DUHU DA HASKE: Fita Ta Huɗu 

DUHU DA HASKE: Fita Ta Huɗu 


  DUHU DA HASKE


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 4*


                 ~A kofan gidansu ameesha ya tsaya itace ta fara sauka sannan shima ya sauko, hanunsu sarke dana juna suka shiga cikin gidan, karamin gidane madaidaici, yana da ɗan kyau irin na masu rufin asiri gini da komai irin na gidansu man ne, wata kyakkyawar mata ce tana da ɗan kiba zaune akan kujera tana gyara farcenta, ganin sun shigo jikinsu a mace taji a ranta yauma babu sa'a kamar kullum basu samu aiki ba saide yau taga yanayinsu ransu a ɓace sosai musamman man, cikin sanyin murya tace "Abdul kuna lafiya?"
a hankali ya jijjiga kai, ganin gashin kanshi a hargitse ta kalli ameesha dake kakalo murmushi da kokarin nuna ba abinda ya faru tace "Ameesha kuna lafiya?"
da sauri tace "eh Unty muna lafiya"
girgiza kai tayi tace "ameesha nice na haifeki nasan halinki da ɓoye damuwa shima Abdul nice na raineshi tun yana jariri kullum yana tare dani nasan ɓacin ranshi kuma nasan farin cikinshi akwai abinda kuke ɓoyemin"
danne kukan da yazo mata tayi sannan ta durkusa kusa da ita ta zuba hannayenta akan cinyarta tace "Anty muna lafiya babu komai"
daga nan ta tashi ta shiga ɗaki, akan kujeran da sukaji jiki kaɗan ta zauna ta kifa kanta a hanun kujeran ta fara kuka, shigowa yayi ya tsaya a bakin kofa ya harɗe hanu a kirji ya zuba mata manyan sexy eye's nashi masu kama dana turawa, ganin kukan yana karuwa ya taka a hankali ya isa inda take, zama yayi a kasa daidai inda ta aje kanta shima ya kwantar da kanshi a wajen yana kallon fuskanta da yake kusa da nashi, cikin kuka zata juyar da kanta yasa hanu ya hanata juyawa shima hawaye ne ya fara wanke mishi fuska, da sauri ta share hawayenta tace "man kukan me kake?"
yace "kin manta munyi alkawarin ba zamu bar ɗaya a cikinmu yayi kuka shi kaɗai ba? kin manta munce zamu rinƙa sharing damuwanmu tare? munsha wahala tun muna yara ƙanana iyayenmu maza suka mutu suka barmu a cikin wannan rayuwan da babu daɗi, bana samun farin ciki idan ban ganki ba, koda rabin awa nayi ban ganki ba sai na kira wayarki naji muryanki nake samun nutsuwa haka kema, kinsan kowane ɗigon hawayenki yanasa zuciyata tana zafi sosai, meyasa kike kuka bayan kin san haka? ba kince ke jaruma bace?"
share mishi hawayen tayi sannan ta share nata, murmushi tayi tace "na daina kuka, ba zan kara kuka ba, kaima ka daina?"
jijjiga mata kai yayi, tace "to yanzu sai ina kuma zamu fara neman aiki?"
ɓata rai yayi yace "ni gaskiya ki daina min maganan neman aikin nan kullum bana hutawa"
jan kumatunshi tayi tace "kaine babba a cikinmu ya zama dole ka nemi aiki domin ka ɗauki duk ɗawainiyanmu idan ka zama me kuɗi ai zamu huta"
yace "ba kince bakya son nayi kuɗi ba?"
tashi tayi tana kwance rigan sanyin dake waist nata tace "no faɗa kawai nake nasan koda wani irin kuɗi kayi ba zaka taɓa mantawa da childhood friend naka kuma babbar kawar ka ba wato Ameeeeeeshaaaaa"
dariya yayi dan yadda take magana kamar karamar yarinya harda ɗaga hanu, ya leka kofa yace "Anti akwai tea?"
