DUHU DA HASKE: Fita Ta 31
DUHU DA HASKE
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 31*
~Ganin zafin bai daina ba ta rikeshi gam tana cewa "zafii"
ido man ya zuba mata, yayi mugun missing na ameesha a rayuwarshi, kallon kyakkyawan fuskanta yake, ta rikeshi tace "zafi fa"
a hankali ya buɗe idonta ya matso da bakinshi kusa da idonta ya fara hura mata iskan bakinshi, ji tayi ya fara sanyi saida yaga ta ɗan sakeshi kafin yaci gaba da hura mata da haka har taji babu zafin ko kaɗan sakinshi tayi tace "sai yanzu na fara gani"
murmushi yayi, ta ɗau cokali tana ɗana miyan tace "wai meyasa ka zama wani shiru shiru naga sai de kayi smiling kawai baka magana sosai"
shiru yayi kanshi a kasa, gani tayi yana wani kunya kunya ma yanzu kamar ba man ba, dariya kawai tayi tace "to shikenan tunda kunya na na kake ji yanzu"
yana tsaye tana girki baiyi magana ba harta gama ya fara kwashewa yana kaiwa dining, har suka jejjera kafin tace "zanje nayi wanka"
a hankali yace "to"
tafiya tayi tana mamakin halinshi na yanzu, koda tayi wanka saida kowa yayi sallan Isha kafin suka fito domin cin abinci, a dinning area suke, Imran dama idan ya samu waje ci yake ba kaɗan ba, nan take ya fara zuzzuba komai da aka dafa akan plate nashi, ameesha ce ta kalleshi yace "to na rage ne?"
tace "nayi magana ne?"
zama yayi duk suka fara cin abincin, saida suka gama Abba yace "gobe zaku fara fita aiki, hanan ga makullin hospital naki"
da gudu ta tashi ta rungume Abba tana ihun murna, ameesha tace "congratulations"
yazeed ma yace "congrats baby girl"
rungumeshi tayi tace "yaya ka tayani yiwa Abba godiya"
makulli ya mikawa ameesha yace "ga sabuwar motarki"
itama rungumeshi tayi tace "thank you Abba"
yace "man da yazeed company ɗin fashion designing gobe zaku fara zuwa, Imran ka samu admission a Oxford university dake nan zaka karanci engineering, sannan kai fahad zaka fara zuwa school gobe ina fatan duk kun fahimta?"
cikin jin daɗi sukayi mishi godiya, yace "ameesha gidan marayu kulawan zai dawo ƙarƙashinki nan da wani lokaci kaɗan"
tace "to Abba"
washe gari saida suka buɗe sabon asibitin hanan kafin suka buɗe babban company, ammi tace ta barwa su faruk wanda company suyi amfani da kuɗin a koda yaushe idan suna buƙata, kowa ya fara zuwa aiki cikinsu yanzu babu me samun isasshen lokaci ameesha ma tana kokarin taga tasa momy farin ciki, shi kuma man da yazeed sun zama ƴaƴan ammi koda yaushe suna kusa da ita.
*bayan shekara ɗaya da rabi*
duk suna zaune a falo suna dudduba tulin kayakin dake tsakar falon wanda Abba yasa momy taje har kasar dubai ta siyo lefen ameesha da man, hanan ce akan kayan sai dubawa take tana cewa
"wow wannan yayi kyau"
su Imran dasu fahad suna tayata, ameesha tana gefe tana rike da wani roban ɗan karami tana cin fruits, ammi ce ta shigo tace "ke ameesha zo"
zuwa tayi tace "na'am ammi"
hanunta ta rike suka tafi ɗaki ta ɗauko zuma ta mika mata tace "shanye duka"
karɓa tayi ganin fuskan ammi babu alamun wasa tace "ammi nifa ba wai sha bane banso gaskiya yana sani kasala sosai"
Ammi ta fahimta ba kasala bane dama akwai maganin da dole saiyasa kinji feelings, tace "shanye ki shanye wannan sai ki rinƙa bacci ace aure saura wata ɗaya amma bakida aiki sai yawo da rashin zama waje ɗaya?"
