Dubun Wani Matashi Da Ya Kware Rufin Masallaci Ta Cika A  Jigawa

Dubun Wani Matashi Da Ya Kware Rufin Masallaci Ta Cika A  Jigawa

 

Daga Jabir Ridwan 

 

Wani matashi ya fada komar Jami'an tsaro bayan shiga karkara yana rushe masallatai da niyyar sabunta su.

 
Matashin ya fada hannun  jami'an tsaron ne a jihar Jigawa bayan korafin da al'ummar ƙauyan Kanoke suka yi akan cewa wani Matashi yazo da niyyar Damfarar dakin ibadar su.
 
Matashin ya isa garin ne da nufin sabunta wa mazauna gari masallacinsu, inda ya ce wata kungiya ce daga kasashen larabawa zata dauki nauyin aikin.
 
Saidai matshin ya cire dukkanin kofofi tagogi da kuma cire kwanon rufin masallacin tare da yin awon gaba da su.
 
Sai daga baya aka gano cewa dan damfara ne, ya kwashe rufin da kofofi da tagogin masallacin ya siyar dasu.
 
Kakakin ‘yan sandan jihar Jigawa DSP Lawal Shi'isu Adam ya ce sun kama matashin inda suka gurfanar da shi a gaban kotu.