daga can zaune tace "akwai amma ku ragewa farhan dan ya kusa dawowa daga makaranta"
yace "to"
wajen da suke aje tea flaks yaje ya ɗauko cup guda biyu ya zuba a ciki, tea sai kamshi yake, ameesha canja kaya tayi zuwa riga dogo na material, cire ribbon tayi ta bazo gashinta baya sannan ta zauna a kasa inda yake zaune akan carpet ɗin ɗakin, ta ɗauki shayin itama ta fara sha, ido ta zuba mishi yace "what?"
girgiza kai tayi tace "nothing"
cigaba sukayi da shan shayin har suka gama yace "muje mu ɗauko fahad a school"
tace "ka manta wannan rakwaɓaɓɓen motar taka ta ɓaci?"
yace "a kafa zamuje saimu biya school nasu Imran mu dawo tare"
tashi tayi tasa hijabi dogo ta fesa turaren da Anty ta siya mata sannan tazo wajenshi tace "kaima bari na fesa maka"
fesa mishi tayi yana murmushi yace "kinason kamshi"
aje turaren tayi tace "kamar yadda kake so ba?"
fita sukayi a tare suna hira cikin farin ciki kamar babu abinda ya faru, yace "Anty bari muje school mu ɗauko fahad kafin nan an tashi wasu Imran saimu ɗaukoshi"
tace "to shikenan ku kula sosai Allah ya tsare"
Ameen suka amsa a tare, binsu tayi da kallo a ranta tace "suna warware matsalarsu tare, ya Allah kada ka karesu daga kowane sharri"
tafiya suke akan titi suna hira man yana dariya domin ameesha tana bashi labari, dama idan kanaso kaga yana dariya to saide idan suna tare da ameesha saɓanin haka mugun miskili ne, baya magana kuma baya sakewa da mutune, sun iso dab lokacin da aka tashi wasu fahad, kyakkyawan yaro ne fahad yana kama sosai da yayarshi ameesha ba zai wuce 12years ba yana ganinsu yazo da gudu ya faɗa jikin man yace "yeeee ya Abdul yau nasan zaka siyamin ice cream ɗin can"
nuna mishi me ice cream yayi, waro ido man yayi sanin baida ko sisi a aljihunshi, zaiyi magana ameesha tace "ai gashi ma ya bani kuɗin da zan siya maka dashi"
nuna mishi ɗari biyar na hanunta tayi da mamaki man ya kalleta sai kuma yayi magana a kunnenta ta yadda fahad ba zaiji ba yace "aina kika samu kuɗi?"
a kunnenshi itama tayi magana cikin raɗa tace "a jakan umma ɗazu na sace"
waro ido yayi fahad yace "muje to"
zuwa sukayi suka siyi na 500 aka basu guda huɗu karɓa tayi tana sha shima man yana shan nashi fahad ma haka, rike ɗayan tayi wa Imran, saida suka shanye suka tafi zuwa school ɗinsu Imran, a lokacin aka tashi musu sabida secondary suke, yana ganinsu farin ciki ya kasa ɓuya a fuskanshi, ameesha tace "guess what?"
taɓe baki yayi alaman bai sani ba, ta ciro hanunta data ɓoye a hijabi tace "ice cream for you"
cikin jin daɗi ya karɓa yana mata godiya, sha zai fara ta karɓe tace "nice zan baka"
buɗe baki yayi tana bashi man ya tsaya kawai yana kallonsu, a kullum suna farin ciki ne sabida ameesha bata barin kowa cikin damuwa, saida ya kusa shanyewa tasa a baki ta shanye sauran, turo baki Imran yayi yace "dama nasan kece kika siya shiyasa ba zaki barni na shanye duka ba"
dariya tayi tace "sorry gobe zan siya maka wani"
yace "aina zaki samu kuɗi?"
sun fara tafiya ta kalli man ta kashe mishi ido alaman kada yace itace ta ɗauka, tace "Allah zai bani"
da haka suka isa gidansu man, suna shiga umma dake bakin kofa tace "waya ɗau 500 nawa a jaka?"
shiru sukayi harda ameesha dake rarraba ido, umma tace "ameesha waya ɗau 500 ɗina?"
