman tana murna yace "zamuyi shagali"
chatting suke kamar basu jima da rabuwa ba.
ta gama shirya duk zanen sannan ta fita ta bawa driver, dawowa tayi ta nuna ɗaya daga cikin matan da suke aikin tace "muje ɗakin hoto ana buƙatan model wacce zamuyi amfani da hotonta wajen sawa akan sabbin rigunan mata da za'a kawo"
tashi tayi budurwa ce fara amma gajeruwa kuma tanada kiɓa sosai, nunashi tayi sai yau yaji ta kira sunanshi tace "Abdool tashi ka ɗau camera kafin na fito ki canja kaya wanda zaki sa yana can ciki"
da sauri ta amsa da "to"
shiga ciki tayi ta canja kayan, Abdool ya ɗau camera ya rataya a wuyanshi ita kuma manal ta shiga ta fito da kayan makeup nasu na company, me makeup ta shigo ta fara makeup, wani keɓantaccen ɗaki ne me tsananin kyau a ciki suke hotunan kuma suna samun models masu kyau, saida aka gama kwallinyan manal ta nuna mata wajen zama tace "yawwa ki tabbatar kinyi style masu kyau wanda zasu ja hankalin masu kayan"
tace "to"
Abdool ne ya fara ɗaukan hoton yana kallo, manal tazo tana kallo ta cikin camera, tsaki taja tace "duk style basu ba ki canja style"
canjawa tayi, ta kara kallo tayi tsaki tace "basu yi"
akalla sunyi hoto ya kai kala 20 duk ba wanda yayi, cikin ɓacin rai tace "tashi na gwada miki yadda zaki zauna da kuma yadda model suke ɗaukan hoto, dole sai kin sama very sexy"
zama tayi akan kujeran, zaman ma irin na models kafarta ta ɗan tura baya yayinda ta ɗan turo kirji gaba kaɗan, tace "idan kin zauna haka, sai kin lumshe ido kin buɗe kamar haka"
lumshe ido tayi ta buɗe, tasa hanu a kanta ta cire ɗankwalin ta bazo gashinta baya ta ɗan ɗaga kai kaɗan ta kalli camera tace "kamar haka"
wani irin murmushi Abdool yayi ganin yadda tayi kyau cikin hoton daya ɗauka mata, jin karan hotuna da yake ɗaukawa ta kalleshi, da hanu yayi mata alman like, a fusace tace "me kake...."
yatsa ɗaya yasa a baki alaman tayi shiru, shirun tayi ya kara ɗaukanta wani kafin ya tafa hanu yace "wow madam kece model daga yau"
haɗa rai tayi, bai nuna mata hoton ba kuma bai jira tayi magana ba ya fita, computer ya nufa da kanshi ya gyara hoton yayi printing, ta fito a fusace zatayi masifa taga ya manna a jikin bangon office, duk suka kalli hoton suka fara tafi, "yau madam ce da kanta ta zama model"
atake suka tura, cikin mamaki da ganin karfin halin Abdool da take taji wayarta yana faman ringing ɗauka tayi taji ance "wannan hoton approved ba jikin kayan ba manager yace har jikin kayan makeup na wannan shekaran wannan hoton za'asa"
batayi magana ba ta cire wayan, wani kiran ta kuma gani a wajen ta ɗauka ji tayi ance "muna magana da c.e.o na m.u.m designing?"
a hankali tace "eh"
akace "munga hoton da za'asa a jikin kayan wannan shekaran muna neman izini mu ɗaura hoton a kayan company ɗinmu da zaizo daga kasar India, turaruka ne muke yi a company ɗinmu idan kin amince?"
a hankali tace "na amince"
sauke wayan tayi man dake rike da waist yana kallonta yaga ta saki wani murmushin daya kara fitar da kyawunta, gani yayi ta tafa hanu tace mishi "well done"
murmushi yayi, ta juya ta tafi, koda aka tashi ameesha tana jiranshi kamar kullum yana fitowa ya rike hanunta suka shiga mota.
*Jiddah Ce...*
08144818849
managarciya