DUHU DA HASKE: Fita Ta 37

DUHU DA HASKE: Fita Ta 37


DUHU DA HASKE:


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 37*


                 ~Manal da kanta ta yiwa kanta lalle tayi kitso sannan ta shirya komai nata, ranan juma'a aka fara shirya ɗaura aurenta, cikin fahad da Imran babu wanda ya kula, su ameesha kawai suke bawa kulawa har man basa mishi magana, ammi tana ɗan zuwa ta duba ameesha domin Imran ya faɗa mata duk abinda ya faru ta kasa yin fushi da meesha tana kula da ita, yazeed yana zaune yaga sakon text message ya shigo, a hankali ya duba yaga manal tace "congratulations yau za'a min aurena kai kuma saika gama sauran aikin ina fatan baka ɓatar da alluran da zaka yiwa ameesha ta dawo hayyacinta ba?"
ya tura mata "ban ɓatar ba yana nan a inda na ɓoye"
tace "good"
murmushi tayi tace "momy na baki wani labari?"
momy tace "ina jinki"
tace "wani allura ne me kashe gaɓoɓi da fitar da mutum a hayyacinshi, alluran guda biyu ne ɗaya na ciwon ɗaya kuma na magani, saina bawa yazeed na ciwo dana magani ya karanta sannan yace bani na ciwo na yiwa Ameesha, saide kin san me?"
momy tana haɗa turare tace "a,a"
kwanciya tayi a cinyar momy ta lumshe kyawawan idanunta tace "duka na ciwo na bashi babu na magani a ciki"
murmushi sukayi su duka momy tace "kin tabbata ƴata"
tace "daga karshe zan juye komai akanshi kinga idan ya mata wannan ta mutu saina bayyana komai wa hukuma daga nan idan an tafi dashi ba kece da riba ba?"
momy tace "kwarai nice"
dariya sukayi su duka, tace "momy nayi missing na Abdool"
lumshe ido tayi a ranta tace "kiss, hug, and the best s**"
murmushi tayi me kyau sannan tace "komai zai zama nawa, manal bata haɗa abinda take so da kowa"

Bayan sallan juma'a tayi wanka me kyau cikin farin leshi, momy ce tayi mata makeup tayi kyau sosai sai kamshi take ta rufe kanta da farin mayafi tayi bala'in yin kyau, mutane suka taru aka ɗaura aure, tana zaune a falo itada momy suna hira ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya man suka shigo da yazeed sunyi kyau cikin fararen shadda, a hankali ta tashi taje ta rungumeshi, bakinshi ya kai kunnenta yana shafa bayanta yace "congratulations manal umar maidawa"
kallon yazeed tayi ya ɗauke kai, man yace "kinyi mamaki dana kiraki da wannan sunan ko?"
a lokacin Imran ya turo ameesha akan wheelchair yazo da ita dakin, ammi ta fito daga ɗaki tayi kyau cikin shadda fari tace "congratulations man naso ayi wannan auren babanku yana raye amma duk wanda Allah yace kwananshi ya kare babu me karawa"
ya saki manal yaje wajen ameesha ya durkusa ya rike hanunta yace "my wife"
a firgice manal ta kalleshi tace "your wife?"
murmushi me sauti yayi ya tashi yayi hugging na ameesha sannan ya mata kiss a gefen kumatu yace "manal waya gaya miki Allah yana bawa mugu dama sau biyu?"
tace "man karka kara cewa ameesha matarka a gabana"
cikin jin zafi da kuma jin bakin cikin sanin manal da yayi a rayuwarshi ma ya durkusa kasa bakinshi ya haɗa dana ameesha a hankali yake kissing nata yana kallon idonta dake hawaye, ammi ta sunkuyar da kanta Imran da fahad ma haka, hanan tayi tafi tana hawaye tace "congratulations hakika duk wani wahala yanada karshe manal keba mutum bace keda mahaifiyarki ku macizai ne"
a hankali ya saki ameesha yaje wajen yazeed, hanu ya buɗe mishi sukayi hugging juna yace "akwai wanda ƴan uwanka ne kawai ciki ɗaya ne baku fito ba, haka yake tsakanin nida yazeed, ba zai taɓa yadda a cutar dani ba kamar yadda ba zan yadda a cutar dashi ba, kinyi zaton Abba yana prison ko?"
girgiza kai yayi yace "Abba yana nan lafiya ƙalau duk wani shiri da kikeyi idonmu akanki domin ammi taji duk abinda kuke faɗa da momy"
yace "momy kin bani mamaki"
momy tace "ni me nayi? manal ce take yin komai bani ba"
manal wani kallo take aikawa momy tana murza hanunta ganin tanaso ta juye mata komai, Abba ne ya shigo ɗakin man yace "baba ne kawai kukayi nasaran kashe shi shima sabida kwananshi ya kare ne, sannan na auri ameesha ita batasan abinda muke shiryawa ba"
Abba ya kalli momy yace "na gode sosai rukayya, koda shike ni ban sanki a rukayya ba a mahaukaciya na sanki, sannan na sakeki saki uku"
man yace "nayi kuskure dana saki manal saki ɗaya a kotu, manal ni man na sakeki saki uku"
ammi tace "manal nice fa na rikeki tun kina yarinya kina ganin zan iya mantawa da ke ne? ba zan taɓa mantawa da kowane tabon halittan dake jikinki ba, tun ranan da kika shigo na gane kece ba wata Amal"