da mamakin Imran yaga ameesha ta nunashi tace "inaga Imran ne dan naga sa siyi ice cream"
waro manyan idanunshi yayi yama kasa magana, man shima kallonta yake yadda tayi maganan kamar da gaske, umma tace "Imran meyasa ka ɗaukemin 500 baka tambayeni ba?"
zaiyi magana tace "rufemin baki baka sha ice cream ba?"
a hankali yace "nasha"
tace "to wallahi ka kiyayeni"
fahad zaiyi magana ameesha ta rufe mishi baki tareda ɓalla mishi harara"
umma tsaf tasan ameesha ce ta ɗauka domin tasan itace da karfin halin iya ɗaukan.
man wucewa yayi ciki ameesha tace "umma sai hakuri kin san yaro ne bai wuce 20years ba"
kallonta yayi ta ɗauke kai tana dariya, umma a ranta tace kamar ita ɗin wata babba itama ba 22years take ba?
shiga sukayi ciki har suka ci abincin rana Imran baiyi magana ba sai kumbura yake kamar zai fashe, duk sanda ta haɗa ido dashi saita kwashe da dariya.

safiyan ranan ta tashi a gajiye domin bikin gama school nata da sukayi jiya dana buɗe company ɗinta ya bata wuya ta gaji sosai, kwance take akan makeken gadonta tana rungume da pillow tayi rub da ciki, baƙin riga da wando na bacci ne a jikinta silk me kyau, bakin kayan ya bawa farin fatarta daman kara bayyana kyaunshi, cikin bacci take turo baki dan tana jin bayanta yana mata ciwo alaman gajiyan, turo kofan Ammi tayi itama tayi kyau cikin riga dogo na atamfa da beast a wuya da hanun rigan, hanunta rike da plate wanda yake ɗauke da glass cup ɗin da aka cika da yellow ɗin juice, zama tayi a gefenta ta ɗan bubbugata a hankali tace "manal? manal? wake up karfe 12 fa yayi"
cikin bacci ta murza ido a hankali ta buɗe dara daran idanunta tana kallon Ammi, idonta ta kai kan agogo me adon ɗawisu dake manne a jikin bangon bedroom nata, a hankali ta tashi tana gyara wuyan riganta daya sauka, rungume Ammi tayi cikin muryanta me cike da izza da yanga tace "good morning my ammi"
ammi tayi murmushi ta mika mata cup ɗin tace "ga juice dana haɗa miki da kaina nasan kina so sosai kuma yana kara kuzari"
karɓa tayi ta ɗaura a bakinta a hankali ta shanye tace "wow ammi kinsan duk duniya wa nafi so?"
girgiza kai tayi 
tace "kece nafi so duk duniya banason kowa ya shiga tsakanina dake, daga ke sai dady ina sanshi sosai, sannan yadda kike son dady bana tunanin akwai masu irin wannan soyayyan a duniya yanzu"
murmushi ammi tayi tace "kin san meyasa nake son dadynki?"
girgiza kai tayi, ammi tace "sabida na yadda dashi, na bashi yadda hundred percent, tun ina shekara 20 nake son dadynki har iyayena na rabu dasu sabida shi"
da sauri ta waro ido tace "Ammi barin iyayenki sabida namiji?"
murmushin gefen baki tayi sannan tace "manal idan akace miki soyayya an gama komai, naso dadynki kamar raina, na soshi fiyeda yadda nakeson kaina, kuma har yanzu ina mishi wannan son, ko kaɗan bana zarginshi hasalima duk abinda zai kawo zarginshi a raina kawar da abin nake sabida nasan ba zai taɓa cutar dani ba duba da soyayyan da nake mishi, yasan na samu matsala da iyayena sabida shi, hakan yasa ko kishiya baiyi min ba, kuma yayi alƙawarin ba zaimin ba"

sauka tayi daga kan gadon tace "Ammi gaskiya kinason dady nima ba zanso ganin ranan da zai cutar dake ba, nasan ma ba zai taɓa yin hakan ba"
har tayi wanka ta fito ammi na zaune tana jiranta, koda ta fito dogon riga me kyau kawai tasa sannan suka fito tare, akan chinese carpet ɗin dake tsakar falon suka zauna, manal ta janyo babban warmer ta zuba abinci wanda yake kamshin spices, ci ta fara suna hira da ammi, dady ya fito cikin shirin farin shadda ɗinkin babban riga shadda da yaji zubi me kyau, yayi kyau sosai yana zuba kamshi hanunshi rike da jaka da kaya a ciki, ganin manal tana cin abinci yace "my love yau kice kika kyale ɗiyata taci abinci bana nan?"
