DUHU DA HASKE: Fita Ta 35
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 35*
~Koda ya tashi daga nannauyan bacci yaji ya samu sauki sosai, wanka yayi ya fito daga ɗakin bayan yayi salla, Abba ne yazo da tsadaddun shadda masu kyau ya zuba a tsakiyan falon duk suna zaune yace "man ya jikin?"
a hankali yace "da sauki Abba"
"Allah kara sauki"
duk suka amsa da ameen, Abba yace "tashi ka zaɓi shadda wanda ya maka"
murmushi yayi cikin jin daɗi yaje ya zaɓi fari me kyau, Abba yace "ya maka?"
yace "eh"
Abba yace "yazeed jeka ɗauka kaima"
ɗaukan fari shima yayi me kyau, Abba yace "ya maka?"
yace "eh na gode"
yace "Imran jeka ɗauka"
Imran ya zaɓo me kyau blue dark, Abba ya tambaya ya mishi? yace eh, sai fahad shine karshe ya zaɓi blue shima akace ya mishi yace eh, Abba yace "saura ku matan"
ya bawa ammi da momy nasu irin ɗaya sukayi godiya, shida baba yayi musu kala ɗaya, sai kuma Ameesha da Hanan da kuma Amal anyi musu kala ɗaya leshi me matukar kyau fari kana gani kasan tsadadde ne, duk suka mishi godiya, washe gari kowa ya kai ɗinki, ameesha bayan ta dawo ta fara shiri itada hanan zasuje gyaran gashi sabida zatayi kitso ana gobe auren, tayi kyau cikin material tayi rolling kanta da pink na mayafi, hanan ms material tasa amma hula kawai tasa tasa flat shoe da mukullin mota zasu tafi Amal cikin hausanta da baya fita sosai har yanzu tace "na biku?"
sukayi shiru, ameesha taji ta bata tausayi tace "shirya ki bimu"
da sauri ta tashi ta fara shiryawa kayanta baƙi tasa sannan tasa matafi baki suka jera tare suka fita"
momy tace "ku dawo lafiya"
wajen wanke kai hanan ta kaisu dan itace take driving, a babban shagon wankin kai da gyaran jiki suka shiga, aka fara yiwa amarya saida aka wanke tulin gashinta sannan akayi mata gyaran jiki, sai hanan itama anyi mata wankin kai sai kuma Amal itama an gyara mata tulin gashinta sai murna take tana kallon kanta a madubi this is the first time data fara gyara kanta"
Ameesha ta kalleta taga tana murmushi tana kallon gashinta ta cikin madubi tace "kinyi kyau gashinshi yanada kyau"
tace "na gode"
hanan tace "ba gara a kitse miki ba?"
tace "a barni haka"
dariya sukayi ta sunkuyar da kai itama tana dariya, ameesha ta kalli hanunta tace "to yaushe zanyi lalle?"
Amal tace "na iya henna zanyi miki kuma na taho dashi daga saudi"
tace "yawwa idan mun koma gida da wuri sai kimin sabida banson zaman lalle wallahi"
tace "to"
hira sukeyi har aka gama, subhanalla jikin ameesha wani irin tsantsi yake yi ga sheƙi da kyau data kara, ga kuma cika da takeyi ko kaɗan bata ramewa, hanan tace "wai kekam amare suna ramewa ke kuma sai kiɓa"
tace "to me zai dameni?"
tace "aiko kece ya kamata ki damu"
tana driving tana magana, ameesha tace "damuwan me?"
tace "kinga ya man mugun jarababbe ne idan bakiyi hankali ba zaki shiga uku"
tace "na sani ai kawai dai bana sawa a raina ne sabida banso na rame"
hanan tace "kinga ya yazeed yace kada na faɗa miki ya nunamin gidan da zaku zauna keda ya man, subhanallah gidan ya cusa wanda muke ciki sau ɗari"
murmushi tayi tace "yayi kyau ni kuma nafi so mu zauna tare kamar yadda muka saba"
hanan tace "a'a ina, wannan ya man da baida kunyan? yanzu ma kamar ya cinyeki a gabanmu? gara dai ku tattara ku tafi can"
murmushi tayi, tace "Amal idan munci abinci saimu fara lallen ko?"
