DUHU DA HASKE: Fita Ta 21

*DUHU DA HASKE*
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 21*
~Kwantar da kanshi yayi a gefenta kan gadon hanunshi cikin nata, ta lumshe ido tana bacci shi kuma idonshi biyu yana kallonta, turo kofan akayi Dr yana rike da takadda ya kalli abdool yace "kaine mijinta?"
gyaɗa kai yayi, yace "okay akwai abinda nakeson faɗa maka"
a hankali yace "ka faɗa anan"
cikin sanyin murya Dr yace "ciwon cancer n zuciya yayi chronic a jikinta, akwai wani likitan irin wannan ciwon a kasar libya inada tabbacin idan ka kaita zata warke, zan baka number ɗinshi kuyi magana sannan kuyi fixing date saika kaita can amma dai matukar kuna nan to gaskiya samun saukinta zaiyi wuya"
da sauri Abdool yace "ka bani numbern zan kira"
kana ganinshi zaka san yana bukatan ganin ta samu sauki, dr ya bashi number yace "ka kirashi yanzu idan kunyi magana ka bani muyi magana dashi"
da sauri yace "to"
jikinshi har yana rawa ya kira number ɗin, kusan kira biyar bai ɗaga ba, hankalin Abdool a tashe ya kara kira, ganin bai ɗaga ba yace "baya ɗauka"
dr ya kalli abdool wanda ya daburce ya zama kalan tausayi yace "kara kira"
kira ya kara har ya kusa katsewa aka ɗauka, da sauri yace "Barka da warhaka sunana abdool"
mutum ne babba domin daga jin muryanshi zaka san ba karami bane, yace "how can I help you?"
da sauri yace "matata tanada cancer a zuciya kuma yayi chronic har ansa mata date na mutuwa kuma a wannan shekaran akace zata mutu"
murmushin manta me sauti mutumin yayi sannan yace "babu wanda yasan ranan mutuwan wani ko kuma date na mutuwanshi sai Allah daya haliccemu, zanso kazo da ita nan zamuyi mata aiki kuma da yaddan Allah zata samu sauki, amma kuɗin aiki yana iya kai biliyan ɗaya"
da sauri yace "ba matsala"
mutumin yace "yaushe zaku zo?"
har zece gobe sai kuma ya tuna akwai zaman kotu nan da sati biyu, a hankali yace "nan da sati biyu"
mutumin yace "okay ka turomin full name nata da state da kuma phone number saina cika muku form kafin kuzo"
yace "okay"
mikawa Dr waya yayi, Dr suka gaisa yace shine ya turasu, daga nan ya karɓi wayan ya tura mishi komai, dr yace "Akwai wani da yake bada maganin gargajiya idan ta samu sauki zuwa anjima saika kaita wajenshi tayi amfani da maganin kafin nan da sati biyu"
cikin sanyi yace "na gode Dr"
kwatance yayi mishi na unguwar da mutumin yake yayi godiya da nufin idan an sallamesu saisu wuce can kafin suje gida, saida suka kara kwana sabida ta gama alluranta, da safe ta tashi daga baccin da alluran suka sata ta buɗe ido da sauri ta rufe ganin haske, a hankali tasa hanu tana murza ido kafin ta buɗe ta sauke akan Abdool wanda yake kallonta da murmushi akan fuskanshi, cikin sanyin murya tace "my abdool har yanzu ina hospital? ka kaini gida ina Ammi?"
tashi yayi ya rike hanunta yace "muje brush"
toilet ya kaita yayi mata brush sannan ya fara cire mata kayan jikinta, saida ya cire mata duka sannan ya ɗau sabulun daya siyo ya kunne shower ɗin toilet, wanka ya fara mata, ta baya ya rungumeta hanunshi akan kirjinta yana pressing a hankali, cikin sanyin murya tace "wanka ne haka?"
murmushi yayi yace "haka nakeso"
murmushi me sauti tayi sannan ta bige hanunshi tace "a hospital muke"
turo baki yayi a shagwaɓe yace "to ba kin samu sauki ba?"