murmushi ammi tayi sannan tace "ni ai ba zan shiga tsakaninku ba kunfi kusa"
manal tace "to dady abar zancen abinci where are you going with bag?"
kallon ammi yayi yace "baki faɗa mata zanyi tafiya bane yau?"
ammi ta dafa kai alaman mantuwa tace "oh sorry wallahi na manta kasan na saba idan zakayi tafiya ma a bakinta nake ji"
manal tace "dady ina zaka?"
yana kallon agogon hanunshi yace "zanje Abuja kuma zanyi kwana uku kafin na dawo ina fatan zaki fara kula da company ɗinki daga gobe"
tashi tayi ta rungumeshi tace "dady gaskiya zanyi kewarka"
yace "kwana uku kacal da zanyi kuma ai gaki da amminki"
sakinshi tayi tace "to dady ka dawo lafiya"
yace "Allah yasa"
kallon ammi yayi yace "my love babu bye bye ne?"
tashi tayi ta rungumeshi tace "Allah kiyaye hanya"
yace "ameen"
rike jakanshi tayi suka sashi a tsakiya har suka kaishi wajen mota ya ɗaga waya yace "gani nan zuwa"
katse wayan yayi yana ɗaga musu hanu har driver yaja motarshi suka fita, hanun ammi ta rike ganin tana cikin yanayin damuwa tace "ammi karki damu zai dawo"
cikin sanyin murya tace "manal ko kaɗan banaso yayi nisa dani, tunda iyayena suka rasu yake kula dani, kuma sun mutu basa min magana sabida na nuna nafi sonshi akansu"
girgiza kai tayi ganin hawaye yana cika idon ammin tace "banson wannan hawayen ya sauka daga idanun wacce nafi so a cikin wannan duniyan, ammi yadda nake jinki a raina ji nake zan iya yin komai akanki, duk wanda zai cutar dake ba zan taɓa barinshi ba"
Ammi tayi murmushi tace "manal nima ina sanki sosai amma inaso ki rinƙa sakin fuska manal wani lokacin ni kaina tsoronki nakeji"
murmushi tayi kawai taja hanunta suka shiga ciki, kwantar da kanta tayi a cinyarta tayi shiru tana kallon tv, a haka suka wuni a ranan, sai yamma likis ammi ta kirashi yana ɗagawa yace "my love"
cikin fara'a tace "na'am kun isa lafiya?"
yace "mun isa lafiya ƙalau gamu a Abuja ina nan ina kewarki"
rage volume tayi ta yadda manal ba zataji ba tace "nima inata kewarka"
yace "ina manal?"
mikawa manal wayan tayi tace "gata"
tana karɓa tace "dady ya hanya?"
yace "Alhmdllh hanya sai godiya mun iso Abuja lafiya"
tace "good dady gobe zan fara fita aiki"
yace "masha Allah ma'aikatanki duk na sanar dasu zasu fita saiki tsara yadda aikin zai kasance"
tace "to dady bye"
yace "bye"
bawa ammi tayi wayan suka cigaba da hira tana jinsu abin yana bata nishaɗi a ranta musamman da taga ammi tana dariya sosai da alama tana matukar son dady harma son da take mishi yafi wanda yake mata yawa, a ɗakin ammi ta kwana rungume da ammi cikin nutsuwa take bacci.

