DUHU DA HASKE: Fita Ta 15
DUHU DA HASKE:
Na
*Jiddah S mapi*
*Chapter 15*
~Har dare yana tare dasu su faruk sun tafi sai shi da ammi da manal kawai, tagumi yayi yana tunanin ta yadda zai fara yiwa su umma maganan kuma ba zai ɓoye musu ba sabida kada suzo suji a wani wajen suyi fushi dashi, cikin dare ya turawa ameesha text "kuyi hakuri zan dawo gobe da safe akwai abinda ya taso ne"
tana gani tace "ina fatan lafiya?"
yace "lafiya ƙalau"
daga nan bai kara tura nata text ba itama bata kara ba, ammi tunda tayi salla ta kwanta akan sallayan tana bacci shi kaɗai yake zaune idonshi biyu yana kallon manal dake bacci da oxygen, juyi ta fara zata fizge drip ɗin yayi saurin rike hanunta, a hankali ta buɗe ido jin an rike mata hanu, ido huɗu sukayi tayi mishi alaman ya cire mata oxygen ɗin, cirewa yayi kaɗan, a hankali tace "ka ciremin duka zan iya numfashi da kaina"
murmushi yayi ya cire mata, a hankali tace "ka aureni?"
gyaɗa kai yayi, tace "yanzu kai mijina ne?"
gyaɗa kai yayi, tace "ni matarka?"
ya kuma gyaɗa kai, tace "zan rinƙa ganinka kullum?"
gyaɗa kai yayi idonshi cike da hawaye, tace "zan rungumeka?"
a hankali yace "eh"
rungumeshi tayi ta kankameshi, shima rungumanta yayi tace "na gode, yanzu zaka tafi dani gidanku matsayin matarka?"
a hankali yace "eh"
kallon ammi data tashi tayi tana dariya tace "ammi Abdool ya aureni yanzu ni matarshi ce ni kaɗai yake dashi nice kaɗai zan raɓeshi, zan taɓashi a duk lokacin da naga dama, bayan ni babu wata mace da zatayi hakan ko Abdool?"
gabanshi yayi mummunan faɗuwa tunawa da ameesha, tace "ko?"
da kyar yace "eh"
ganin zata sauka a gadon ya riketa yace "ki nutsu drip ɗin saura kaɗan ya kare"
fizge drip ɗin tayi tace "na warke yanzu bana jin komai mu tafi gida kawai"
ammi tace "manal ya zaki cire drip kinga hanunki yana jini?"
kallon hanun tayi yana jini sosai tace "yes na gani ammi"
man yayi sauri ya rike hanunta yace "kina ganin jini a jikinki?"
tace "ban damu ba da jini ya fito a jikina"
a ranta tace "matukar zan samu biyan bukata ta"
a fili kuma tace "ssbida na saba da hakan"
auduga ya danne wajen dashi jinin ya tsaya, ammi tace "dole sai kin hakura saboda dare yayi zuwa safe saimu tafi"
sauka tayi a gadon tasa takalmi tana jin jiri sosai tace "muje na warke banson kwanan asibiti"
man ya kalli agogo karfe biyu na dare yace "kiyi haƙuri gobe saimu tafi"
tace "no"
ammi zatayi magana yayi mata alaman tayi shiru, shirun tayi ya tashi yace "to shikenan tunda kinaso mu tafi saimu tafi"
cikin jin daɗi ta rungumeshi tace "thank you abdool I love you"
shiru yayi, ammi ta shirya ta ɗau sallayansu kawai da maganin manal already sun biya kuɗin, a motarshi suka shiga suka fara tafiya, shiru motan yayi Abdool yana tunanin yadda zai fara faɗawa su umma hankalinshi a tashe yake, hanunta yaji akan nashi baiyi magana ba har suka isa gidan, yace "ku shiga ni zanje gida sai gobe"
girgiza kai tayi tace "ba zan barka ka tafi a wannan daren ba saide mu tafi tare"
yace "no ki...."
rufe bakinshi tayi tace "nifa matarka ce ko ka manta?"