tace "eh"
ameesha tace "yanzu fa kin kware a hausa babu me iya siyar dake"
dariya tayi sosai tace "har yanzu dai da saura"
suna hira har suka isa gida, abinci sukaci sukayi salla kafin suka canja kaya zuwa na zaman gida, Amal ce ta shiga cikin ɗaki ta duba kayanta ta ɗauko wani lalle me kyau tazo dashi, kwaɓawa tayi ta zauna da kyau tace "to zoki mu fara"
zuwa tayi ta mika mata kafanta suka fara zana lalle, hanan tace "wow kin iya lalle haka? shine baki taɓa faɗa mana ba?"
murmushi kawai tayi, har bayan Isha basu gama lalle ba sabida kananan style take mata kamar wata amaryar kasar waje, har su man suka dawo ya zauna ya zuba mata ido, cikin shagwaɓa tace "ba'a ganin lallen amarya ya man ka tafi"
ya taɓe baki yace "za'a fara gani akaina babu inda zanje sai an gama miki"
ɓata rai tayi yace "ko me zakiyi saide kiyi ina nan ina kallon kyakkyawan amaryata"
hanan tace "ya man gaskiya ka tafi"
Imran ne yayi sallama ya shigo da ɗinki a hanunshi fahad na biye dashi fahad kamar zaiyi kuka shi kuma Imran ya haɗa rai zasu wuce man yace "kai daga ina kuke?"
sukace "wajen ɗinki"
man yace "to me ya sameku kamar zakuyi kuka?"
Imran yace "dan Allah ya man wannan ɗinkin amma na kanin amarya kuma kanin ango? kalli hanun fa kamar me kwasan kashi"
dariya man ya kwashe dashi yana kallon ɗinkin yadda aka buɗe mishi hanun kamar na mata bubu, ameesha ma dariya ta fara ganin fahad ma ya ciro nashi yana hawaye, ganin suna musu dariya fahad ya fara kuka, Amal ce ta kallesu sannan ta tashi daga lallen da take, zuwa tayi ta rike hanunsu ta zaunar dasu akan sofa, a hankali taje ta kawo musu ruwan sanyi ta bawa fahad a baki, imran ya karɓa da kanshi yasha, murmushi tayi tace "karku damu za'a iya gyarawa ai ko kuma ku canja dress"
fahad yace "ta yaya?"
wayarta da Abba ya siya mata irin masu ameesha ta ɗauka ta nuna musu wasu tsadaddun yaduka sannan tace "zaɓi wanda kukeso a ciki"
duk suka zaɓi ruwan zuma, tashi tayi ta shiga ɗaki cikin sanyinta ta fito da akwati babba, zama tayi kusa dasu ta buɗe a kasa kasa ta ciro wasu zafafan yaduka ta basu ruwan zuman tace "ku kai wani shago ayi muku ɗinki express"
kuɗi ta ɗauka ta basu tace "kuje ayi muku yanzu"
cikin jin daɗi suka fara mata godiya, a hankali ta ciro sauran yadukan farin ciki ta mikawa man tace "gashi yaya"
kallonta yayi itama tana kallonshi, a hankali ya karɓa yace "thanks"
mikawa yazeed tayi shi kuma coffee tace "yaya gashi"
karɓa yayi yace "na gode"
murmushi tayi tace "wannan na Abba wannan kuma na baba"
na baba fari sol na Abba ma fari, murmushi sukayi mata ameesha tace "an gode sosai"
tace "ba komai"
maida akwatin tayi tazo ta fara cigaba da lallen sai can dare yayi nisa kafin suka gama na amarya, tace hanan tazo tayi mata, yi suka fara tuni ameesha tayi bacci, suma sun tsaga dare kafin sukayi bacci, itama ta yiwa hanunta da kafa.
