DUHU DA HASKE: Fita Ta 23

DUHU DA HASKE: Fita Ta 23


DUHU DA HASKE: Fita Ta 23


     Na
*Jiddah S mapi*


*Chapter 23*


                 ~Saida yayi wanka yayi bacci sosai kamar ba zai tashi ba, sai yamma likis ya tashi ameesha ta kawo mishi abinci yaci sannan ta bashi paracetamol yasha ya zauna akan sofa yace "yanzu ta ina zamu fara neman Anty?"
Ameesha tace "mu bar wannan maganan sai gobe"
zaiyi magana ta tashi ta fita ta barsu suka fara hira da fahad, yazeed ne ya shigo ɗakin da leda a hanunshi ya zauna kusa dasu, ya buɗe ya ciro su fruits dasu chocolate da snacks harma da ice cream, ya mika musu yace "gashi wa ku na siyo"
karɓa sukayi suna godiya, bai amsa musu ba kawai ya tashi ya fita, imran yace "shi wannan waye shi?"
fahad yace "yayan Anty hanan ne sunanshi yazeed"
yace "Ayya yayi kalan miskilai amma yanada hankali gashi kyakkyawa"
yace "umm"
yana shan ice cream ɗin, saukowa Imran yayi suka sa abin a gabansu suka fara sha, naci kuma suna ci, sunyi kallo a tv Imran yaji shi cikin farin ciki, akan makeken gadon da yake ɗakinsu suka kwanta Ac yana hurasu sun kashe wutan ɗakin suna bacci, ameesha a hankali ta shigo ɗakin ta kunna wutan, kallonsu tayi duk sunyi bacci, a hankali ta hau gadon ta kwanta a tsakiyansu tayi shiru ta ɗaga kai tana kallon saman ɗakin, Imran cikin bacci ya fara mummunan mafarki zufa ya fara yana cewa "A,a manal karki kashe ya Abdool, dan Allah ki barshi dan Allah karki kasheshi na rokeki"
Ameesha dake tsakaninsu da fahad wanda ya buɗe ido ta juyo tana kallonshi, har ya fita a hayyacinshi, ido kawai ta zuba mishi a hankali ya fara buɗe nannauyan idonshi ya kalleta, da sauri ya rungumeta yace "Anty ameesha"
sai kuma ya fashe da kuka, tace "ba zan hanaka kuka ba sabida man yayanka ne ciki ɗaya kuka fito, kasa man a ranka shiyasa kake mafarki dashi Imran, Inaso ka cire man a ranka ka manta dashi a rayuwarka ka fara sabon rayuwa, inada tabbacin ko man ya dawo cikin rayuwarka to zaka gwammace baya cikin rayuwarka kwata kwata, daga karshe ma da kanka zaka fita a rayuwar"
tashi tayi ta zame hanunshi daga jikinta tace "kayi addu'a kafin ka kwanta"
kashe musu wutan ɗakin tayi ta fita kamar ranta a ɓace, shiru yayi ganin ranta yana ɓaci sosai idan akayi maganan man.

wucewa take a fusace fuuu kamar zata tashi sama haka take tafiya domin ta tafi ɗaki ta kwanta, ga baccin da takeji ga gajiya, ɗakin yazeed ta wuce zata wuce nasu taji kamar yana magana, dawowa baya tayi ta tsaya a bakin kofanshi tayi shiru tana jin abinda yake faɗa a wayan,
cikin kasa ƙasa da murya kamar zaiyi kuka yace "baby ina missing naki sosai, gobe kizo nigeria im having blue balls"
dafa kirji ameesha tayi ta rufe ido jin ya kara cewa "baby please I don't know how to masturbate cikina kuma ciwo sosai"
ji tayi yana numfashi kasa ƙasa kamar wanda baida lafiya, cikin nauyin murya da nuna halin da yake ciki da kyar yace "video call? zai kara min ciwon idan na ganki"
sai kuma yace "okay"
video call rohi ta kirashi tana ganinshi tace "sorry baby zanzo nigeria gobe"
yace "okay to me zakimin naji sauki"
waro ido ameesha tayi kamar idonta zasu zubo kasa jin kamar s*x call ya fara"
da sauri ta matsa a bakin kofan tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, me nakeji haka daga bakin yazeed? mahaifinshi mutumin kirki ne, kanwarshi ma haka mutuniyar kirki batada matsala, hasalima bata taɓa jin hanan tana waya da saurayi ba, Abba kuma kullum hankalinshi akan taimakon marayu da marasa karfi, zata iya rantsewa akan halin Abba baya neman mata, meyasa yazeed yake haka? harma kenan zata zo nigeria gobe?"
