DUHU DA HASKE: Fita Ta 34

DUHU DA HASKE: Fita Ta 34

DUHU DA HASKE


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 34*


                 ~Sun gama shirya komai kafin suka bar ɗakin, kowa ya koma ɗakinshi kamar babu komai
"Amal karki damu da komai dake faruwa a gidannan tsoronki da suke ji ba wai komai bane labarin manal dana baki shiyasa suke jin tsoronki sabida kina kama dani sosai ni kuma ina kama da manal sosai, ki kwantar da hankali zasu gane ba ke bace a hankali"
tace "to Anty amma naga duk suna janye jiki dani, gara ma me suna ameesha ɗin wannan kyakkyawar sosai tana sona amma wancan hanan ɗin bata sona ko kaɗan"
cikin harshen larabci suke magana, tace "karki damu ita hanan tun tana karama ta tsani manal sabida ta bata wahala a school lokacin da suke yara kuma ta kona mata teddy shiyasa take miki kallon tsana, amma idan sun gane ba ke bace zaki gane kyawawan halinsu"
tace "to Anty"
hira suka fara sosai tana bata labarin zamanta da tayi babu kowa mata irin wahalan da tasha.

yamma likis itace ta fito cikin dogon riga irin na mutanen makka me kauri fari, ta kame gashinta irin yadda larabawa suke yi sannan tasa karamin ɗankwali mara nauyi, momy tace "ki bar girkinnan fa sabida basu saba cin irin abincin nan ba"
make kafaɗa tayi tace a barta tayi girki sabida ta saba, momy tace to taje tayi, kitchen ɗin ta shiga akwai komai enough ta fara shirya girkin zata fara, yazeed ne ya shigo yana sanye da jallabiya ya tsaya a bayanta yana murmushi, jikinta ya bata ana kallonta cikin nutsuwanta ta juyo dan ganin ko waye, murmushi yayi mata da suka haɗa ido sannan ya karaso ciki, sunkuyar da kai tayi tana mishi sannu da zuwa, murmushi yayi ya mika mata hanu alaman su gaisa, kallanshi tayi sosai sannan ta kalli hanunshi taga yayi mata alaman su zama friends, smiling tayi me kyau sannan tasa hanunta a nashi suka gaisa, zamewa yayi bayan sun gaisa ya fara tayata aikin da takeyi na girki, bini bini tana juyawa ta kalleshi tayi dariya kaɗan sai taci gaba, binta yake da kallo yadda take girki cikin kwarewa yasan manal bata iya ba, har ta gama girkin ta jera a dinning sannan ta koma ɗakin momy ta zauna, sai can taji muryansu da alama sun taru a wajen cin abinci, tana son mutane shiyasa ta tashi da sauri ta fita, ganin duk sun taru ta fara murmushi ta karasa, kujeran dake kusa da yazeed ta zauna kanta a kasa, yazeed ya kalleta duk suka kalleta abincin suka fara sawa ammi tace "masha Allah waye yayi wannan girkin?"
yazeed ya nuna Amal yace "wannan ce"
murmushi ammi tayi mata sannan ta mata alaman girki yayi daɗi, smiling da yasa gefen kumatunta lotsawa tayi sannan tayi alaman taji daɗi, man ya kalli Imran dake cin abinci ya kashe mishi ido, a hankali Imran ya gyaɗa kai, juice yellow sosai ya cika cup dashi sannan ya tashi yace "bari na ɗauko remote na game na gyara"
tuntuɓe yayi nan take juice ɗin duka ya zube akan Amal kayan jikinta fari sal ya koma yellow fuskanta ya ɓaci, waro ido Imran yayi a tsorace yace "kiyi hakuri"
ganin ya haɗa hanu alaman roko ta gane hakuri yake bata, cikin sakin fuska da rashin damuwa da abin ta ware hanunshiwta girgiza mishi kai alaman ya daina rokonta, tashi tayi zata je ta canja kayan Imran yaɗan sa mata kafa, sulɓin juice ɗin ya jata kasa ta zube, kara tayi tana ciza karamin leɓenta, da sauri ya durkusa ya mika mata hanu ta rikeshi ya ɗagata da kyar yana mata alaman sannu, gyaɗa kai kawai tayi tayi magana da larabci "zanje na canja kaya"
momy ce ta fassara musu, Imran ya saketa tana ɗingishi kaɗan kaɗan taje ɗaki, Imran ya goge wajen, babu jimawa ta fito tana ɗingishi kaɗan ta zauna kusa da yazeed alama yayi mata sannu, yace "momy ya kamata a samo mata wanda zai rinka koya mata hausa da turanci sabida ta rinƙa fahimtan me ake cewa"
momy tace "to shikenan zan nema mata"
yace "zan nema mata karki damu daga gobe za'a fara koya mata"
momy tayi murmushi tace "na gode sosai yazeed"
ta kalli Amal ta faɗa mata abinda yace, haɗa hannu tayi alaman ta gode, ya jijjiga kai kawai.