daga wajen karɓan ɗinki suka tashi lallen hanun Ameesha kamar inji ne ya zana tayi kyau sosai tasa Black abaya, itama Amal abayan ne a jikinta, sai hanan da tasa riga da skirt na atamfa, duk a gajiye suke duk wani ɗinkin da amarya dasu zasu sa saida suka karɓo, ameesha tace "zanje kitso kuma dan nasan anjima mutane zasu cika gidannan kafin ma gobe"
Amal tace "na iya zanyi miki"
murmushi tayi tace "karki damu kin gaji sosai ki bari zanje Amin"
tace "saide idan bakiso nayi miki"
ameesha tace "a,a to kimin"
saida sukayi la'asar kafin ta zauna a kasa amal na kan kujera ta fara fenta mata wasu irin kananan kitso masu bala'in kyau, hanan tace "wow gaskiya kin haɗu komai kin iya"
ameesha tace "na gode sosai"
abokan momy na arziki da kuma makota ne suka fara shigowa gidan domin tayasu aiki, Abba da baba suna can suna shirye shiryensu suma, ameesha kitso ake mata me matukar kyau, sai dare aka gama, ko waya da man batayi tsaban gajiya, safiyan juma'a ranan da za'a ɗaura aure ta tashi da sauri domin tayi breakfast ta samu taje kotu anyi mata kira na musamman tanaso ta fita ko hanan karta sani dan zasu hanata, da kayan baccin a jikinta ta shiga kitchen ta fara breakfast cikin sauri take yin komai, ita kaɗai tana magana tace "gara na gama da wuri naci a kitchen ɗin na saci hijabi da dogon rigan hanan nasa na gudu anjima na dawo tunda case na gaggawa ne"
shigowa yayi ganin itace kaɗai ya rufe kofan, ta baya ya kankameta yace "oh I miss you so much Baby"
tace "man ya kake?"
cire hulanta yayi yana kallon kitsonta sai kuma yayi kiss a kitson yace kinyi kyau sosai, ji nake kamar lokaci baya tafiya"
tana cigaba da aikinta tace "sakeni to da mutane a gida zasu shigo"
manna bakinshi a wuyanta yace "ni ki barni nayi missing naki sosai"
batayi magana ba tana ji yana kissing wuyanta aikinta kawai take yi, Amal wacce ta saba tashi da wuri tayi girki taga kitchen a rufe, tace "wayyo yau nayi late"
buɗe kofan tayi, a hankali ta juya ganin man yana kissing wuyan ameesha ya kankameta kamar za'a kwace mishi ita, kasa ƙasa suna hira, tayi gyaran murya man ya saki meesha kallonta yayi ta mishi murmushi, meesha tace "na gode Allah da tazo"
fita yayi ita kuma ta shigo, ameesha saida taga ya tafi tace "dan Allah inaso ki taimakeni Amal"
tace "dame?"
tace "wallahi wani case aka kirani ana nemana da gaggawa a kotu ya zama dole na fita amma banso ko hanan ta sani"
Amal tace "kina ganin fitan babu matsala?"
tace "babu matsala amal ki taimakeni tunda kin shigo da dogon hijabi ki bani na tafi dashi zan rufe fuskana ba lalle a ganeni ba"
hijabin ta cire mata tace "gashi amma ki kula sosai kuma kin san anjima za'a ɗaura miki aure kiyi sauri ki dawo"
tace "insha Allah"
hijabin ta karɓa tasa sannan ta fita ta kofan baya tana rufe fuska, bata yadda ta shiga motar gida ba ta wuce bakin titi domin shiga taxi, Amal kuma ta fara girkin cikin natsuwa take yin komai, saida ta gama komai taje ta shir shirya, jim sosai kafin ta fito daga ɗakin tareda momy suna hira kaɗan kaɗan, ammi ma ganin time na cin abinci yayi suka fito tareda baba mutanen da sukazo biki duk dasu aka taru zasu fara cin abinci, knocking aka fara Imran ne yaje ya buɗe kofan kallonsu yayi ganin police sukace "zamu iya shiga?"