tafiya tayi zuwa ɗaki da sauri ta shiga ta kwanta ta runtse ido, taya zata taimaki yazeed kamar yadda mahaifinshi da kanwarshi suka taimaketa? a hankali tace "ya zama dole na taimakeshi ya bar wannan harkan duk da baiyi kama da mazinata ba"
da kyar bacci ya ɗauketa da tunani kala kala.
washe gari hanan ta fita aiki Abba baya nan sai momy itama ta fita, ameesha shiru tayi a gidan kamar itama bata nan, saide bini bini tana leka window tana kallon kofan ɗakin yazeed, bataga ya fita ba harma ta cire rai da zai fita ɗin, ta koma zata kwanta taji karan buɗe kofanshi, da sauri ta tashi tana kallo tana jiran taga shine zai fito?
ganin wata kyakkyawar ba'indiyan budurwa yasa ta dafa kirji wato itace rohi? wacce taji suna waya jiya? tana sanye da bakin dogon riga na hijab, shiga ɗakin tayi ameesha saida ta samu waje ta zauna sabida jiri daya kusa kadata.
yazeed dake kwance akan gado ya buɗe mata hannayenshi yace "welcome my rohi"
faɗawa jikinshi tayi ta kankameshi tana sauke ajiyan zuciyan kewanshi da tayi, sun jima a haka shima yana jin irin missing nata da yayi, a hankali ya ɗago kanta yana kallon kyakkyawan fuskanta yace "ya kike?"
kuka ta fashe dashi sabida tana yiwa yazeed wani zazzafan so, bakinta kawai ta haɗa da nashi, shima kissing nata ya fara yana janye rigan jikinta kasa, lumshe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya akai akai, saida ya rabata da kayan ya sauke ajiyan zuciya me nauyi, yana ganin suran jikinta yana jin wani irin shauƙi, komar da ita yayi ƙasa ya danneta a kan gadon trying to samun nutsuwa a jikinta, saide duk iskancin yazeed baya taɓa yadda yayi asalin zina da ita, cikin sanyin murya tace "s*x me baby"
girgiza kai yayi yace "till we get married"
turo kofan akayi ameesha ce ta shigo ta kunna wutan, da sauri rohi ta tureshi tana kare jikinta, kallon ameesha yayi wacce take musu murmushi kyawawan hakoranta suka bayyana, rohi tayi saurin rufa kanta da blanket sabida kada ameesha ta gane mata jiki, yazeed da yake cikin mugun desire yace "fita"
takowa tayi zuwa bakin gadon tana sanye da riga da wando na material yayi kyau sosai a jikinta ta ɗaura headband ta rabe gashinta gida bayi ta zauna kusa dashi tana ganinshi yana kokarin zipping trouser ɗinshi, murmushi tayi ta rike hanunshi dake wajen a hankali ta fara janye mishi zip ɗin, saida ta rufe zip ɗin kafin tace "my husband banji haushin cheating ɗina da kake ba, amma ba komai tunda ni ka aureni"
rohi jin sunan data kirashi dashi na my husband, tayi saurin zame blanket ɗin tace "who is she?"
ameesha tayi mata murmushi tace "his wife"
da sauri ta tashi tana kallon yazeed da mugun mamaki cikin harshen turanci suke maganan harda ameeshan, tace "dama kanada aure?"
girgiza kai ya fara yama kasa magana sai kallonta da ameesha yake, cikin tsawa tace "you are married yazeed?"
da sauri yace "no..am..."