shiru tayi ta shanye ammi tace "daga yau kada na sake jin kinbi hanan kunje yawo"
tace "to"
"muje naga kayan sabida tun safe banje part naku ba sai yanzu"
tashi tayi suka jera suna hira har dukaje part ɗin, ameesha tayi kyau sosai gyaran jiki ammi ta nemo me zuwa har gida ana yimata a haka ma dan tana yawo ne, wannan karon su man sun dawo tana ganinsu tace "ya yazeed"
yace "meesha amarya"
murmushi tayi bata yiwa man magana ba, ya zuba mata ido kamar zai haɗiyeta yadda take wani cikowa shi yafi komai jan hankalinshi gashi taki yadda ko irin su rinƙa keɓewa yana ɗan taɓata ko zai samu sauki, night wears hanan ta buɗe wani ɗan iskan arnen riga ta ɗago, tace "wow yayi kyau"
sunkuyar da kai ameesha zatayi sukayi ido huɗu da man, signal yayi mata da sauri ta ɗauke kai, itafa wannan iskancin ne bataso da sun haɗa ido sai yayi mata signal ko kuma ya kashe mata ido, ko abinci suke ci ya rinƙa taɓa kafanta sam bata sakewa gashi da shegen tsuma idonshi kafin ya kalli mutum, yazeed yace "kai maye ne?"
alama yayi mishi da "me nayi?"
"zaka cinyeta ne?"
tsaki yaja, muryan momy suka jiyo tun daga nesa tana ƙwala musu kira, duk suka daina abinda suke yi suka zubawa kofan ɗakinta ido, fitowa tayi da waya a hannu tazo cikin birkicewa tace "na sameta wallahi na sameta"
da mamaki ameesha tace "wace?"
muryanta yana rawa tace "ku gafarceni na ɓoye muku cewar mamana ta haihu bata mutu ba a lokacin da mace muku ta mutu, nayi hakan ne sabida tsananta da nayi ta wurgar dani a titi, amma yanzu na samo kanwata a social media, dama kullum ina addu'a Allah ya bayyanamin dangina ko guda ɗaya ne, amma tunda tafe min itace na tabbatar itace kuma ita kaɗaice ta ragemin yanzu a duniya, tace mama ta mutu tayi rayuwan wahala a cikin larabawa da kyar ta tsira da ranta yanzu haka tana rayuwa a gidan marayu"
kuka take yi sosai, man ne ya yiwa Ameesha alaman ta lallasheta, a hankali ta tashi taje ta rungumeta tace "ya isa haka momy ki daina kuka, insha Allah zaki samu sauƙi a ranki tunda Allah ya bayyana miki ɗaya a cikin ƴan uwanki"
tana hawaye tace "kina ganin zaku karɓeta idan tazo nan a matsayin ƴar uwa? zaku sota koda kwatankwacin yadda kuke sona ne?"
atare suka ce "haba momy babu wacce zamuki idan tazo daga wajenki, kinyi mana taimaki sosai kin kula damu sannan kina bawa kowa respect"
Abba daya shigo yace "ki tura mata kuɗi tayi passport, sannan ta gama shirye shirye nan da kwana uku ki tura mata kuɗin jirgi ta dawo nan da zama"
cikin kuka tace "na gode muku na gode sosai"
hanan ce tace "ya sunanta? tunda ameesha zatayi aure ta barni nima nayi sabuwar kawa"
tace "sunanta AMAL amma bata jin hausa sai larabci"
hanan tace "zata koyi hausa Indai anan zata zauna har na fara ji kamar ba zata zo ba"
ameesha ta turo baki tace "kenan zaki daina ƙawance dani?"
tace "na isa?"
tashi tayi tace "bari naje kitchen na ɗauko cup, tana tafiya man ya tashi ya bita, tsayawa tayi a cikin kitchen ɗin tayi shiru ta rasa me take tunani, gyaran murya yayi da sauri ta ɗau cup zata tafi, tare hanyan yayi yace "tsaya inaso muyi magana"
tsayawa tayi ta bashi attention, yace "wai meyasa baki bani time ne?"
tace "to ai an kusa aure"
tsaki kaɗan yaja yace "dan an kusa aure shine saiki daina bani time? ko waya fa baki yadda muyi kullum, kuma ni akwai abinda nakeso"
da sauri tace "me?"
ganin yadda ta waro ido saita bashi dariya, ya dake yace "wani abu"
tace "miye shi?"
dama hanan tace mata ta karanta a littafi maza sai an kusa aure zasu fara nuna miki asalin kalansu, kallon da yake mata me kama dana Iskanci yasa tace "nikam ka matsamin na wuce"
murmushi yayi muryanshi can kasa yace "to baki bani abinda nake so ba"
tace "ni banida abinda zan baka ka matsa na wuce"
yayi mamakin yadda ta fahimci ba maganan arziki zai fito daga bakinshi ba, da sauri ta raɓa gefenshi zata wuce ya rike hanunta, hanunta ya harɗe a nashi sannan ya rungumeta ta baya yana shinshinar wuyanta yace "baby"
tace "nika sakeni"
yace "tsaya mana abu kaɗan kawai zanyi"
itafa idan yace abu ɗinnan shine yake tsinka mata rai, light kiss ya mata a wuya sannan ya goga sajenshi a wajen, yace "kin san me nake so ne?"