matsa musu yayi suka shiga ciki, ammi a firgice ta kallesu tace "meya kawo police gidannan?"
suka nuna Abba sukace "Alhaji Abdullahi you are under arrest"
yace "ni kuma? me nayi?"
sukace "idan munje can zakaji me kayi"
yazeed yace "idan kunje ina? me yayi muku?"
sukace "zaifi kyau muje can kaji laifinka kada mu fallasaka a gaban iyalanka kai kasan me kayi ko kuma me kakeyi"
cikin rashin fahimta yace "ban gane nasan me nayi ba ku faɗa mana a gaban kowa in dai da gaske kuke"
yace "to shikenan tunda kace haka"
waya ya ɗauko ya kunna video, macece sanye da hijabi tana zaune a gaban hukuma tana kuka aka sa mata mic tana magana tace "Alhaji Abdullahi shine wanda ya kaimu gidan marayunshi tunda mahifinmu ya mutu, bamu san me manufanshi ba, ashe ya buɗe gidan marayu ne sabida wata manufa nashi, yana kwashe ƴammata idan sun girma ko kuma ya samesu a girmansu saiya rinƙa kaiwa masu kuɗi suna amfani damu suna bashi kuɗi, saiya bamu kaso kaɗan daga kuɗin, har kasashen waje yana kai mata domin ayi zina dasu a basu kuɗi, abin taƙaici harda ƙananan yara, ni kaina bansan sau nawa nayi ciki na haife ba, amma saiya ɗauke jariran ya siyarwa masu tsafi da yara suna biyanshi maƙudan kuɗaɗe, har yara maza bai bari ba, wannan yaron ɗana ne"
aka nuna wani karamin yaro yana zaune a gefe fuskanshi abin tausayi tace "wa ƴan luwaɗi yake kai yaron, shi kanshi yana luwaɗi da yara ƙanana maza, har saida ya lalatawa yaron bayanshi yanzu haka baya iya rike kashi, a haka yaron a tsorace yake baya yadda ya shiga cikin mutane, ko hotonshi ya gani zai firgita ya fara ihu"
nunawa yaron hoton Abba akayi ya fara yin baya yana ihu yana rufe ido, matar tace "kun gani ba, ya azabtar da yaron, sannan duk wanda kuka tambaya a cikin gidan marayun saide su ɓoye sabida tsoro amma kowa yasan me akeyi acan"
jiri ne yake shirin yar da Abba yazeed ya rikeshi da sauri yace "Abba"
police yace "wannan shine evidence sannan ga wasu ma idan baku yadda ba"
video ya kara kunnawa na wata yarinya wacce take zama a gidan marayun Abba
tana kuka tace "tabbas abinda ƴar uwata ta fara gaskiya ne, duk abinda aka faɗa yana faruwa, ni kaina bansan sau nawa yayi lalata dani ba"
Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
duk wajen jikinsu ya fara rawa harda baba da yake maimaita kalman Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, ankwa suka sawa Abba, yana jin kamar zai faɗi kasa tsaban jiri, man yace "waye yayi mishi wannan sharrin?"
tsayawa sukayi ya kalleshi yace "ba sharri bane domin daga wannan gidan aka fara bamu tabbaci kuma wacce ta fara kawo wannan maganan tayi zaman gidan marayun"
tafiya zasuyi yazeed yace "wacece ita a cikin nan? wacece ta yiwa Abba wannan mummunan sharrin?"