mari ta wankeshi dashi tana kuka tace "cheater"
tana kuka ta ɗau jakanta ta fice daga ɗakin, yace "rohi i can explain, rohi"
rufe kofan tayi gau sannan ta fita a gidan da gudu tana kuka, wani kallo ya yiwa Ameesha wacce ta sunkuyar da kai a hankali zata fita, damko hanunta yayi sannan ya fizgota jikinshi, waro manyan idanunta tayi tana tureshi yace "tunda kin koreta sai kimin abinda yasa na kirata"
wani irin bugawa kirjin ameesha ya fara, idanunta sukayi rau rau yana iya jiyo bugun da zuciyarta ke yi, da kyar tace "da.da..dan Allah ka sakeni"
yatsa ɗaya yasa yana zagaye lips nata yace "um um ba zan sake ki ba matata dole kimin abinda ya kawota"
kuka ta fara kana ganinta kasan a tsorace take har jikinta yana rawa tace "dan girman Allah kayi hakuri wallahi banson ganin kana zina shiyasa nayi hakan dan Allah kada kamin komai ya yazeed"
murmushi yayi ya zauna a bakin gadon hanunshi cikin nata yana janta, saida ya zauna ya janyota ta zauna akan cinyarshi da karfi, dogon karan hancinshi yasa a wuyanta yana shinshinata cikin kasa da murya yace "to ya zanyi da halin da nake ciki wifey? kefa kikace ke matata ce to ai idan zina zanyi da ita ke kuma ai sunna ne ko?"
yayi maganan yana manna bakinshi a wuyanta, kuka takeyi sosai tana kara ruɗewa, hakan yakeso shiyasa yake mata hakan saboda watarana kada ta kara wannan kuskuren na shiga harkanshi.

tace "dan Allah kayi hakuri ba zan kara ba, kayi komai tsakaninka da Allah ne, amma zan fita a haƙƙi zan faɗa maka gaskiya zina haramun ne, Allah yace kada ma mu kusanci zina, duk abinda kuma kayi da ƴar wani koma wace yare ce, koma wace addini ce to sai anyi kaima da ƴarka, ba zanji daɗi ba ace anyi zina da ƴarka sabida abinda kayi"
shiru yayi jikinshi yayi sanyi ya ɗan saketa, ta share hawaye tace "zina babban zunubi ne sannan bashi ne, ranan lahira wutan masu zina yana ajiye duk wanda yayi zina idan bai tuba ba Allah yace saiya konashi a cikin wannan tuwan, amma idan kaga zaka iya jure azaban Allah to shikenan kaci gaba"
tashi tayi zata fita yace "na gode"
murmushi tayi jin abinda ya faɗa, a hankali ta juyo tace "zaka daina kenan?"
gani tayi ya ɗauke kai yana jijjiga kai alaman eh zai daina, cikin jin daɗi tace "yaya yazeed ba zaka kara yin zina ba?"
a hankali yace "ban taɓa zina ba itama iya romance nake tsayawa"
share hawaye tayi tace "Allah ya tsareka yasa kada ka faɗa sharrin zina, Allah ya maka albarka"
jikinshi yayi sanyi saiya tuna da momynsu data rasu kullum idan yayi mata abu taji daɗi sai tace Allah ya maka albarka, hakan yasa da yaji a bakin ameesha sai yaji sanyi a ranshi yaji wani kala, a hankali yana murza yatsanshi kanshi a kasa yace "Ameen"
kallon yanayinshi tayi sannan ta fita tana murmushi kaman anyi mata Albishir da gidan aljanna, kitchen taje ta ɗau vacuum flask ta zuba ruwan zafi a cup sannan ta buɗe fridge ta ɗauko lemon tsami guda ta yayyanka ta zuba a cikin ruwan zafin ta ɗana, runtse ido tayi jin tsami, da sauri tasa sugar kaɗan ta juya sosai kafin ta ɗaura akan karamin plate ta fita dashi, knocking tayi bata jira ya amsa ba ta turo kofan ta shigo, yana kwance rub da ciki yayi shiru, ta zauna a kusa dashi tace "gashi"
a hankali ya kalleta baiyi magana ba ya tashi yana kallonta, cup ɗin ta kai bakinshi tace "sha"
buɗe bakin yayi tasa mishi ya rufe ido dan tsami ya ɗauke kai, tace "please kasha"
juyowa yayi ya fara sha, ganin yana janye bakinshi yana taɓe baki alaman tsami tace "ka shanye duka ya yazeed kaga saura kaɗan"
cikin muryan lallaɓawa take mishi maganan a hankali ya shanye, ta cire cup ɗin tayi mishi irin yadda yara sukeyi tace "ko ko ko ya kare"
gani tayi yayi murmushi kawai ya koma ya kwanta, tashi tayi zata fita yace "maganin me?"
tace "halin da kake ciki"
daga nan ta buɗe kofan ta fita, bai fahimci ne take nufi ba, amma ya fara jin sauki cikin ikon Allah ya fara jin bacci abinda ya jima baiyi ba kenan.