tureshi ta fara jin yayi maganan cikin kunnenta sannan yayi kasa da murya sosai ta yadda daga shi sai ita zasu ji, idonta ya cika da hawaye ganin man gaba ɗaya ya canja mata ya fara komawa ɗan iska, tace "nikam ka sakeni ko nayi ihu su baba suna falo kuma zasu ji"
kunnenta yasa harshe ya lasa sannan cikin wani irin murya yace "kiyi"
ammi dake zaune tana kallon momy sai taji gabanta yana faɗuwa, ganin babu man da ameesha a falon tun ɗazu suna kitchen daga ɗauko cup, a ranta tace "gara naje yaran yanzu basuda hankali da hakuri"
tashi tayi tace "ina zuwa"
hanyan kitchen zata nufa yazeed yace "am...am...ammi ina zakije?"
tace "kitchen"
tsarguwa yayi dan yasan man dole akwai abinda yakeyi yasa basu fito ba, da ammi ta gani gara shi, yace "me zaki ɗauko dama nima inaso na ɗauko abu"
tace "man zan kira"
tashi yayi yace "bari na kirashi koma ki zauna"
komawa tayi ta zauna, shi kuma ya nufi kitchen ɗin, ameesha tana hawaye tace "dan Allah kar kamin komai dan Allah bafa ayi auren ba zunubi....."
rufe bakinta yayi da nashi, jikin ameesha ya fara wani irin rawa ta fara tureshi, kissing nata yake amma bai taɓa komai na jikinta ba, saide kamar zai cinye bakinta wani irin ajiyan zuciya yake sauke idanunshi suna sauya kala, ameesha tun tana tureshi harta hakura, da wani zaizo kofan kitchen ɗin zata iya rantsewa tun daga nesa kaɗan meshi zai iya jiyo karan kiss ɗin da kuma yadda man yake sauke ajiyan zuciya, kamar wanda ya jima yanason yin hakan da ita sai yau ya samu dama, knocking yazeed yayi, sam man baiji ba, tureshi ta fara jin ana knocking, turo kofan yazeed yayi jin shirun yayi yawa, da sauri ya juya baya yace "sorry"
a hankali man ya saki ameesha yana maida numfashi, ganin haka ta fita da gudu dan ko kara haɗa ido dashi bata so, yazeed ya kalleshi ganin ya juya yana saisaita kanshi yace "amma wallahi man kai mugun ɗan iska ne na bugawa a jarida, har kitchen zaka biyo yarinya mutane suna falo kazo kana tsotseta?"
ɓata rai yayi ya juyo zai fita, lips nashi sunyi jajur, yazeed yace "kasan Allah gara ka tsaya ka gama nutsuwa kafin ka fita, idan ka fita a haka sai kowa ya gane"
dawowa yayi ya tsaya bai yadda sun haɗa ido da yazeed ba dan yasan halinshi dan neman tsokana ne, fita yazeed yaga ammi ta riko hanun Ameesha ta zaunar da ita, duk a birkice take ta kasa nutsuwa ta zauna kusa da ammi, tace "kinga wannan kayan saura naji kin rabar dan nasan halinki da shegen kyauta"
ganin tana sunkuyar da kai da yazeed yazo ta kalleta ta kara kallonta, lips nata ta gani sun ɗan taso kuma sunyi jajur, man ya fito yana sosa kai yaki yadda su haɗa ido da ammi ya ɗau waya yana latsawa, sai yanzu ammi ta gane meke tafiya musamman da taga yazeed yana kunshe dariya, ammi a ranta tace "zanyi maganinku zanga inda zaka sake ganinta ai"
koda suka koma part nasu da ameesha ta hanata fitowa ko abinci saide ta kai mata ko kuma hanan ta kai mata, da dare suna cin abinci ma babu ameesha sai dubawa yake yana kallon hanyan part nasu ko zata fito, ganin bata zo ba har suka gama yayi shiru, yazeed yana kallonshi, har suka koma ɗaki yayi shiru, ya kira wayarta a kashe, damuwa ya shiga, yazeed daya shigo yanzu yace "hi"
shiru yayi mishi yace "ya da damuwa haka? kiss fa kawai ka ɗanɗana idan kuma kayi me gaba ɗaya ranan da baka ganta ba haukacewa zakiyi kenan"
yace "yazeed banson tsokana"
yace "okay bari to na zauna muyi lissafin abinda akayi yau a company"
laptop ya ɗauko musu suka fara lissafi, har dare yayi nisa suna kan lissafi saida suka gama kafin sukayi bacci.