ganin yana cire belt da gaske yake, tayi saurin janyo towel ta ɗaura, tureshi tayi tace "banyi sauƙi ba"
cikin shagwaɓanshi daya saba yimata idan yanason sata farin ciki yace "baby to fa jiya banyi ba"
gwalo ta mishi kafin ta fita, da sauri tasa dogon rigan daya siyo mata black ne me kyau da mayafin, ta rame kaɗan amma tayi kyau, fitowa yayi yana ɓata rai, murmushi tayi ganin ya rike hanunta yace "muje"
kallonshi tayi da suka fara tafiya yaki ya kalleta shi a dole yana fushi da ita, a ranta tace "banda abdool a toilet ɗin hospital wani irin jaraba ne haka?"
tare suka shiga office na dr yana ganinta yace "manal sannu da jiki?"
a hankali tace "yawwa"
payment sukayi zasu fita yace "ki kula da mijinki sosai yana sonki ko bacci baiyi ba haka ya kwana ido biyu ina fatan zakiyi mishi biyayya ki kula dashi ki kula da farin cikinshi kada ki cutar dashi kada ki cutar da na kusa dashi idan kikayi haka Allah ba zai barki ba"
dum dum taji gabanta yana faɗuwa, ta kasa ta juyo tana kallonshi ta yadda Abdool ba zai gane ba, sannan tace "to"
fita sukayi suka shiga mota Abdool ke driving, ganin sun kama hanyan da ba na gidansu ba tace "my abdool ina zamuje?"
bai mata magana ba yaci gaba da driving, cikin muryan shagwaɓa kamar zatayi kuka tace "please kamin magana mana kasan fa ba zan iya jure ganinka kana fushi dani ba, please kamin magana"
shiru yayi, kyawawan idanunta ta lumshe a hankali tasa hanu akan belt nashi ta fara cirewa, ta tsani ganin Abdool cikin fushi musamman idan wa ita yake yi, saita rasa hankalinta, bai kulata ba, gani yayi tana shirin zama a kanshi, da sauri yace "shikenan na sauko"
a hankali ta koma ta zauna tana murmushi tace "da gaske?"
yace "yes"
mayar mishi da belt nashi tayi sannan tace "fushinka yana sani a wani hali my abdool ina tsoron ranan da zaka rabu dani"
murmushi yayi yana kallonta baiyi magana ba, domin aranshi yasa duk lokacin data samu sauki ta warke to zai fita daga rayuwarta, dama tausayin halinda take ciki yasa yake kula da ita, bayan haka babu wani abinda zaisa ya zauna cikin rayuwarta, tace "my abdool?"
yace "yes baby"
tace "kamin alkawari ba zaka rabu dani ba komai zakaji a kaina"
shiru yayi ganin ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta kawai ya rike hanun yana cigaba da driving, tace "ina zamuje?"
yace "gidan magani"
shiru tayi suna tafiya yace "maganin gargajiya zan karɓa miki inji dr sannan zamu tafi kasar libya bayan sati biyu"
dum taji gabanta ya faɗi da sauri tace "me zamu je yi?"
yace "akwai wani dr acan yana aiki akan cancer ɗin zuciya kuma ina fatan muyi nasara idan munje"
tace "idan na samu sauki zaka rabu dani?"
tambayan yayi mishi nauyi shi kanshi bai san me zece mata ba, kawai ya tsinci kanshi da cewa "meyasa zan rabu dake?"
murmushi ne ya suɓuce akan fatar bakinta da yayi ja, a kofan wani gida suka tsaya shi ya shiga ya karɓi maganin sannan ya fito suka tafi, daidai zasu fita a unguwan motarsu ta tsaya, duk yadda yayi ya tada motan yaƙi ga rana sosai, fitowa yayi yana dubawa rana yana facing nashi yana rurrufe ido domin abdool baison rana ko kaɗan, manal ta cikin madubi take kallanshi ganin rana yana damunshi ta buɗe marfin motan ta fito tana gyara siririn mayafin kanta, wasu ƴammata da suke zuwa islamiya suka ganta tare suka kalli juna, atare suka haɗa baki sukace "balarabiyan mahaukaciya?"
kallonsu tayi cikin rashin gane me suke faɗa tace "waye mahaukaciya?"
nunata ɗayan tayi tace "wallahi kece balarabiyan mahaukaciya baki tsufa ba? tun muna yara muka sanki"
Abdool ma da mamaki ya tsaya yana kallonsu, kafin ya sauke bayan motan yaga manal ta cafko ɗaya daga cikinsu tana mata dukan mutuwa, zuciyanta yana tafasa tana cewa "na muku kama da mahaukaciya?"