Abdool ya gama shirya musu komai shida manal na tafiya, zaune yake a falon hanunshi rike da luggage yayi kyau cikin kananan kaya yasa p-cap a kanshi orange a kanshi, Atika ce a gabanshi tana durkushe kanta a kasa yace "zamu bar miki amanan Ammi dan Allah ki kula da ita kinga halin da take ciki, abinci magani ki rinƙa bata akan lokaci, bamusan kwana nawa zamuyi ba amma nasan ba zamu kai wata ɗaya ba, komai da komai na danka a hanunki sabida naga kinfi kowa nutsuwa, kuma kin fisu manyanta"
a hankali tace "to Alhaji insha Allah zan kula da ita"
manal dake tsaye tana gyara karamin veil nata a kanta, tayi matukar kyau cikin material baƙi da fari wanda akayi ɗinkin yana jan kasa sosai, takalmi me tsayi kamar koda yaushe a kafarta, kallon Atika tayi tace "sau ɗaya idan wani abu ya samu ammina zan kasheki"
Andool kallonta yayi da sauri tace "ina nufin zan ɓata miki rai"
tashi yayi yaja luggage nashi yace "let's go jirginmu ya kusa tashi"
tana rike da hanunshi suka tafi zuwa wajen zazzafan motar dake fake yana jiransu, shiga sukayi driver ya jasu zuwa airport, manal hanunta sarƙe dana andool suka shiga jirgi suna zaune kusa da juna, shiru duk sukayi babu me magana har jirgin ya tashi zuwa kasar Libya.

Baba megadi yana ganin sun tafi ya ɗaga waya yayi kira, da sauri ta ɗauka tace "baba ina yini"
yace "lafiya ƙalau ƴata ya kike?"
da sauri tace "lafiya baba akwai wani labari ne?"
yace "eh yau Abdool da madam manal sun tafi zuwa kasar Libya domin yi mata aiki"
tace "to baba zanzo anjima insha Allah"
yace "to ƴata Allah ya kaimu"
ta amsa da ameen sannan ta aje wayar, kanta ta haɗa da sofa tace "ya zama dole naje gidan nayi bincike ko dan na san inda mama take, inada tabbacin manal ce ta sace mama kuma insha Allah zan ganta, ba zan faɗawa kowa zanje ba da kaina zan binciko inda mama take kuma nasan Allah yana tare dani"
har dare bata nuna musu zataje ko ina ba, tare dasu momy suke zaune a dinning suna cin abinci, yazeed idan sun haɗa ido da ameesha saiya ɗauke kai yana jin matukar kunya, momy tana kula da hakan saide tayi murmushi kawai taci gaba da cin abinci, Abba yace "alhmdllh nikam na cika cikina fam kuma na tafi saida safenku"
duk sukace "saida safe Abba"
fahad da Imran suna zaune suna kallon ameesha sai kallon agogo take akai akai, ido huɗu sukayi da Imran yayi mata alaman menene?
murmushi tayi mishi ta girgiza kai alaman ba komai, yace "okay"
hanan tace "momy muje ki bani abinda kikace kin siyo mana nida ameesha"
momy cikin innocent voice nata tace "to muje"
ameesha gani tayi kamar momy bata gama cin abincin ba, kuma tanada kawaici ko yanzu ta fara cin abinci Abu ya taso tana iya bari tayi abin bata damuwa, tace "hanan ai momy bataci komai ba"
da sauri momy tace "ba komai na koshi ameesha"
tafiya suka fara da hanan tana rike da hanunta tana mata surutu, sai murmushi da uhm kawai take yi, ameesha ta kalli agogo ganin dare yana yi ta tashi zata fita makullin mota yana aljihun wandonta, muryan yazeed taji yace "ina zakije?"
turus ta tsaya, sai kuma tace "zanje wani waje ne"
yace "na raka ki?"
shiru tayi sai kuma can tace "eh muje"
tashi yayi ya bar abincin yazo wajenta suka jera tare suka fita, jikin Imran yayi sanyi ya tashi zai tafi fahad yace "bakaci abinci sosai ba fa"
yace "na koshi"
tafiya yayi baiji daɗi ba ganin ameesha da wani ba ya abdool ba sai hakan yasa yaji ya kara tsanan ya manal itace ta datse kyakkyawan alaƙan dake tsakanin Abdool da ameesha.