washe gari wata mata ce ta ɗan manyanta tazo gidan da takaddan larabci haɗe da turanci da kuma Hausa itace wacce yazeed ya nemo domin ta fara koyawa amal hausa da turanci, ɗaki ɗaya aka basu inda zasu rinƙa karatun harma da black boat ta fara koya mata daga kalmomi har zuwa yadda zata haɗa kalma, duk da bata gane komai amma taji daɗi tunda sun nuna damuwansu akanta.

duk wani aikin gidan itace take yi kafin su tashi daga bacci, momy tace ta bari akwai masu aiki tace a,a ta riga ta saba da wannan wahalan idan ma batayi ba bata jin daɗin jikinta, zuwa yanzu ta fara sabawa dasu sosai, musamman yazeed idan ya dawo daga aiki yana kara koya mata hausa da turanci kuma Alhmdllh yanzu ta fara ganewa, bikin man da ameesha saura kwana goma yanzu shirye shirye akeyi sosai hanan da ameesha basu fiye zama a gida ba, ammi duk wani motsin amal akan idonta saide zuwa yanzu duk sun tabbatar wannan ba manal bace Amal ce.
man kwance yake akan gado yasa laptop akan cikinshi bayanshi da pillow yana aiki, yazeed yace "wannan fa na gama yadda ba itace manal ba dan wannan akwai tsoro sosai"
man yace "nima na jima da yadda tunda naga yatsunta amma kasan mata ameesha idan na faɗi haka to na shiga uku"
wayarshi aka kira ya duba sunan kafin ya ɗauka yace "hello mr chang"
magana suka fara sosai daga karshe yace "zaku samu insha Allah daga yau zamu fara aiki"
katse wayan yayi yace "kasan mr chang babban ɗan zane ne na duniya, a baya munyi aiki tare yanzu ma yace yanaso ayi mishi zane amma wannan karon fa dayawa yake so ya kamata mu kira su faruk daga kaduna su bar wancan branch ɗin su dawo nan muci gaba da aiki tare kawai gobe su zo"
tashi yayi yace "ɗauko mana plain shit da sauran kayan zane yau zamu fara"
yazeed yace "okay dama jikina a mace babu abinda zanyi muje muyi a falo"
ɗauko musu abin zane yayi suka fita zuwa falo, Amal ce zaune tana kallon tv ta zubawa tv ido kamar wacce bata taɓa gani ba, zama sukayi man ya fara zanen yayi kyau sosai cikin singlet da gajeren wando ya bar gashinshi a hargitse hakan ya karasa yayi kyau, lips nashi na kasa ya cusa cikin baki yana tsota yana zanen, yazeed ya kalli Amal yace "kin iya zane?"
girgiza kai tayi cikin hausanta da take koya tace "ban iya ba"
dariya yayi jin yadda tayi maganan, yace "to zoki koya"
tashi tayi cikin nutsuwa tazo ta zauna kusa dashi tana kallon yadda yake zane, kallon na man tayi yadda ya maida hankali duka yana zane cikin kwarewa, a hankali tace "wannan yayi sosai"
murmushi yazeed yayi yace "wannan ai babu me iya bigeshi a zane"