washe gari ammi tana shirya mata breakfast akan dining ta buɗe murya tace "manal ki fito mana"
saukowa tayi a hankali take taku kamar ɗawisu, ido ammi ta zuba mata har lokacin data sauko daga stair, riga da skirt na leshi tasa ɗinkin kamar a jikinta akayi, blue black ne kalan leshin farin fatarta ya fito sosai, batayi makeup ba amma ta shafa lipstick fari, ta ɗaura kanta step by step, karamin jessy veil a hanunta takalmin kafarta kuwa me tsini, tasa babban space baki a idonta ba karamin kyau tayi ba, kamshi take yi sosai kamar ka saceta ka gudu, saide babu fara'a ko kaɗan akan fuskanta, wani irin kwarjini take dashi na musamman domin ko ammi saida taji shaƙƙan yi mata magana koda shike ta saba da rashin fara'an manal, tace "masha Allah, ubangiji ya tsareki daga evil eye's, Allah ya tsare wannan kyaun naki duniya da lahira"
sai yanzu tayi murmushi kaɗan tace "Amin" 
a takaice tayi maganan, zata tafi ammi tace "ga breakfast naki"
girgiza kai tayi ta kalli tsadadden agogon dake ɗaure a hanunta tace "no zan siyi kifi a hanya ina saurin naje na fara aiki a cikin company ɗina"
ammi ta buɗe baki zatayi magana, ɗaga mata hanu tayi tace "no please"
fita tayi daga ɗakin, ammi tace "ya Allah kasa ta zama me sauƙin sha'ani ta rage wannan tsautsauran ra'ayin"
tana fita ta nufi babban compound na gidan, motarta ta shiga ta kunna, hon tayi da sauri me gadi ya buɗe wani kallo ta aika mishi lokacin da tazo fita daga gidan ganin yayi delay wajen buɗe kofan, saida ta wuce yace "ban san dalili ba amma na tsani wannan yarinyar tun ranan da tazo gidannan na samu wannan ciwon ƙafan har na zama nakasashe yanzu saida sanda nake iya tafiya, gata muguwa bata dariya ga raini ga jiji da kai, duk da Alhaji yace min ƴarshi ce ta cikinsu amma naji bana sonta"
manal driving take cikin kwarewa fuskarnan ba walwala, tafiya take tana jin waka a hankali yake tashi a motan, kallon wani restaurant dake nesa tayi a hankali tace "anan zan siyi kifi banson useless restaurant"
a kofan restaurant ɗin tayi parking sannan ta fito tana rufe marfin motan, juyawa tayi zata shiga ciki taga dady yana kokarin sa facemask a fuskanshi gefenshi wata budurwa ce zankaɗeɗiya, daga dressing ɗin dake jikinta zaka san wannan karuwa ce babba, domin kuwa kitso ne akanta har bayanta na attachment, ga kuma wani wando daya kama jikinta da riga ɗan karami tasa dogon takalmi yatsunta tasa nails dogo dogo, sai taunan cingum take tana kaɗa makullin mota a hanunta, dady bayan ya rufe fuskanshi da facemask ya ɗauko ledojin da sukayi takeaway ya rike suna tafiya, zuciyan manal ya bada wani sauti dum dum, ganin yarinyar ta yiwa dady side hug taji idanunta suna rufewa, da sauri ta juya baya ta yadda ba zai ganta ba har suka shiga tsadadden motan dake fake a gefe da alama na yarinyar ne, tana ganin sun fara tafiya ta kalli motarta zata shiga sai kuma taga wani matashin saurayi ya fito daga restaurant ɗin yana shirin tafiya, da sauri taje wajenshi tace "please ina neman taimako"
yace "okay name?"
ta nuna mishi motarsu tace "wancan motan nakeso nabi ko zaka bani aron motarka? ga can nawa ga makullin"
da mamaki ya kalli tsadadden motar data nuna mishi ya mika mata makullin nashi yace "idan baki dawo ba fa?"
cikin son bin dady tace "na bar maka"
da sauri yace "kin barmin kuma....?"
a tsawace tace "zaka bani ko bazaka bani ba?"