sauran suka sa gudu a tsorace sukace"balarabiyan mahaukaciya bata tsufa ba?"
jin sun kara kiranta da sunan ta kwantar da yarinyar a kasa tasa kafa ta take mata wuya, manal tanada mugun karfi, Abdool waro manyan idanunshi yayi a mugun firgice ganin yarinyar tana wurwurga kafa, manal kuma tana tsaye jikinta yana rawa tana huci, idanunta suka koma jajur, karamin bakinta sai rawa yake, da wani zafin nama ya riketa ya fizgota, yace "kinyi hauka ne? idan kika kasheta fa?"
cikin hawaye masu zafi tace "kaima da hauka zaka kwatantani?"
kwace jikinta tayi tana kallon jikinta tace "wai nayi kama da mahaukaciya ne da gaske? haka fa kwanaki suka min wannan ihun, nayi kama da mahaukaciya?"
cire mayafin tayi ta bazo gashinta tace "ina kama da mahaukaciya my Abdool?"
janyota jikinshi yayi yana bubbuga bayanta a hankali yace "shiiii ya isa haka baki kama da mahaukaciya ko kaɗan kawai de kin san yara da yaranta muje motan ya gyaru"
tana kuka ya rike hanunta zuwa cikin motan, yaran ta gani suna wirgin motan da dutse suna kara kiranta da sunan da ko a mafarki bataso taji, zuciyanta ya fara tafasa, Abdool ganin zata buɗe ta fita ya damke hanunta da kyar yaja motan suka bar unguwan, shima cike yake da mamaki ga mutane dayawa suna wucewa yaran basuyi musu ihu ba sai ita? ko dan kyawunta da suka gani me kama dana larabawa da farin fatarta? a hankali ya saci kallonta karaf suka haɗa ido, muryanta yana rawa tace "kaima ka fara yadda ko?"
girgiza kai yayi, buga jikin motan tayi tace "eh mana"
kuka take yi sosai yana lallashinta da kyar suka tafi gida, yana parking a compound ta fito da gudu ta shiga ciki, ammi dake zaune akan wheelchair taga manal ta shigo a guje, zuciyanta yana dukan uku uku ta zubawa bakin kofa a ido, a ranta tace "Allah yasa ba wani abu ta yiwa Abdool ba"
hankalin ammi ya tashi sai kallon kofa take a firgice, Abdool ne ya shigo fuskanshi duk gajiya da damuwa, murmushi tayi mishi me kyau sannan tayi mishi alaman yazo, zuwa yayi ya durkusa a gabanta, janyoshi jikinta tayi ta saki ajiyan zuciya a ranta sai taji kamar ɗanta ne ya dawo, jikinshi yayi sanyi a hankali yace "ammi ya kika kwana?"
zameshi tayi daga jikinta ta ɗago face nashi tana kallonshi tana murmushi a hankali yaga ta mishi kiss a goshi, murnan daya gani a fuskanta ya bashi mamaki kamar irin uwa da take tunanin ɗanta yana cikin wani hali saita ganshi, karan fashewan kwalabe suka jiyo daga sama, waro ido tayi a tsorace, sakinta yayi ya tashi da gudu ya haura stair yaje kofan ɗakin yaga ta kulle, daga waje yana iya jiyo kukanta tana watsi da kayan ɗakin tana cewa "nice mahaukaciya? ni manal zasu kira da sunan mahaukaciya?"
ammi dake zaune akan wheelchair tayi murmushi jin abinda take faɗa, a ranta tace "Alhmdllh Allah yasa Abdool ya gane ba itace ta haifeta ba sannan ya ɗauketa daga gidannan ta samu ta fara bacci cikin kwanciyan hankali"
Abdool yana bubbuga kofan yace "manal open the door"
cikin kuka tace "ba zan buɗe ba, kaima ba ka fara yadda ba?"
cikin tsoron kada ciwonta ya kara tashi yace "Baby ta buɗe kofan kinji? kinga ni zanje da police su kama yaran da iyayensu sabida karsu kara ganinki a hanya su kara kiranki da wannan sunan kinji baby na?"
cikin sanyin murya me cike da lallashi da soyayya yake mata maganan, a hankali ta fara share hawayen tace "ka tabbata?"