yace "ba sharri bane domin gaskiya ta faɗa kuma itace ta kawo matar har kofan station sannan tace zata iya tsayawa akan maganan sabida ita ɗin babban barrister ce"
kirjin man ya fara duka da karfi ya kalli ammi da jikinta yake mugun rawa yasan daga ita sai ameesha sune barrister a wannan gidan, yace "am...ammi...kece?"
girgiza kai tayi tace "wallahi bani bace"
yace "bata nan yanzu muka rabu da ita taje station ɗin munyi zaton ma ta rigamu zuwa amma bamu ganta ba"
ameesha ce ta shigo da sallama ganin motan ƴan sanda a kofar gidansu, duk suka zuba mata ido, a tsorace tace "meya faru?"
kallon ta yayi yace "yawwa itace wannan"
tace "nice wa? me nayi? me Abba yayi muku kuka kamashi?"
murmushi yayi yace "kai mata akwai pretending kalli yadda take nuna bata ma sanmu ba, kamar yadda kika bamu shaida shine mukazo mu kamashi kuma karki manta kinyi alkwarin tsayawa akan wannan case ɗin"
ta nuna kanta tace "ni kuma? wani case?"
da mamaki yace "kamar yaya? ya kike nuna kamar baki san komai bane?"
tace "ni ai ban taɓa ganinku ba yau ne na fara ganinku"
yace "gaskiya ne da akace kada ka yadda da mace yanzu kece zakice baki taɓa ganinmu ba? to idan baki taɓa ganinmu ba wannan ID card naki da kika bari a hotel ɗin da muka haɗu kika bamu bayani aina na sameshi?"
ido ta zubawa ID card nata, tabbas itace, hanu tasa zata kwace ya nuna musu yace "kunga itace wallahi yanzu tanaso ta musa badan wannan id card ɗin ba zatace bata sanni ba"
hanun Abba suka rike sukace "muje"
da gudu taje tana jansu tace "ku sakeshi me yayi muku? me kuke nufi?"
yazeed yazo yasa hanu ya damke hanunta, fita sukayi da Abba, yazeed ya wanketa da maruka masu zafi yace "dama ke munafuka ce?"
ta dafa kunci da hanu biyu tana kallonshi a mugun firgice tace "wai me suke nufi ne? Nifa ban gane komai ba"
man yace "ya isa haka ameesha idan baki faɗi komai ba aina suka samu id card naki? sannan waye ya faɗa musu ke lawyer ce? kuma ina kikaje?"
tace "man kenan kaima ka yadda?"
yace "koda ban yadda ba ke abin zargi ne ameesha ya kamata ki yiwa kowa bayani yadda zamu gane ina kikaje yanzu?"
tace "kotu naje"
waya ya ciro yace "dawa kuke tare a kotu?"
tace "da sauran mutanen da kasan muna zama mana man"
waya ya kira yasa a speaker yace "barka sunana man"
gaisawa sukayi yace "ameesha Ibrahim tazo kotu ne yau? ina nufin yanzu bada jimawa ba ta kirani tace tana kotu zanzo na ɗauketa amma driver nakeso na tura"
sukace "batazo ba rabonta da zuwa kotu ai tafi sati tunda aka fara shirye shiryen bikinta"
yana kallon cikin idonta yace musu "na gode"
da karfi tace "amma ba yanzu ba taso daga kotu ba?"
katse wayan yayi yana aika mata mugun kallo yace "ina kikaje?"
kallon ammi tayi tace "ammi wai meke faruwa ne?"
ammi tace "ameesha ki bamu amsa ina kikaje?"
baba kam ya fita yabi bayansu Abba, tace "kema ammi kin yadda kenan?"
tace "hanan....."
hanan dake kuka tace "stay away from me dan Allah Ameesha"
ta kalli fahad tace "kaima ka yadda?"
yace "ko ban yadda ba ki bada amsa ina kikaje sannan ya akayi id card naki yaje wajensu?"
man ya kalli mutanen dake wajen yace "kowa yaje an fasa aure"
a kiɗime ameesha tace "what?"