girgiza kai yayi, tace "muje ko kuma mu kwana anan"
a hankali ya shiga cikin gidan dasu, fitowa yayi tayi mishi sight hug suka shiga ciki, ɗakinta sukaje ta canja kaya zuwa na bacci sannan ta kalleshi tace "wani zai kwana babu kayan bacci yau"
tayi mishi gwalo, murmushi yayi yace "saiki bani naki nasa"
dariya tayi sosai tace "ka taɓa ganin namiji da rigan mata? ai saide mata da rigan maza"
yace "eh fa hakane sabida ameesha kullum kayana take yawan sawa"
ɗip jinta da ganinta suka ɗauke, wani irin kishi taji a ranta a hankali ta juyo tana murmushi tace "ina ganinta ai kuma yana mata kyau"
dariya mara sauti akan fuskarshi da alama idan anyi magananta yana jin daɗi, kwanciya tayi akan gadon ba zato yaji ta ɗaura kanta a cinyarshi tayi shiru, hanunshi ta ɗaura a kan gashinta dake tsantsi, shafawa ya fara a hankali ya jingina bayanshi da jikin gadon yana kallonta har tayi bacci, a hankali ya zameta zai kwantar da ita a gefe yaji ta rikeshi gam taki sakinshi, barinta yayi taci gaba da baccin, wayanshi ya buɗe yana kallon hotunan Ameesha, murmushi yake yi yana kallonta kullum tana cikin dariya ga son wasa kamar yarinya karama, yana kallon hotonsu tare ta turo baki ta shagwaɓe fuska shi kuma yana dariya, yana kallo har bacci ya ɗaukeshi wayar a hanunshi, a hankali ta buɗe ido jin yana numfashi a hankali, kallon kyakkyawan fuskanshi tayi ta shafa sajenshi dake kwance luf, karamin bakinshi me ɗauke da pinkish lips, taga gashin idonshi me tsayi a kwance, gashin kanshi me yawa da kyau da tsanti ta kalla, sai kuma ta kalli kirjinshi dake da faɗi, ta wuyan riganshi daya ɗan sauka tana iya kallon gashin dake kwance a kirjinshi, zame wayan tayi ta yadda ba zaiji ba, hoton ta kalla taga shi da ameesha ne, goge hoton tayi ta kashe wayarshi sannan ta aje a saman gadon, rungumeshi tayi taja blanket ta rufasu dashi, cikin muryan baccin da take ji tace "Abdool nawa ne ni kaɗai, babu macen da zata raɓeshi koma wacece ita"
a haka sukayi bacci Abdool a zaune ita kuma kwance a jikinshi.
washe gari a firgice ya tashi yana salati, gani yayi tana bacci sosai cikin kwanciyan hankali, tunawa yayi da duk abinda ya faru jiya, zameta ya fara daga jikinshi yaji ta rikeshi sosai, cikin sanyin murya tace "good morning"
yace "morning ya kika tashi? ya jikin?"
a hankali ta tashi tayi mishi kiss a gefen kumatu tace "da sauki"
sauka yayi daga gadon yaje toilet yayi alwala yazo ya shinfiɗa sallaya yayi salla, itama taje tayi alwala tazo tayi salla hijabin yayi mata kyau maroon, yana zaune akan sallayan ya rasa da wani ido zai kalli su ameesha ya fara faɗa musu yayi aure a daren jiya?"
a hankali tace "zamu je gidanku? Acan zan zauna?"
jijjiga kai yayi, tace "Allah yasa na samu farin cikin dana rasa a gidanmu idan naje can"
shiru kawai yayi, ammi tayi knocking tace "yes ammi"
shigowa ammi tayi tace "kun gashi lafiya? ya jikinki?"
tace "da sauki"
Abdool ya gaisheta ta amsa, tace "bari na kawo muku breakfast"
tashi yayi yace "no yanzu zamu tafi"
tace "to ita manal fa? ai zata sha magani?"
yace "zata sha acan insha Allah"
gani yayi ammi ta shigo ta tsaya a gabanshi, durkusawa tayi kasa a gabanshi ta haɗa hanu biyu alaman roko tace "Abdool dan girman Allah ka kulamin da manal, bata tashi da kowa ba sai ni da dadynta, shi kuma ya mutu ni kaɗai na rage mata sai kuma kai, zan baka amanar ta"
durkusawa yayi ya raba hanunta yace "haba ammi ya zaki durkusamin?"
tace "so nake kamin alkawarin kula da manal"
ganin tana kuka sosai yace "na miki alkawarin kula da ita, ba zan bari komai ya sameta ba"
tace "na gode Abdool"
yace "to ammi"
Address na gidansu ya bata yace "wannan shine address idan zaki zo dubata sai kibi address ɗin har gida insha Allah"
karɓa tayi tace "na gode"
haɗawa manal kayanta tayi a akwati ta rungumeta tace "manal ki kula da kanki dan Allah ki rinƙa dariya kinji?"
tace "to ammi"
kuka sukeyi, yaji tausayinsu sosai yazo yaja hanunta da akwatin yace "let's go"
tafiya sukayi ammi tana ɗaga musu hanu tana share hawaye har suka fita.