yace "eh na tabbata babyn Abdool buɗe kofan kinji? yawwa baby"
jin karan tafiyanta ya sauke ajiyan zuciya, buɗe kofan tayi zata juya ya rungumeta ta baya, ganin yadda ta farfasa kwalaben turaren wuta da kuma yadda tayi watsi da kayan ɗakin yasa fuskanshi a wuyanta yace "shine kika farfasa kwalabe sanida maganan yara?"
a hankali tace "ba kaima ka fara satan kallona ba alaman ka fara zargi"
shafa sajenshi yayi a wuyanta kana yayi mata kiss masu zafi yace "to ai ni kallon soyayya nake miki"
zatayi magana taji yasa hanu akan kirjinta yana matsawa a hankali yace "tunda mun dawo yanzu sai..."
bigeshi tayi ta janye jikinta tace "nika kyaleni bacci nake ji"
yace "um um bazan kyaleki ba"
murmushi take ganin yana biyota, da gudu ta shiga toilet ta rufe, dariya yayi ya zauna a bakin gadon yana jinta tana kara yin wani wanka, tagumi yayi tunani sun cika mishi ƙwaƙwalwa ya rasa ya zaiyi, ya rasa ina zaisa kanshi bayada kwanciyan hankali ko kaɗan, ameesha yake gani cikin idanunshi yadda tayi kyau cikin kayan lawyer, ya akayi ta zama lawyer? waya bata kuɗi? ya akayi skin nata ya kara yin kyau da alama tana cikin kuɗi da kwanciyar hankali, sannan fahad yace mishi ta gudu ta bar gari kenan yau ne ta dawo? domin yaga shock ɗin da Imran da fahad suka shiga a lokacin da suka ganta, ina Anty? waya sace Anty? ina zai fara nemawa ameesha mamanta? hawaye ya share a hankali yace "ina kike anty? waye zai bani amsa? yasan ko sama da kasa zasu haɗe ameesha ba zata taɓa yadda su kara magana ba, koda ta yadda ba lalle su dawo kamar da ba, ba lalle su kara zama besty ba, ba lalle su kara sharing duk wani matsalansu ba, ya mata alƙawari kuka zasuyi a lokaci ɗaya sannan dariya ma haka
rufe ido yayi yana tuna duk wani moment nasu, yana tuna ranan da taje faɗa mishi ya samu aiki, faɗawa tayi kanshi, shafa lips nashi yayi inda tayi kissing nata, a hankali ya lumshe ido yayi missing komai nasu, tafiya a mashin zuwa neman aiki zuwa yawo tare, yawan kiss da take mishi a goshi ko kumatu idan yayi abin birgewa da kuma yawan ɓata rai da nuna damuwa idan yayi abinda ba daidai ba, dariyanta, murmushinta da kullum bata dainawa yaga duk yanzu babu, ta zama wani kala bata fara'a yanzu bata sakin jiki, ta daina tafiya da sauri da action ta daina sa riga da wando yanzu sai uniform.
hawaye masu zafi yaji suna wanke mishi fuska, fitowanta kenan daga toilet taga ya rufe fuska da pillow yana hawaye, jingina tayi da jikin bangon itama taji zuciyanta yana karyewa batason ganin Abdool yana kuka, soyayyan Abdool zai fasa mata zuciya, duk abinda tasan zai shiga tsakaninta dashi zata kawar ta kowane hanya ne, a hankali ta karasa har inda yake, zame pillow tayi daga fuskarshi ta kalleshi, yayi kamar ba kuka yake ba, zama tayi akan cinyarshi ta manna kanshi a kirjinta da tayi kasa da towel ɗin, fararen soft yatsunta ta ɗaura akan gashinshi, a hankali ta manna bakinshi kan breast nata, cikin sanyin jiki da karyewan zuciya ya fara sucking yana rufe ido, shafa kanshi take tana sauke ajiyan zuciya, shima ajiyan zuciya yake saukewa a nitse ya kashe wutan ɗakin ya kwantar da ita akan gadon, duk abinda yake yana hawaye har ya zame towel ɗin duka ya cire tareda trouser da boxer na jikinshi, tana jinshi ya fara wasu hot romance da tasan sabida halin da yake ciki na damuwa yake yi ko zai samu natsuwa, amma ina har yanzu idanunshi bai daina ganin ameesha wacce take sanye da uniform ba, cikin sanyin murya yace "manal ina cikin damuwa"
tausayi ya bata, a fili tace "my abdool kayi hakuri, ina sanka sosai".