duk suka fara tafiya sum sum, tana tsaye a wajen hanunta har yanzu a kunci tana bin kowa da kallo cikin mugun shock, momy da take tafiya kawai taji zata zube kasa, da gudu ameesha taje ta riketa, fizgewa tayi daga jikinta tace "karki sake ki taɓani"
cikin gigita take kallon momy, Amal ce ta rike momy a hankali ta tafi da ita ɗaki, yazeed da man duk suka har gidan domin bin bayan Abba, fahad ma ya fita a ɗakin ya bisu, Ammi ta tafi itama, ya rage daga ita sai imran, ko magana ta kasa sai kallo take bin ko ina dashi, Imran ne yazo ya riketa yace "zauna"
bakinta yana ɓari tace "ka..ka..ka..."
maganan yaki fitowa, yace "ki nutsu"
tace "kana gani?"
yace "ina gani Anty meesha karki damu nasan sharri ne"
idonta a bushe tsaban tashin hankali tace "to aina suka samu id card ɗina? waya basu? ni yaushe nace Abba yana safaran mata? yaushe nace yana gay?"
ganin bata hayyacinta ma take maganan a zare, hugging nata yayi yace "calm down, Anty meesha relax"
tace "im...im...ran man yace an fasa auren, kalli fa nayi kitso nayi lalle kalli fa har gyaran jiki....kullum...anamin sabida shi...kalli fa har magani inasha ammi tana bani....."
rufe mata baki yayi yace "try to cry Anty meesha kiyi kuka dan Allah ko zaki dawo hayyacinki"
kankameshi tayi tace "Imran na kasa kuka, zuciyata zata fashe na kasa kuka Imran"
yana ɗan bubbuga bayanta yace "relax"
momy akan gado Amal ta kwantar da ita, ta ɗauko mata ruwan sanyi ta kawo mata, cikin sanyin murya tace "kisha"
girgiza kai tayi tana hawaye tace "ba zan iya ba"
kuka ta fashe dashi sosai tace "meyasa zata mishi wannan sharrin? mutum me hankali ta ɓata mishi suna, bakisan yadda ya soni bane amal ya soni sosai shine ya tsamoni daga datti ya kawoni nan gidan amma daga karshe shine zata saka mishi da wannan sharrin, me yayi mata? me yayi mata? shine fa ya ɗaukoni cikin hauka ya maidani me kime me daraja a idon mutane, bai rabu dani ba duk da yasan nice na haifi ƴar mahaukaciya"
tashi tayi daga kwancen ta share hawayen ta karɓi ruwan cikin sanyin murya tace "to amma ya zanyi? ya zama dole nasha ruwan tunda burina ɗaya ya cika"
shan ruwan tayi sai kuma ta fashe da kuka tace "shine masoyina bazan iya rayuwa babu"
nunata tayi tace "ke ba"
dariya ta kwashe dashi itama Amal ta kwashe da dariya, momy tace "ta ina uwa zata iya rayuwa babu ƴarta?"
tashi tayi ta goya hanu a baya tace "kamar yadda ƴa ba zata iya rayuwa babu uwarta ba"
murmushi tayi sannan ta maida fuskanta na asali ta nuna kanta tace "nice manal ƴar mahaukaciya kamar yadda sukace, abinda basu sani ba shine mahaukaci baya taɓa yadda ka taɓa mishi ƴa ko ɗanshi"
momy tashi itama tayi ta dafa manal tace "tun ranan dana ganki a kotu nace musu ba zan zauna ba kaina yana ciwo tun daga ranan nasan ke ɗin ƴata ce, a ranan da suke kaiki prison kuwa saida naje na tabbatar da cewar ke ɗin ƴata ce sannan nayi miki alkawarin zan cireki a prison bazan bari ayi miki hukunci ba kota wuya kota daɗi.....
Jiddah Ce....
managarciya