shiga motan tayi shima ya shiga ya zauna, itace take driving cikin kwarewa tanajin faɗuwan gaba, duk lokacin da wani yaje gidansu manal baya fitowa saita naɗa mishi sharrin da sai ya gwammace baizo duniya ba, yau gashi zataje tana tsoron abinda zai biyo baya, amma koba komai uwa tafi komai, yazeed ya kula da yadda jikinta yake rawa yace "kina lafiya?"
a hankali tace "a,a gaskiya ina cikin tashin hankali yazeed"
shiru yayi yana nazarinta da alama bata iya ɓoye farin cikinta ko damuwanta batada ɓoye ɓoye sam, yace "me yake damunki?"
a hankali ta fashe da kuka, yace "stop"
kamar jira take yayi magana ta tsayar da motan ta haɗa kanta da jikin sitiyarin motar ta fara kuka mara sauti, tausayi yaji ta bashi, handkerchief ya mika mata, ta karɓa ta share hawayen ta mika mishi, muryanta daya dashe tace "na gode"
saida ta ɗan samu natsuwa zata fara driving taji ya rike hanunta, shiru tayi tana kallonshi shima yana kallon cikin idonta a hankali yace "nasan bamuyi sabon da zaki faɗamin komai a kanki wanda ya shafi rayuwarki ba, amma naji inason jin labarinki kuma naji Inason na taimaka miki kamar yadda kika taimakamin ban faɗa zina ba"
a hankali ta sunkuyar da kai tace "ban yadda da kowane namiji ba bayan Imran da fahad kannena kenan, bayansu babu namijin dana yadda dashi sabida nasan dole watarana zai nisanceni, zanso ka taimakeni amma zuciyata taki yadda na yadda da kowa sabida taimako dan nasan zatazo ta karye daga baya"
ya girgiza kai yace "nayi alkawarin zan taimaka miki ba zan barki ba"
a hankali ta fashe da kuka ta fara bashi labarin komai tun daga kan yarantarsu har zuwa yau da zataje gidansu abdool da manal domin dubo mahaifiyar ta, ta karashe maganan tana damke hanunshi dake cikin nata tana kuka kamar zata mutu, tinda yake bai taɓa jin yanason ya taimaki wata kamar yadda yaji yanason ya taimaki ameesha ba, yadda take kuka kaɗai zai tabbatar maka tana jin ciwo a zuciyarta, cikin kuka tace "sau uku ina attempting suicide hanan ce ta hanani, itace ta hanani kashe kaina..."
janyota jikinshi yayi yana  ɗan tapping bayanta yace "ya isa ki daina kuka, kinyi kuka sosai ya kamata ki tsaya haka"
tsayawa da kukan tayi tana shesheƙa, yayi shiru yana kallonta kwance a kirjinshi, zame kanta tayi ta share hawayen tana murmushi tace "ya kamata mu tafi dare yana yi"
yace "meesha?"
shiru tayi jin sunan daya kirata dashi, ya kara cewa "meesha"
tace "na'am"
yace "zaki yadda na zama kamar Abdool a wajenki? zaki yadda na goge ciwon daya sa miki a zuciya? nasan childhood friend ba wasa ba amma i will try my best dan ganin mun zama close friend munyi sharing duk wani damuwanmu kin yadda?"
shiru tayi tana kallonshi kamar me neman wani abu a fuskanshi ga idanunta jiƙe da hawaye sai suka kara yin kyau, lips nata yana rawa ta kasa amsa mishi, a hankali ya matse hanunta dake cikin nashi yace "please"
a hankali ta gyaɗa kai hawaye yana zuba tace "na yadda amma dan Allah kada kaci amanata"
yace "insha Allah"
yace "ba zaki ɓoyemin komai ba?"
a hankali ta gyaɗa kai alaman eh.