Ameesha cikin sauri take shiri, riga baƙi da wando baƙi tasa ta kame gashinta wanda yasha gyara, zama tayi a gaban mirror tana shafa powder kwalliya ta fara tana murmushi, Anty ta shigo tace "inata kiranki kinmin shiru kamar baki jina..."
da mamaki ta tsaya tana kallonta ganin tana kwalliya tace "ameesha yau kece kike kwalliya? ina zaki je?"
girgiza kai tayi tana sa ɗankunne tace "babu inda zanje gidansu man ne kamar yadda na saba zuwa kullum"
Anty tace "to yau gidansu man shine kike kwalliya dan zakije?"
tashi tayi tana ɗauko takalmi snicker tana sawa tace "yau ɗin na daban ne Anty"
kallon gaban madubin tayi taga wani ƙaramin kwalin zobe anyi kamar heart ajiki, tace "to Allah bada sa'a"
tace "ameen"
fita umma tayi ameesha ta buɗe kwalin zoben tana kallo tana murmushi, zobe ne guda biyu an yishi kamar heart sai kuma farin sunansu da aka rubuta AA wato Ameesha and Abdulrahman, a hankali take shafa zoben tace "yau zan faɗa maka abinda na jima ina ɓoyewa ko kuma ance abinda nake neman dama na faɗa maka amma bana samu, nayi yunkurin faɗa maka a lokuta da dama saide wani abin yana zuwa ya katsar mana da maganan, man tun muna yara muka shaƙu da juna, a tunanina iya shaƙuwa kawai mukayi amma sai naga ba shaƙuwa bace so ne, man yau zan faɗa maka wani kalman daya jima yana damuna a raina"
kallon kanta tayi a madubi tace "man yau zan bayyana maka soyayya ta sannan na baka wannan zoben dana jima ina jiran a kawomin, na tara kuɗi da kyar kafin na samu na siya mana domin zobe ne mai tsada, duk kuɗin da nake samu a aikina saina raba kashi uku ɗaya na kashewa ɗaya nasu Imran ɗaya kuma saina tara kuɗin wannan zoben da nake jiran wannan ranan da zan bayyana maka komai"
murmushi ta yiwa kanta, ta juya zata tafi sukayi ido huɗu da fahad, murmushi yayi mata yace "unty ameesha nida Imran kullum wannan shine burinmu wato muga kunyi aure da ya Abdool, gashi Allah ya karɓi addu'armu ke da kanki kikayi wannan tunanin, mun san ya abdool baida matsala matukar kikace eh to komai ya wuce, dama munyi expecting matsala daga wajenki muna ganin ba zaki yadda ba kasancewar ku best friend amma tunda kin yadda munji daɗi"
tace "amma fahad naji ana cewa idan mace ta fara cewa tana son namiji zai rainata"
shan shayin dake hanunshi yayi saida ya haɗe kafin yace "babu maganan raini tsakaninki da ya Abdool ina nan ina tayaki da addu'a Allah yasa ya bada sa'a"
cikin jin daɗi tace "kasan akan me zanje?"
ya girgiza kai tareda taɓe baki, tace "akan mashiiiiiiin"
dariya yayi ganin ta fita a guje, mashin ɗinta data ɓoye ta ciro tana goge kuran da yayi, hawa tayi cikin farin ciki da kyawun da tayi da kwalliya ta fita zuwa gidansu man.
zata shiga mota tace "no mu bari sai gobe akawo motocin"
tace "to"
yana rike da akwatin ɗayan hanun kuma yana rike da hanunta suna tafiya, napep ya kama musu ya fara sa akwatin sannan ta shiga shima ya shiga sukayi shiru ne napep ya fara tafiya zuwa inda ya faɗa mishi, Abdool banda tsinkewan zuciya babu abinda yake yi, a hankali tace "Abdool kana ganin family ɗinka zasu soni?"