cikin sauri take shirshirya breakfast akan dinning tana duba agogon wayanta, tayi kyau sosai cikin riga dogo me ɗan kauri light purple da hulanshi data cusa tulin gashinta ciki, ta kara zama fara sosai saide ta rame tsakanin jiya da yau, hanan ce ta fito daga ɗaki tana kiranta "my meesha?"
cak ta tsaya da shiryawa jin sunan data kirata dashi, a duniya Abdool ne kaɗai yake kiranta da wannan sunan, tayi saurin yin farfar da ido domin mayar da hawayen da suka kusa zubowa, juyowa tayi da murmushi akan fuskanta tace "hanan kin manta yau akwai zuwa aiki?"
turo baki tayi, sunye take da riga da wando silk na bacci, tace "nifa na gaji"
murmushi ameesha tayi, zama tayi tace "me kika dafa mana sarkin son aiki"
tace "abincin da kikafi so"
da sauri tace "macaroni sala?"
tace "yes"
buɗewa tayi tace "wow kinji ƙamshi?"
fahad wanda yayi bacci sosai ya fito daga ɗakin yace "good morning Anty ameesha?"
tace "ya ka tashi?"
yace "fine"
ya kalli hanan yace "good morning unty hanan"
tace "morning my boy zauna muyi breakfast"
zama yayi ameesha ta zuba mishi tana kallon yadda duk ya canja, yayi baƙi saɓanin da da yake fari sol harma ya fita fari, gashi ya rame kana ganinshi zaka san yana cikin damuwa, abincin ya ɗibo ya kai baki sai kuma sukaga ya aje spoon ɗin yayi tagumi, a hankali ta dafa bayanshi tace "me?"
yace "mama bansan ina take ba, gashi imran baici komai ba yanzu na sani"
shafa bayanshi tayi cikin lallashi tace "ga can abincin Imran da kaina zan kai mishi kaci abinci ka huta kaji?"
da kyar suka lallasheshi da hanan ya fara cin abincin, yazeed ya fara saukowa daga kan stair yana kallon wayarshi, yayi kyau cikin shadda baƙi yana ta kamshi, hanunshi ɗaure da bakin shigo sannan kafanshi sanye da takalmi baƙi, ba karamin kyau yayi ba saide babu dariya akan fuskanshi, hakan kuma ya zame mishi jiki da alama, hanan tana ganin yaja kujera ɗaya ya zaune tace "yaya ka tashi? ya gajiya"
a hankali yace "fine"
ameesha wacce tasha jinin jikinta tace "good morning"
yace "morning"
fahad ma yace "good morning"
a ɗan tsorace, aje wayan yayi ya kalleshi, sai kuma ya mishi murmushi yace "morning ya kake?"
yace "fine"
yace "ya baka cin abincin bakada lafiya ne?"
girgiza kai yayi, ameesha ido ta zuba mishi da mugun mamaki jin yana magana, muryanshi da bala'in daɗi yace "gashi ka rame"
da sauri fahad ya kalleshi taya akayi yasan ya rame?