Ameesha a gefen ammi bini bini take shafa lips nata tana tuna abinda ya faru, sai kuma tayi murmushi, kallonta ammi tayi a ranta tace "first kiss"
sai kuma ta watsar kamar bata ganta ba taci gaba da aikinta, haka har sukayi bacci,
kamar da wasa kwana biyu fa baiga Ameesha ba kuma wayanta baya shiga, yau ya gama hakura ganin hanan tana fitowa kamar daga bacci ma ta tashi ya janyo hanunta yace "zo"
tace "ya man meya faru?"
yace "ina ameesha?"
tace "tana ɗakin ammi"
yace "please zaki taimakeni?"
gyaɗa kai tayi, yace "kice mata banda lafiya tazo ta dubani a ɗakina kinji?"
tace "ya man karyan rashin lafiya fa babu kyau"
yace "shikenan idan ba zakiyi ba"
murmushi tayi tace "zanje"
yace "yawwa good girl"
komawa ɗaki yayi ita kuma ta wuce ɗakinsu ammi, tana shiga ta ganta akan gado tana bacci tayi kyau sosai fatarta tana hasken amarci ga kuma kiɓa kaɗan da tayi, wando guntu a jikinta da riga shara shara, gashinta a kame tana bacci cikin nutsuwa, murmushi tayi tace "dole ya man ya ruɗe mana ya kasa nutsuwa idan bai ganki ba"
zama tayi a gefenta tace "ameesha..ameesha tashi mana"
a hankali ta tashi tana murza sexy eye's nata da suke cike da bacci suka zama so attractive, tace "ya man fa baida lafiya"
da sauri ta buɗe idon tace "kai yaushe?"
sauka tayi a gadon zata fita haka, hanan tace "hijabi"
wurga mata hijabin tayi ta cafe sannan tasa ta fita, ɗakinsu taje tana knocking cikin kasa da murya yace "yes"
shiga tayi taga ya yazeed zaune yana dube dube a drower da alama akwai abinda yake nema, hayewa gadon tayi tace "sannu ya jikin ka?"
a hankali yace "da sauki"
hanu tasa a wuyanshi tana taɓawa taji ba zafi tace "ya yazeed yaushe ya fara rashin lafiya?"
yazeed da yanzu suka gama hira da man ya kalleshi zai bada amsa yaga man ɗin yayi kalan tausayi, yace "jiya"
tace "ayya sorry bari naje na kawo maka magani"
hanunta ya rike yace "no hanan tamin allura kawai ki zauna kusa dani"
ganin baida lafiya yasa ta dawo ta zauna tayi shiru batason ganin mutum babu lafiya, yazeed kam cigaba da neman abinshi yayi, ya rasa inda ya aje, yazeed ya kallesu yace "wallahi man banga takaddannan ba na duba sama da kasa amma bari naje wajen Abba may be a samu"
man yace "ok"
fita yayi, man ya cire hijabin jikinta yana kallon kayan, ganin babu bra a jikinta yace "meyasa bakison sa bra?"
tace "taƙura ni yake"
yace "I see, shiyasa kullum haka kike zama"
sauke hijabin zatayi yace "no"
tace "idan kai ka taɓa aure nifa ban taɓa ba, sannan bamuyi aure ba wannan taɓe taɓen all is haram"
langwaɓe murya yayi ya zama abin tausayi yace "to ai banida lafiya ne"
sauke hijabinta tayi tace "shiru kayi bacci"
shiru yayi yana kallonta, ta ɗauke kai tana kallon gefe yace "kalleni mana"
kin kallonshi tayi, yace "i love you so much meesha"
a hankali tace "thanks"
murmushi yayi yanata kallonta, yadda take kawar da kai yaji tana kara shiga ranshi.
momy tana nan tana farin ciki ƴar uwarta amal zata zo gobe, ta kasa ɓoye murnan da take yi, duk sun lura da haka domin har abinci taci sosai yau, Abba yana kallonta yace "gobene ko zata zo?"
da sauri tace "eh ta gama shirya komai gobe zatabi jirgin safe"
yace "masha Allah a ɗakinsu Ameesha zata zauna tunda kince ba zata wuce sa'arsu ba"
tace "to na gode"
Imran cikin wasa yace "nifa idan tazo idan tamin ba sai na karasa karatu ba kawai Abba ka aurar dani"
duk sukayi dariya banda man daya ɓata rai yace "tun yanzu kake zancen aure? zan ɓata maka rai idan ka kara"
murmushi momy tayi tace "ka barshi mana kowa da ra'ayinshi ai, idan tayi maka nida kaina zan aura maka ita"
yace "yawwa momy, kinga idan an gama nasu ya man kamar da wata ɗaya sai ayi nawa"
yazeed yace "naughty boy"
Jiddah Ce...
managarciya