tafiya ɗaki tayi ta fito da akwati a hanu ta rike hanun momy kamar zasu tafi tace "mune dai matsalan family ɗinku ko? to zamu tafi amma ku sani ba zan taɓa bari ka rayu da ameesha ba"
kafin su ankara ta harbe ƙafan ameesha wacce ta tashi daga zaunen tana takowa inda take, hanan tace "wayyo meesha"
da gudu taje ta riketa, ɗaga bindigan tayi zata kara harbi man yayi kukan kura ya kwace, harbeta yayi a ciki sannan ya kara mata wani a kirji ya kara mata a ciki, momy data buɗe kofa zata gudu ya harbeta a bayanta faɗuwa tayi a wajen, ya saita kanshi da bindiga zai harba yazeed ya fizge ya ɗaga sama harbin yabi iska, a firgice yace "kanada hauka ne? zaka kashe kanka sabida me?"
yace "sabida nine nasa rayuwar family ɗina a matsala sabida ni ake shigan wannan halin"
manal da take gigin mutuwa tace "koba komai naji daɗi domin manal ta mutu ne a hannun abdool"
hanan ce ta fara duba ƙafan ameesha itada su ammi basu ma kula akwaisu momy a wajen ba, Abba yace "waɗannan mutanen ya kamata mu ɗaukesu ba tareda kowa ya sani ba muje tsakiyan daji mu binnesu da kanmu"
yazeed yace "tabbas amma sai dare yayi sannan zamu ɗaure fuskansu da bakin kyalle sabida ko gawansu ba abin yadda bane.
sai dare sukayi kamar yadda sukace, saida sukayi nesa da gari kafin suka je suka binnesu suka dawo gida, hanan ce take kula da kafan ameesha wanda yaji ciwo, Imran da fahad farin ciki suke ciki sosai.