da sauri ya miƙa mata ta shiga da gudu ta fara bin bayan motarsu dady, bugun zuciyarta ne ya karu lokacin da taga motar ya nufi hanyan babban hotel me suna ENJOY GUEST PALACE ji tayi kan motar yana nema ya suɓuce mata, da kyar ta daure taci gaba da binsu har suka shiga ciki, itama shiga tayi Allah yasa glass na motan tinted ne ba zasu ganta ba, tana ganin dady ya fito ya cire facemask ɗin fuskanshi ɗauke da walwala, yarinyar ta fito ta rungumeshi, rufe ido tayi lokacin da taga sun haɗa baki, a hankali ta buɗe idon cike da hawaye ji tayi jikinta yana rawa, gani tayi sun nufi ciki suna rike da hanun juna, idanunta sunyi jajur, bakinta yana rawa tace "cheater"
jan motan tayi da mugun speed ta fita a hotel ɗin, hanyan gidansu ta nufa sai kuma tayi murmushin da ita kaɗai tasan dalilin yinshi sannan ta juya motar zuwa company, buɗe mata gate akayi ta shiga, a fusace ta fito tana taku fuskanta babu alaman dariya ko kaɗan, tana shiga duk suka tashi daga zaunen da suke kowa da computer a gabanshi, aje jakanta tayi a office nata ba tareda ta amsa gaisuwan kowa daga cikinsu ba, dawowa tayi ta tsaya, tsit sukayi kowa ya daina abinda yake yi suka zuba mata ido sabida ganin fuskanta zai nuna maka ita ɗin wacece, tace "da fatan kun san wacece ni?"
kowa yace "yes madam"
murmushin gefen baki tayi sannan ta haɗa rai tace "aiki kukazo anan ba wasa ba, ga dokokin da zan baku wanda idan mutum ya tsallake koda sau ɗaya ne to na koreshi daga company ɗin m.u.m"
shiru sukayi kowa yana jinta baka jin karan komai sai ac dake aiki, hanu ta goya a bayanta tana zagayesu tana karewa kowa kallo tace "a duk lokacin dana riga wani daga cikinku zuwa aiki to kada ma ya shigo min company na koreshi, bazan ɗauki uzuri ba koma menene ya faru ya zama dole azo aiki, na biyu idan na shigo kowa ya tashi ba zaiyu ina tafe kuna zaune ba har sai na wuce office ɗina kafin ku zauna, koda a rashin sani wani daga cikinku ya zauna ina tafiya tofa na koreshi daga aiki, na uku banason wasa ko dariya ba amince amin a company ba, aiki kukazo ba dariya ko wasa ba, na huɗu banason kazanta duk wanda yayi wani abu me kama da kazanta na koreshi, na biyar kowa ya zauna cikin shiri domin ko dare aka kiramu aiki ya zama dole a fito domin babu excuse, sannan na shida kowa yasan aikinshi ina fatan kun gane?"
da sauri sukace "mun gane madam"
tace "okay kowa ya fara duba zanen dana tura na sabbin style's ɗin dana zana zamu fara aiki dashi a matsayin sabon salo"
da sauri sukace "to madam"
maida glass nata tayi sannan ta wuce cikin tafiyanta me action"
office nata ta shiga ta zauna akan kujeran dake juyawa, ɗaga kanta tayi sama tana kallon tsararren p.o.p dake cikin ɗakin tana juyawa, cikin zafin murya tace "dady kayi cuta kuma na tsani macuci, dady na tsani macuci, meyasa zakayi haka?"
a hankali ta rufe ido ta kuma buɗewa, wayarta dake ringing ta kalla, sunan da tayi saving da best dady ta gani yana yawo, ji tayi zuciyanta yana zafi wayar ta ɗaga ta buga da bangon jikin office ɗin, nan take ya tawarwatse ya fashe, dunƙule hanu tayi cikin zafin murya tace "macuci"

Ammi girki take ta kira numbern manal ji tayi wayan a kashe, kara kira tayi taji a kashe, sauƙe tower ɗin tayi tace "manal da kashe waya? anya lafiya?"