yatsa ya harɗe ya mika mata kamar yadda ta bashi labarin yadda suke alƙawari dasu Abdool yace "promise"
karamin yatsanta tasa ta sarke nata cikin nashi tace "promise"
murmushi yayi yace "dawo nan ni zanyi driving"
zatayi magana yace "no"
a hankali ta fita shima ya fita suka canja waje, shi yake driving sai satan kallonshi take har yafi hanan kyau fuskanshi kamar mace, sai ya juyo saita ɗauke kai, da haka har suka isa kofar gidansu manal, kallonta yayi bayan yayi parking yaga jikinta yana rawa, yace "ki daure ina jiranki anan"
tace "to"
buɗe motan tayi zata fita yace "Allah bada sa'a"
tace "ameen"
fita tayi yana kallonta tana tafiya da sauri har ta tsaya a dab gate ɗin tayi knocking, baba megadi yace "waye?"
tace "ameesha ce"
buɗe mata yayi yana murmushi yace "sannu da zuwa kin kinzo?"
a hankali tace "eh"
shiga tayi ta durkusa ta gaisheshi ya amsa kafin ta tashi, yace "tun ranan dana ganki a gidannan nasan kinada gaskiya shiyasa na biki domin na baki hakuri, sannan naji duk abinda ya faru tabbas manal zata iya yin fiye da abinda kika faɗa, tun tana karama muguwa ce haka ta girma batasan tausayi ba, idan tanason abu dole saita mallaka idan kuma taga zata rasa tofa saide kowa ya rasa, zan baki wani shawara idan har kinaso ku karashe bada labarinku Abdulrahman yana raye"
a firgice ta kalleshi cikin rashin gane me yake nufi, yace "kwarai matukar manal taga Abdool zai koma rayuwa daku taga cewar zata iya rasashi tofa zata kashe shi"
waro manyan idanunta tayi tace "baba shima yana santa ba zai barta ba"
baba yace "to shikenan Allah ya baki sa'a ki samu shaidu wanda zai tabbatar miki itace ta sace mahaifiyarki"
tace "ameen baba zan shiga ciki"
yana ɗingishi ya koma ya zauna yace "ki rike wayarki kusa dake sabida tsaro duk abinda naga zai faru ba daidai ba zan kiraki"
tace "na gode sosai baba"
yace "kiyi bincike ta yadda ko sun dawo ba zasu gane ba"
tace "to baba"
shiga tayi kasancewar baba ya tura mata duk wani lungu da sakon gidan ta watsapp yasa tasan ko ina na cikin gidan, ɗakinsu da man ta fara shiga tana bincika ko ina da tasan manal zata iya ɓoye shaida, bataga komai ba, tana ta dubawa ko Allah zaisa ta dace bata ga komai ba, a gajiye ta fito ta nufi ɗakin ammi cikin sanɗa ta shiga ta kunna wutan ɗakin a zatonta ammi tayi bacci sai taga idonta biyu tana zaune akan gado ta haɗa kai da gwiwa, zaro ido tayi a tsorace ta kashe wutan ganin bata ganta ba ta buɗe kofan zata fita, da sauri ta kunna wutan ta kara kallon ammi gani tayi kamar bata motsi da sauri taje bakin gadon tana taɓata tace "ammi? ammi? Ammi?"
a hankali ta buɗe ido da alama bacci tayi a zaunen, ganin ameesha sai tayi mata wani murmushi me sanyi da yasa jikin ameesha yayi sanyi sosai, juyawa tayi zata tafi taji ta rike mata hanu, a hankali ta juyo tana kallonta sai taga hawaye masu zafi akan suna wanke fuskan ammin, ji tayi ba zata iya tafiya ta barta a wajen ba, dawowa tayi ta hau gadon ta zauna a gefenta ta share mata hawayen da tafin hanunta tace "kukan me kike? karki damu ƴarki ce tayi nasara nasan ba zan taɓa yin nasara a kanta ba, ta rabani da mama"
hanunta ammi ta rike gani tayi tana nuna mata maganinta da hanu, kallon inda maganin yake tayi tace "magani?"
gyaɗa kai tayi, tace "bakisha bane?"
gyaɗa kai ta kuma yi, ameesha cikin mamaki tace "meyasa bakiyi bacci ba sabida bakisha magani ba?"