bayan kwana uku, ameesha ƙafan har yanzu babu sauki Hanan tace dole zafin ciwon zai dameta sabida zafin bullet ba wasa ba, ammi itace take musu girki kowa yana ci amma man duk yana samuwa da ciwon ameesha, yauma kamar kullum suna cin abinci babu ameesha a hankali ya kalli yazeed ya langwaɓar da kai kasa kasa yace "ina so naje naga ameesha ina jin kunya"
yazeed yace "yaushe ka fara kunya?"
tsaki yaja yace "dama banda kunya ne?"
ammi ganin ya kasa nutsuwa yaci abinci tace "man jeka duba matarka mana ka kai mata abincin ɗaki"
da sauri yace "to"
tashi yayi ammi tayi murmushi tace "ɗan kaniya duk ya kasa nutsuwa"
shiga yayi babu sallama yanzu ta fito daga toilet tana ɗingishi tayi kyau sosai, gyaran jikin har yanzu bai barta ba ya haɗu da fatarta me kyau, kasa motsi tayi domin tasan duk tafiyan da zatayi sai jikinta ya girgiza kuma ya tsareta da idanu, tace "wai miye haka kai baka sallama ne?"
yace "to ai ni mijinki ne me na sallama"
turo baki tayi tace "to ka fita zansa kaya"
karasowa yayi ya aje plate ɗin yazo inda take, ɗagata yayi ya ɗaurata akan gadon zata tashi ya bita ya danne, tace "man kowa fa yana falo" yace "to sai me? kwana uku da da aure ko kyakkyawan hug babu"
tace "nikam ka kyaleni"
ya kwaikwayi muryanta yace "nikam ba zan kyaleki ba"

"i miss your lips"
zatayi magana taji ya haɗa bakinshi da nata a hankali ya fara zame towel na jikinta yana bin jikinta da tafiyan tsutsa, lumshe ido tayi yana kallon idonta yadda ta kamu ya fara murmushi, gyara kwanciya yayi a jikinta yana taɓa duk inda yaga dama a jikinta, Imran ya shigo da juice da ammi tace ya kai musu, da sauri ya juya yana rufe idonshi, ganin basu san ma ya shigo ba ya buɗe kofan a hankali ya koma, ammi ta ɗan daga gira cikin manyance tace "ya dai? ya ka dawo dashi basu so ne?"
shiru yayi ya kasa cewa komai, ammi tace "wai ba magana nake maka bane?"
yace "no ban karasa bane kawai nace sai anjima sai a kai musu"
taɓe baki tayi tace "to aje kaci abincinka"
yazeed ne yayi murmushi ganin yadda Imran yake sunnar da kai akwai abinda ya gani dan tsaf yasan halin man, har sun gama cin abinci Abba yace "bari naje na huta na gaji sosai"
tafiya ɗaki yayi hanan ta tashi tace "ammi bara na ɗauko miki wani abu ki gani"
hanyan ɗakinsu ta nufa Imran yace "unty hanan?"
tace "yes"
yace "da kin bari anjima"