shirya abincin tayi ta koma ɗaki tayi wanka, koda ta fito tasa abaya me kyau, kara kiran numbern manal tayi taji a kashe, kallon wayan tayi tace "ba lafiya ba"
da sauri sauri ta buɗe wardrobe ta ɗauko hijabi tasa, glass nata siriri fari tasa a idonta, tasa flat shoe me kyau ta ɗau makullin mota, abincin data dafa ta ɗibawa manal sannan tasa mata youghurt me sanyi a basket ɗin, fita tayi daga ɗakin ta kulle kofan falon, driver ta kira ta bashi makullin tace "kaini wajen aiki ɗin manal"
shiga tayi suka fita daga gidan, kasancewar sunje da dady jiya shiyasa ya gane wajen, suna isa ta kalli wajen parking bataga motar manal ba, da sauri ta fito daga motar ta ɗau basket ɗin, shiga ciki tayi taga duk sun maida hankali akan aiki, gyaran murya tayi duk suka juyo, tace "manal tazo?"
suka amsa da "eh tana office"
kai tsaye ta wuce office ɗin, knocking tayi bata amsa ba, kara knocking tayi cikin tsawan da yasa ammi yin baya a tsorace tana dafa kirji tace "banson ganin kowa"
jikin ammi yana rawa tace "ma..ma..manal kina lafiya kuwa?"
jin muryan ammi tayi saurin saisaita kanta, da sauri ta tashi tana kakalo murmushi taje kofan ta buɗe, suna haɗa ido ta sakar mata kyakkyawan murmushi tace "ammi kece?"
gyaɗa kai tayi tana kallonta, hanunta ta rike da basket ɗin tace "shigo mana"
shigowa tayi a ɗan tsorace tace "manal ina kiran wayarki a kashe kuma banga motarki anan ba"
kujeran ta nunawa ammi wanda ta tashi akai sannan ta zauna akan table tana kusa da ammin tace "wallahi wayar ta faɗi kin ganshi can"
kallo ammi tayi tace "ya akayi haka? ina motarki kuma?"
dafa kai tayi tace "am sorry ammi wallahi motar wani ne ya ɓaci a hanya kuma yana sauri sosai mamanshi babu lafiya yanaso ya kaita hospital, saina fita a nawa na bashi sai nace ya bani nashi shiyasa kikaga banzo da nawa ba"
cikin fara'a da jin daɗi ammi tace "wow my daughter ta girma, taimako yanada daɗi manal kuma naji daɗi da kikayi haka Allah miki albarka"
a hankali tace "ameen me kika kawomin ne ammi?"
buɗewa tayi jin kamshi ta lumshe ido tace "my best momy in the world gaskiya ina sonki ammi"
murmushi tayi ta ɗau spoon ta fara bata a baki, karɓa take tana ci badan taso ba sai dan son ɓoyewa ammi abinda yake faruwa, tasan idan taji wannan labarin zata iya rasa lafiyarta ko kuma ta mutu domin tasa dady a rai kuma ta bashi yadda, ammi tace "kinga dadynki ma inata kiranshi bai ɗauka ba kuma nayi missing na...."
huci ta fara tana dunƙule hanu ta yadda ammi ba zata ganta ba, ɗauke kai tayi tace "na koshi"
da sauri tace "baki koshi ba ki buɗe baki..."
"nace na koshi!!!"
tayi maganan a tsawace, tsit ammi tayi tana kallonta, ganin ammin ta tsorata kawai ta rungumeta tayi shiru, a hankali tace "manal ki rinƙa control na zuciyarki kinji?"
tace "to ammi"
sakinta tayi tace "na gode da abinci tashi na raka ki"
rike hanunta tayi ta ɗau basket ɗin suka fita, tana tafe tasa hanu ta bayan ammi ta rungumeta, har wajen mota ta kaita, koda zata shiga tayi mata kiss a goshi tace "na gode saina dawo"
gyaɗa kai tayi tace "please ki dawo da wuri sabida kinga ni kaɗaice a gida sai bana jin daɗi"
murmushi tayi tace "to ammi"
har suka tafi tana ɗaga mata hanu, saida suka fita ta haɗa rai ta juya tana tafiya, jin ammi take a cikin zuciyarta ko kaɗan batason abinda zai cutar mata da ita, ji take zata iya yin komai akan farin cikin ammi, koda tazo shiga suna ganinta suka mike saida ta shiga office kafin suka zazzauna.


_Jiddah Ce..._
08144818849