kallonta yayi tayi kyau cikin hijabi maroon ɗin yace "eh mana"
daga nan bai kara cewa komai ba shi kaɗai yasan abinda yake ji, da haka har suka isa kofan gidan yana rike da akwatin suka nufi gidan shiga sukayi hanunshi a sarke da nata, knocking na falon yayi yana tsaye tana gefenshi, suna zaune a falo Imran yana latsa game umma kuma tana ɗinka wani waje daya warware jikin tabarmanta, jin ana knocking tace "waye?"
a hankali yace "Abdool ne"
da sauri ta tashi tace "Abdool ka dawo? ameesha tace mana kaje wani never motarka ta ɓaci a hanya saida ka kwana"
buɗe kofan tayi tana cewa "Allah sarki banji daɗin hakan ba ka....."
shiru tayi ganinshi da manal hanunsu rike da juna kanshi a kasa, da sauri tace "me...me...me hakan? tare da ita kukaje meeting ɗin?"
girgiza kai yayi, tace "to me ya faru kuka taho tare da sassafe haka?"
a hankali yace "kiyi hakuri umma"
cikin mamaki tace "hakurin me Abdool na kasa gane komai meya faru?"
kanshi kasa yace "kiyi hakuri"
cikin tsawa tace "wai meya faru?"
ameesha tun daga kasa kamar yadda take kiranshi idan zasuje neman aiki ta fara ƙwala mishi kira domin ya tura mata text ya dawo
tace "maaaaaaaan maaaaaaan?"
sauka tayi daga mashin ɗin ta shiga ciki, zoben yana hanunta duka biyu ta shigo tana murmushi na musamman tace "man yau nazo na faɗa maka abinda kullum nake cewa inaso na faɗa maka....."
tsit tayi da idonta ya sauka akansu suna sarke da hanun juna, umma cikin tsawa tace "ka faɗamin me yake faruwa ka sani a gaba kaki kallo na, meyasa kazo da ita, wacece ita ɗin bayan shugabanka a wajen aiki?"
yace "MATATA"
cikin shock ameesha ta kalleshi itama umma cikin shock take kallonshi, da kyar ta harhaɗa magana tace "ban..ban...gane ba"
ya durkusa kasa yace "umma kiyi hakuri ki yafeni na auri manal jiya shine abinda ya hanani dawowa gida"
da sauri ameesha ta ɓoye zoben dake hanunta, baya baya ta fara, umma tace "sabida me ka aureta?"
a hankali yace "sabida ina santa"
rike kofa umma tayi dan jiri ne yake shirin zubar da ita kasa, tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
duk yadda taso ta daure saida jirin ya kusa fin karfinta, tace "ta yaya zan yadda da cewar ka aureta?"
wayanshi ya buɗe ya kunna mata voice ɗin ɗaurin auren da sukayi da sunanshi da sunanta da kuma waliyyai da kuma kuɗin sadaki"
duhu ta fara gani a hankali ta juya zata shiga ciki jirin yaci karfnta tayi baya zata faɗi da sauri manal taje zata riketa cikin tsawan da yasa manal ta koma baya tace "karki sake ki taɓani"
faɗuwa zatayi Imran ya riketa, a hankali ya riketa ya kaita kan kujera, ameesha baya baya ta fara cikin sanɗa ta buɗe kofan zata fita yace "meesha"
tsayawa tayi cak bata juyo ba, yace "please nasan ke zaki fahimceni nasan koda kowa bai yadda ba ke zaki yadda, nasan koda basu yadda dani ba ke zaki yadda dani, please kada ki tafi kinji?"
watsar da zoben dake hanunta wanda taji kamar ZOBEN WUTA ta riƙe sannan ta share hawayen a ɓoye, juyowa tayi fuska ɗauke da murmushi tace "ƙaddara ce dole saiya faru"
yace "please kada ki tafi"
a hankali ta dawo tana danne komai na ranta, zata shiga cikin ɗakin manal ta rike mata hanu, batayi magana ba tayi shiru, manal tace "ki shiga dani"
a hankali ta rike hanunta tace "bismilla ki shigo"
shiga tayi umma banda kallon tsana babu abinda take aika mata, Abdool ma ta shigo, ameesha zata zauna manal tace "ki kaini ɗaki sabida na bashi waje da umma"
a hankali tace "to muje"
akwatinta taja, tana gaba manal tana baya suna tafiya har zuwa cikin ɗakinsu man, aje akwatin tayi sannan tace "wannan shine ɗakinshi"
juyawa tayi zata tafi ta kara rike mata hanu, a hankali tace "me kuma kike buƙata?"