Ameesha ce ta fito tana hamma da alama daga bacci ta tashi sai tafiya take domin ɗauko ruwa, kallonsu tayi taje ta ɗau ruwa tace "sannunku da aiki"
zata wuce ciki man yace "Baby zo"
a hankali tazo tace "gani"
gabanshi ya nuna mata yace "zauna"
kallonshi tayi taga baya kallonta zanenshi yake kallo tace "to bara naje..."
hanunta ya janyo ya zaunar da ita a gabanshi ya fara zanen da ita gab dashi tana jin mumfashinshi yana sauka a wuyanta, kallon zanen take sai kuma ta kalleshi yadda gashinshi ya hargitse bai damu ba da alama ana buƙatan zanen da wuri, hanu tasa tana gyara mishi gashin tace "meyasa baka taje kai a kwanakinnan?"
yace "kece baki kulawa dani"
tace "um um kai dai baka damuwa"
yana zanen yace "aure saura kwana goma amarya bata zuwa wajen ango ba dole ya zama a firgice ba"
dariya tayi sosai tace "yau ka zama busy meya faru?"
yace "mr chang ya kirani yana buƙatan zane dayawa yanzu ma haka so nake na gama wannan saina kira faruk daga kaduna zasu dawo nan garin da zama tare zamu fara aiki wannan zai zama musu sample ɗin da zasu zana"
tace "Ayya zasu ji daɗi kam"
yace "eh mana"
tayi shiru tana kallon Amal wacce ta maida hankali akan zanen yazeed tana kallo, man ganin basa kallonsu ya juyo da fuskan ameesha dake kallon zanenshi a bakinta taji yayi mata kiss, da sauri ta bigeshi kaɗan tace "nifa banson"
Amal kallonsu tayi cikin jin kunya ta sunkuyar da kai dan basu san ta gansu ba, kiran wayan faruk yayi yace "gobe zaku dawo abuja da zama anan zaku fara aiki naji anyi canceling na m.u.m company ku zo nan gobe da safe zan tura ma kowa address na gidan dana kama muku sannan da address na wajen aiki"
jin suna mishi godiya yace "ba komai karka damu ka faɗawa kowa da kasan munyi aiki dasu a baya"
katse wayan yayi ya kalli ameesha data fara gyangyaɗi da alama baccin bai isheta ba, yace "Baby bacci kuma?"
a hankali tace "A,a"
yace "gashi naga kinayi"
mikar da kafanshi yayi yace "kwanta"
babu musu ta kwanta ta rungume kafanshi babu jimawa bacci ya ɗauketa, bini bini yana kallonta, ji yake kamar ya maidata cikin jikinshi ko zaiji sauƙin abinda yake ji a kanta, Allah yasa mishi wani mugun son ameesha wanda ko kaɗan baison yaji son ya ragu, kullum ma sai karuwa yake, shafa fuskanta yayi me kama dana yara yace "my naughty baby"
sai can dare har sun fara gyangyaɗi yace "kai yazeed mu bari fa sai gobe bacci wallahi kuma zamu fita office da wuri"

yazeed yace "kamar ka sani wallahi har bana gane me nake zanawa"
kallon Amal yayi wacce har yanzu babu alaman bacci a idonta yace "baki baccin wuri ne?"
girgiza kai tayi tace "A,a"
man ya kalli ameesha dake bacci ya ɗan bubbugata kaɗan yace "baby? baby?"
cikin bacci ta kara rikeshi sosai tace "uhmm nika barni bacci nake ji"
cikin shagwaɓa tayi maganan, man ya zuba mata ido yana jin yanayinshi yana canjawa, yazeed ganin haka yace "kaga ɗauketa ka kaita ɗaki dan nasan halinka yanzu zaka fara lalubeta tana bacci"
tsaki yaja yace "tunda nine shugaban ƴan iska"
yace "na nawa kuma? kaida ka bita har kitchen..."
Amal sunkura da kai tayi cikin jin kunyan maganansu ta tashi, a hankali ameesha ta buɗe ido tana jin fitsari sosai, akan man ta sauke idanunta da suke cike da bacci tace "ina jin fitsari"
yace "tashi kije ɗaki kiyi daga nan saiki kwanta dare yayi"
tashi tayi kamar zata Amal ce ta riketa tace "easy"
murmushi tayi mata sannan ta kalli man, a hankali ya matso da bakinshi kusa da kunnenta yace "kiyi mafarkina"
kiss me kara yayi mata a gefen kumatu sannan ya ɗauki zanenshi da sauran abinda yazeed ya bar mishi ya wuce ɗaki, Amal tana rike da hanunta suka tafi ɗaki, saida taje tayi fitsari sannan tazo ta haye gado tana kallon hanan da take sheƙa bacci, a gefenta ta kwanta ta rungumeta sannan ta fara bacci, amal ma ta kwanta akan gadon kusa dasu itama ta rufe ido ta fara bacci.