murmushi yayi kawai ya fara cin abincin, ameesha ta kalli hanan wacce take rarraba ido tasan itace take tura mishi hotuna ba kai ba gindi, tana da tabbacin a cikin hotunansu da fahad ɗin ta tura mishi, murguɗa baki tayi ameesha ta faki idon yazeed ta kwaɗa mata wayanta, karaf a idonshi ya watsa mata harara, tafiya tayi taje tasa dogon hijabi orange color har kasa yake ja da baƙin takalmi flat, hanunta rike da makullin mota ta fito ta ɗauki abincin Imran tace "saina dawo"
fita tayi ta hau motar da yake mallakinta ta fita a gidan, directly ta tafi prison kamar yadda suka saba ɗanawa suka sata yi ta ɗana ta shiga inda yake, tsaban murnan da yake ciki ya kasa bacci, yana ganin ta shigo ya tashi da gudu ya faɗa jikinta ya kankameta, hawaye masu zafi suka fara wanke mishi fuska itama hawayen take hanunta rike da flask ɗin, sun kai 5mins a haka kafin a hankali ta shafa tulin gashin kanshi daya taru sosai tace "Imran"
a hankali yace "my meesha"
jikinta yayi sanyi jin sunan daya kirata dashi, man ne yake kiranta da wannan sunan amma yanzu shi ya kirata da hakan, da kyar ta zameshi daga jininta yaki sakinta dai hawaye yake, zama tayi a kasa ta nuna mishi gefenta tace "zauna"
a hankali ya zauna ya ɗaura kanshi a kafaɗarta ya kara rungumeta, wannan karon kuka yake yi sosai ba hawaye ba, itama tana hawayen tace "to kukan me kake? ba gashi nazo ba? ina tare da kai"
cikin kuka yace "banyi zaton zaki dawo ba, nayi zaton zan karasa rayuwata anan, da baki zo ba nasan ba yanzu an ratayeni"
kuka ya kara sosai, da kyar ta lallashi kanta tace "idan baka daina ba zan tashi na tafi"
da sauri yace "na daina"
murmushi tayi ta buɗe flaks ta ɗibo abinci ta kai bakinshi tace "ci"
rabon data bashi abinci a baki yau shekara huɗu kenan, yana hawaye ya buɗe baki ya karɓa yana ci, yadda yake cin abincin cike da yunwa taji kamar ta wurgar da cokalin ta rungumeshi suyi kuka tare, amma bataso ta kara sashi kuka akan wanda yayi, peach drink me sanyi ta buɗe ta kai bakinshi, saida ya shanye tas kafin yayi murmushi yace "rabona da wannan tun ya man yana tare damu"
ɓata rai tayi kamar bata taɓa dariya ba jin sunanshi daya ambata, shiru yayi jikinshi a sanyaye yace "am sorry"
tace "me yasa ka amsa laifin da nace kayimin alkwari ko mai zai faru ba zaka amsa ba?"
yace "sabida manal tazo har nan prison ɗin, tace idan har ban amsa laifin ba zata kashe fahad hakan yasa na tsorata nace mata zan amsa shiyasa na amsa"
shiru tayi sannan ta tashi ta fara kai komo a hankali, tace "manal umar maidawa a binciken da nayi itace ta kashe mahaifinta umar maidawa"
da sauri yace "what? ta kashe mahaifinta? sabida me?"
girgiza kai tayi tace "Allah ne yasan dalili amma tabbas itace ta kashe shi, to wacce ta kashe mahaifinta da kanta babu wanda ba zata iya kashewa ba ciki harda kai harda ni harda mama harda fahad harma da shi kanshi man, sannan tunda ta ture mahaifiyarta akan stair taji wannan mummunan raunin hakan ya nuna zata iya illata kowa sabida haka ya zama dole muyi taka tsantsan da ita, sannan a binciken da nayi tanada cutan cancer a kirjinta wanda yake iya tashi a koda yaushe, sannan itace ta sace mama na kuma inada tabbacin idan na cireka daga prison zata kashe mama, to ya zama dole mu buga mata game"
tashi yayi yace "wani game kenan?"
tace "sace amminta ya zama dole mu sace mahaifiyarta sabida mu karɓo mama"
yace "amma kin san koda mahaifiyarta ta mutu ba zata damu ba tunda ta turata akan stair bata damu ba koda ta mutu?"
shiru tayi tace "shine abinda yake ɗauremin kai Imran, na kasa bacci na kasa sukuni, yaƙe kawai nake yi imran, manal muguwa ce ta karshe, ta wucemu ta ko ina, saide ayi abu ɗaya cikin biyu, ko ka tsira ta kashe mama ko kuma ka mutu ta saki mama, tanada wayo sosai shiyasa tayi hakan, tasan dole akwai abinda nake shiryawa dana bar gari, tasan ba zan taɓa barinka cikin wannan halin ba shi yasa tayi haka, ni kuma nayi alkawarin fitar da kai ta kowane hali"
yace "ki barni anan na riga na saba ki ceci mama"
girgiza kai tayi tace "mun rasa umma ta dalilin manal, na zama me son kai idan na bari muka rakasa ta dalilin manal, zanyi addu'a Allah ya fito da mama a duk inda take, kai kuma zaka fita a ranan da zamu koma kotu ina fatan ba zaka kara maimaita kuskuren da kayi a ranan can na amsa laifin da baka aikata ba?"
a hankali yace "insha Allah"
hanu ta bashi tace "promise"
sarƙe hanunshi yayi cikin nata yace "promise".
Jiddah Ce..