tace "kowace amarya ana yimata lalle da kitso me kyau idan za'a kawota ɗakin mijinta, ni kuma ban samu wannan gatan ba, ina rokonki wani alfarma guda"
bata kalleta ba tace "menene?"
tace "zanso kiyi min yadda ake yiwa kowace amarya, kwalliya da kuma sa mayafi a rufe kai har sai ango yazo ya buɗe da kanshi"
a hankali tace "to"
zuciyanta kamar wuta, har jikinta ya fara zafi zazzaɓi yana shirin sauko mata, kaya ta cire mata atamta me matukar kyau ta aje mata tace "ki shirya"
kallon atamfan tayi sannan tace "wannan baki ganin yayi local Abdool ya ganni dasu?"
canja mata tayi zuwa wani arenen leshi me kyau, karɓa tayi tasa, ɗankwalinta ta ɗaura mata me kyau ta shafa mata powder da lipstick, mayafi irin leshin ta ɗauko ta rufa mata akanta sannan ta fesa mata turare me kamshi tace "na tafi"
share hawaye tayi bayan ta juya, zata fita kenan Abdool yayi sallama jikinshi a mace ya shigo, kin kallonshi tayi zata wuce ya rike hannunta, bata kalleshi ba shima bai kalleta ba, yace "ina zakije?"
urmushi tayi mishi kamar ba abinda yake damunta taja kumatunshi cikin wasa tace "zanje gida mana man"
yace "okay amma zaki dawo?"
jijjiga kai tayi tace "eh zan dawo"
manal da take kallonsu ta cikin mayafin taji kirjinta yana zafi ganin ya juya gaba ɗaya yana kallon ameesha ta janyo wani biro dake gefen gadon ta fara caccakawa akan hanunta tana jin azaban zafi tana yi tana kallonsu, a hankali ameesha ta zame ta fita, har tayi nisa yana kallonta, umma tace "ameesha ina zakije?"
tace "Anty tamin miss call zanje naji ko me ya faru"
cikin kuka umma tace "ameesha kina ganin abinda yake faruwa? ameesha Abdool ya auri wannan me kama da mugayen, meyasa ya biyewa zuciyanshi ya aureta? shin baiga mugunta bane a idonta?"
da sauri tace "umma zanje kada Anty ta kara kirana"
bata jira me zatace ba ta fita da gudu, da Imran sukayi karo a kofa ya ganta tana hawaye tana gudu, ɗauke kai tayi daga shi ta fita a gidan, mashin nata ta hau da wani irin gudu ta take zoben data watsar a take suka kakkarye, gidansu ta nufa da gudu akan mashin ɗin tana kuka, koda ta isa gida aje nashin ɗin tayi a ciki sannan ta wuce Anty da fahad da suke falo ta faɗa ɗakinsu da fahad akan gado ta fashe da kuka, tare suka shigo sukace "meya faru?"
saida tayi kuka me isanta kafin ta tashi tazo kusa dasu ta kalli fahad da ya shiga cikin damuwa da hawaye a fsukanta tace "kamin alkawari"
yace "to na me?"
tace "kamin alkawari ba zaka faɗawa kowa ina son man ba"
yace "sabida me? bai yadda bane?"
girgiza kai tayi tace "kamin alkawari kawai"
yace "nayi alkawari ba zan faɗawa kowa ba"
Anty tace "amma sabida me ameesha?"
juya baya tayi tace "man yayi aure"
a firgice sukace "aure?"
gyaɗa kai tayi bata juyo ba tace "ya auri manal jiya"
fahad a fusace yace "shiyasa naji na tsani manal ɗinnan tunda na ganta shima ya Abdool saina gaggaya mishi magana"
zai fita ta tare kofan hawaye kamar zasu kare a idonta tace "no banaso ka manta kayi alkawari?"
yace "a,a"
rungumeshi tayi tana kuka, a hankali yake ɗan bubbuga bayanta sai kankameshi take kara yi tana wani irin kuka me cin rai, kallon bayanta fahad yayi yana jin yadda yayarshi take kuka yana taɓa mishi zuciya, ji yayi kamar yaje gidansu man ya shaƙeshi ko zaiji sauƙin abinda yake ji.