"meyasa?"
yayi shiru, yazeed yace "tunda yace haka ki bari mana"
zama tayi ta kwantar da kanta kan cinyar ammi tace "gaskiya ammi kowa da irin nashi ƙaddaran wallahi munsha wahala sosai gashi yanzu komai ya wuce"
ammi tace "komai ya wuce saura aurenki dana Imran dana yazeed kawai ya ragemin"
ɓoye fuska tayi tace "ni kunya nake ji"
Imran yana sosa kai yace "ko dai na gida zamuyi ne?"
cup ta ɗauka zata wurgeshi dashi ya tashi da gudu ya bar wajen yana dariya, tace "ɗan rainin hankali ka taɓa ganin inda yaya ta auri kani?"
yace "Allah huci zuciyar anty waifa gani nayi baki kula kowa sai nace ko dai na miki ne ni kike jira"
tashi tayi daga kwancen ta ɗau katon marfin flask tana binshi dashi, ihu yayi "wayyoo kiyi hakuri"
binshi tayi har bakin kofa ya buɗe zai fita a lokacin faruk ya shigo, yayi kyau sanye da kananan kaya yasa picap a kanshi, tana ganin ya ɓuya a bayan faruk ta fara kokarin kamoshi 
yace "ya faruk dan Allah ka ɓoyeni wallahi batada hakuri"
faruk yace "tanada hakuri mana taɓota kayi na santa tsaf batada magana ma sosai kaine da tsokana"
yace "ya faruk aina ka sani?"
yace "ai kullum muna waya da ita"
duk suka kalleshi, yasa hanu a baki ashe suɓul da baka yayi, yace "yi hakuri ki barshi zan rama miki koma me yayi miki"
karɓe marfin flask yayi yaja hanunta suka shiga ciki, yazeed yace "welcome"
gaishe da ammi yayi ta amsa cikin kulawa, yace "wai ina man?"
yazeed yace "yana ciki"
yace "ka mishi magana inata kiran wayarshi ina ya aje ne? kuma mutane sunata jiranshi a office"
yazeed ya kalli ammi data tashi yace "yana can yana lalube mana kanwa"
tsaki faruk yaja dan kasa kasa suke maganan yace "dan Allah ka mishi magana wallahi da wuri ake nemanshi"
yazeed yace "bari hanan ta mishi magana muje ciki"
yace "hanan kira yayanki man ya samemu a ciki"
tace "to"
suka shiga ita kuma ta wuce ɗakinsu, knocking ta fara ameesha ture man take ganin bema san ana knocking ba, cikin zafin da take ji da kirjinta ke mata tace "anafa knocking"
da kyar ya iya control ya saketa, rufata yayi da blanket sannan ya tashi yana layi, idonshi ya sauya kala ya koma jajur lips nashi har sun zama red gashinshi da ameesha ta hargitsa bai ko tsaya gyarawa ba, shifa rabonshi da abin tun kafin ya rabu da manal shiyasa yanzu baya iya control idan yaga ameesha musamman idan sun keɓe, buɗe kofan yayi hanan tace "barka ya man su ya faruk ne sukace na maka magana ka samesu a ɗaki"
gyaɗa kai kawai yayi ya ɗauke kai bai yadda sun haɗa ido ba, binshi tayi da kallo sannan ta kalli ameesha data rufe ido akan gadon kamar me bacci, shigowa tayi tace "gara ki buɗe ido nasan ba bacci kike ba"
buɗe ido tayi a hankali lips nata sunyi jajur kamar wacce ta shafa red lipstick, tace "ki bani simple dogon riga nasa"
buɗe wardrobe tayi ta ɗauko mata simple dogon riga ta wurga mata, a hankali ta tashi tana yaye blanket ɗin tasa rigan, hanan tace "ya faruk fa yazo"
tace "Allah? Ina yake?"
murmushi tayi tace "yana ɗakinsu ya man"
kallonta ameesha tayi ganin tana murmushi tace "to hanan sarkin love"
dariya tayi tace "nifa banson tsokana"
ameesha tace "miko min abincin naci"
da mamaki ta kalli abincin dama ba abinci suke ci ba tun ɗazu? da mamaki ta mika mata domin bata fiye yawan tambaya ba, ci ta fara tuna duk abinda yayi mata a hankali tace "amma fa da daɗi"
hanan tace "me?"
da sauri tace "babu"
murmushi kawai hanan tayi dan itafa Dr ce babu abinda bata sani ba.

shiga ɗakinsu yayi bai ko kalli inda su yazeed suke ba dan yasan halinsu, yazeed dake nunawa faruk abu a waya ya ɗago ya kalleshi, kwashewa yayi da dariya, ɓata rai man yayi, yazeed ya kasa rike dariyan harda rike ciki, faruk yace "dan Allah ka daina"
da kyar ya takaita yace "kayi wanka to mu tafi"
fuska a murtuƙe man ya shiga toilet yayi wanka koda ya fito kin kallonsu yayi saida yasa kaya yace "let's go faruk"
yazeed yace "to yanzu haka zaka tafi? na tabbata wannan fushin dan bamu barka kayi rel....."
pillow ya ɗauka kaman wani yaro ya danne yazeed dashi, dariya yazeed yake yace "yi hakuri bro yi hakuri...."
faruk me zaiyi banda dariya, yadda suke abu kamar yara wani lokaci yana birgeshi, idan ka gansu zaka rantse mamansu ɗaya babansu ɗaya, suma basa faɗa koda an tambayesu basa cewa iyayensu ba ɗaya ba, sakinshi yayi yace "faruk mu tafi"
tafiya suka fara yazeed yace "amma idan ka dawo zaka karasa ko..?"
tafiya yayi bai bashi amsa ba, yasan yazeed Indai ya gane baka son abu to ya kulla maka kenan..

*duhu da haske is 400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi opay, evidence via 08144818849*

Jiddah Ce...