alama tayi mata da eh, jikinta ya kara sanyi tace "kinyi wanka?"
girgiza kai tayi, ameesha ta taɓa wuyanta taji zafi sosai, a hankali tace "yaune kawai bakiyi wanka ba?"
girgiza kai tayi alaman no, da mamaki tace "kin kai kwana biyar?"
da sauri tayi mata alama da eh, a hankali ta tashi ta ɗauko mata maganin ta kawo mata, kallon bedroom fridge dake gefen gadon tayi, ta buɗe ta ɗau goran ruwa ta buɗe tasa mata maganin a baki sannan ta bata ruwan, tsintsan kanta tayi da zuwa toilet ta haɗa ruwan zafi tazo ta taimaka mata ta sauketa daga gadon, akan wheelchair ta ɗaurata sannan ta kaita cikin toilet ɗin tayi mata wanka ta fito da ita ta shafa mata mai, buɗe wardrobe tayga tulin tsadaddun kayan da suke ciki amma da alama ba'a amfani dasu yanzu, wani rigan bacci me kyau ta ɗauko mata ta juya zata tafi taga hoto ya faɗo daga cikin rigan, durkusawa tayi ta ɗau hoton tana kallo, taga Ammin ce da Alhaji umar maidawa sunyi kyau sosai a cikin hoton da ganin ammi kasan tana farin ciki akayi hoton, zata mayar da hoton ammi tayi mata alama da kada ta mayar, a hankali tazo ta bata hoton a hannu, gani tayi ta rungume hoton tana kuka sosai, jikinta ya kara sanyi tama manta bincike ne ya kawota gidan, da kyar ta karɓi hoton tasa mata kayan bacci ta kame mata gashinta data wanke wanda har ya fara wari, ta kwantar da ita akan gadon sannan da sauri ta kashe wutan ta fita, "ban samu komai ba yaushe zan samu kenan? nan bada jimawa ba"
tana magana ita kaɗai kuma tana bawa kanta amsa har ta fita ta samu baba megadi tace "ban samu komai ba amma kullum zan rinƙa zuwa, idan sun dawo kawai ka sanar dani a waya"
yace "to shikenan Allah ya bayyana ta"
tace "ameen"
kuɗi ta ciro masu yawa ta bashi, yace "a,a ameesha banyi miki haka dan ki bani kuɗi ba nayi ne dan na taimaka miki"
tace "nima baba banyi dan ka taimakamin ba nayi ne dan Allah"
da kyar ya karɓi kuɗin tayi mishi saida safe sannan ta tafi zuwa kofa inda yazeed yake zaune a mota yana jiranta, buɗe motan tayi ta shiga yana baccinshi hankali kwance da alama ya gaji da jiranta ne, tafa hanu tayi tace "salam"
gani tayi bai motsa ba, bakinta ta kawo daidai kunnenshi da ihu tace "yaya yazeeeeeeeeed"
a firgice ya buɗe ido yana kalle kalle, dariya ta tsuntsire dashi tana sa hanu a baki tana rufewa, tsayawa yayi yana kallonta, dariya yana mata kyau sosai, ganin yana kallonta ta daina dariyan, tada motan yayi yace "kina kyau idan kina dariya"
murmushi tayi, yace "da alama kinyi nasara"
girgiza kai tayi, yace "shine kuma kike dariya?"
tace "a koda yaushe anaso mutum ya zama baya cikin kunci koda kana cikin damuwa ka mikawa Allah kayi dariya wa kowa insha Allah komai zai yi daidai"

ta bashi labarin halin data tsinci ammi, har suka isa gida tana bashi labari, koda suka shiga yayi mata saida safe kafin ya shiga ɗakinshi, itama ɗakinsu ta shiga, hanan tana zaune duk hankalinta ya tashi sai kiran waya take ba'a ɗauka, tana ganin ameesha ta tashi ta rungumeta tace "kin tsoratani ina kika shiga?"
ta zameta tana cire kayan domin sa na bacci tace "mun fita ne"
tace "ke da wa?"
shiru tayi, tace "keda wa?"
tace "nida ya yazeed"
hanan tace "Awww na gane"
daga nan bata kara cewa komai ba ta hau gado tayi kwanciyarta.


_jiddah Ce...