shiga yayi ya zauna kusa da ita har yanzu idonshi akan kofa tunda ameesha ta fita, so yake ya bita amma baison barin manal ita kaɗai, a hankali ya ɗaga nata mayafin yace "kinyi kyau sosai"
tace "na gode"
fuskanta da damuwa tace "amma ummanka..."
da yatsa ɗaya ya rufe mata baki yace "shiiiii umma dole zatayi fushi kuma nasan zata sauko"
tace "to Allah yasa"
yace "ameen"
umma Imran tasa a gaba tana kuka tace "man ya ɓata komai tunda ya auro wannan yarinyar, wallahi Imran haka kawai nake jin tsananta tun daga kasan zuciyata wallahi na tsaneta"
lallashinta yake yace "nima umma na tsaneta wallahi bana santa"
da kyar ya samu ya lallasheta ta daina kukan, har dare kowa rai babu daɗi, Imran ya taimakawa umma ya kaita har ɗakinta sannan ya fita zuwa ɗakinsu, knocking kawai yayi ba jira sun amsa ba ya tura kofan ya shiga, kallo ɗaya yayi musu manal tana shafa fuskanta a sajen Abdool tana murmushi jin ya shigo ta janye a hankali, gadonshi ya fara ja daga ɗakin, Abdool yana kallanshi har ya fitar da gadon ya kai ɗakin umma, dawowa yayi ya kwashe duk wani abu da yasan nashi ne ya komar ɗakin umma, rufe musu kofan yayi cikin damuwa ta kalleshi, yayi murmushin yaƙe yace "karki damu ba abinda zai faru dole zasuyi fushi dani"
tace "fushi da kai? ko kuma dai basa sona?"
yace "a,a suna sonki"
murmushi tayi tace "to na gode"
ameesha tana kwance akan gado kanta akan cinyar mama ta rufe ido kamar me bacci, a baɗini tunani take, da kyar ta samu tayi bacci a ranan.
a haka har sukayi kwana uku, manal kullum sai tazo ta gaida umma, ko kallonta batayi bale ta amsa, ameesha kuma ta ɗauke kafa daga zuwa gidan, man yana iya kokari dan ganin yasa manal farin ciki, can kasan zuciyanshi yana jin zafin rashin zuwan ameesha gidansu, ya kira wayarta ta amsa tace babu komai kawai bata ɗan jin daɗi ne amma idan tayi sauki zata zo, shiru yayi dan yasan ba gaskiya take faɗa ba, ya san idan hatada lafiya yadda take da kuma idan tana lafiya, tana kwance akan kujera tana karanta littafi taji an kwace, da sauri tace "waye?"
kallon man tayi ya tsaya yana kallonta, murmushi tayi mishi tace "kaine?"
zama yayi kusa da ita yace "dariya, wasa, neman tsokana rashin hakuri duk ina kika kaisu ne? kin daina zuwa gidanmu kin daina shiga harkana umma ka ta daina yaune kawai ta amsamin gaisuwa Imran ma baya min magana sosai, me yasa hakan? dan nayi aure?"
da sauri tace "no ba haka bane"
yace "in dai ba haka bane to ki canja"
tace "to shikenan zan canja yanzu dai bani takaddata ta"
yace "bazan bayar ba sai munje gidanmu"
tashi tayi tace "muje"
tafiya sukayi da kafa suka isa gidan, umma tana zaune tayi tagumi taji muryanta, murmushi tayi tace "ameesha?"
da sauri tazo ta zauna a kusa da umma, umma tace "Abdool kaje ka ɗaukomin ita dama tayi fushi damu"
cikin jin daɗin maganan da tayi mishi yace "ai yanzu ta daina"
dariya kawai ameesha tayi, manal jin muryan ameesha taji gabanta ya faɗi, kirjinta ya bada sautin dum, da sauri tasa hijabi karami ta fito, ganinta tayi kusa da abdool da sauri ta zauna a tsakaninsu tace "ameesha kinzo?"
a hankali tace "eh ina kwana"
"lafiya ƙalau"
umma ta tashi tace "ameesha idan kin gama ki sameni a ɗaki"
suna gama gaisawa ta tashi ta tafi dakin umma, manal tayi shiru tana wasa da yatsanta ya rike hanun yace "muje na baki labarin da nace zan baki"
murmushi tayi tace "to"
tafiya sukayi zuwa ɗaki ya fara bata labari sai dariya take wanda yake matukar kara mata kyau.
*Jiddah Ce....*
08144818849
managarciya