washe gari su faruk sun taho Abuja kowa ya sauka a gidanshi da man ya basu, duk sun haɗu a wajen aiki ya gabatar musu da yazeed matsayin ɗan uwanshi na jini sannan ya faɗa musu matsayinshi a wajenshi, murmushi yazeed yake yi yanajin daɗi a duk lokacin da man ya kiranshi da ɗan uwa na jini har cikin ranshi yana son hakan, kowa an bashi kujeranshi da sunanshi akai kamar yadda sukayi  a kaduna, wajen ya tsaru sosai komai na buƙata an samu, man yana zaune a office nashi ya kifa kanshi akan desk ɗin da yake zane yana bacci, shigowa yazeed yayi yace "bro akwai sauran kala da ake buƙata"
ganin yana bacci yanzu ga zufa da yake yi ya taɓa wuyanshi yaji zafi sosai, da sauri yace "bro man meke damunka?"
a hankali ya buɗe ido yace "cikina yazeed ciwo sosai"
yazeed ya zuba mishi ido yace "dama kana ciwon ciki ne?"
girgiza kai yayi yace "sai lokacin da kafin nayi aure"
shiru yayi yana kallonshi sai kuma yace "sorry tashi muje gida hanan ta dubaka"
cikin wahala yace "A'a bazan iya tafiya ba"
yazeed yace "subhanallah sannu ka daure muje gida tashi zan rike ka"
tashi yayi yana ciza baki yazeed yana rike dashi ta gefe ɗaya suka fito, su faruk ganin baida lafiya suka fara mishi sannu, a mota yazeed ya sashi sannan yaja motan suka tafi gida, a gida ma saida ya rikeshi kafin suka karasa ciki, abba dake zaune a falo yana waya yaga sun shigo yace "meya sameshi?"
da kulawa yayi tambayan, yazeed yace "cikinshi ke ciwo"
abba yace "sannu Allah baka lafiya bari na kira hanan"
kiranta yayi yace "mamana dawo gida man baya jin daɗi"
ameesha ta shigo da uniform a hannu tace "sannu da gida Abba"
yace "yawwa ameesha ya aikin? kede ance ki bari zuwa bayan aure amma kinason wannan aikin naki"
dariya tayi a hankali, yace "man sun dawo baida lafiya yanzu na kira ƴar uwarki tazo ta dubashi"
da sauri tace "meya sameshi?"
Abba yace "suna ɗaki jeki ki dubashi shida yazeed ne"
tashi tayi da sauri taje ɗakin ya kwanta akan gadon yayi rub da ciki sai juya kai yake cikin azaba, da sauri ta karaso tace "meya sameshi ya yazeed?"
yace "ciwon ciki"
zama tayi ta janyo kanshi ta ɗaura a kafarta tace "sorry man"
ciza baki yake yana hawaye, sai sannu suke mishi har hanan tazo, da sauri tace "ku yafeni na jima banzo ba"
fara dubashi tayi saida ta gwadashi da kyau sannan ta kalli ameesha wacce ta zama kalan tausayi fita zatayi ameesha tace "me yake damunshi?"
kallon yazeed tayi sai kuma tayi shiru, yazeed ya ɓata rai yace "ba tambayanki ake ba kin tsaya kina rarraba ido?"
tace "am..wannan"
ya gane batason faɗa ne tana jin kunya yace "jeki ɗauko abinda zaki ɗauko"
fita tayi da sauri, babu jimawa ta dawo da allura, yi mishi tayi sannan tace "shikenan zai samu sauki idan yayi bacci, ameesha tashi muje"
tace "bazan iya tafiya ba hanan gara ina kusa dashi"
tace "no tashi mana yana bukatan hutu"
zatayi magana taja hanunta suka fita, kallonshi yazeed yayi cikin tausayinshi danshj yafi kowa sanin irin wannan bala'in ciwon cikin, ameesha tace "kenan zaiyi bacci?"
hanan dake wurgar da siringe a cikin dustbeen tace "ke baki gane abu ne it's normal irin wannan ciwon cikin musamman ma daya jima babu mace kuma ya riga ya saba da mace"
Amal tace "dama ya taɓa aure ne?"
duk suka kalli juna basu san tana jinsu ba, tace "ya taɓa aure?"
shiru sukayi babu wanda ya amsa mata, duk da hausanta baya fita amma tsaf suke gane me take cewa, ganin basu amsa mata ba yasa taja bakinta tayi shiru.



Jiddah Ce....