Dubu 50 ne kuɗin sake buga shedar jarabawa----NECO

Dubu 50 ne kuɗin sake buga shedar jarabawa----NECO

Duk mai buƙatar a sake buga masa shedar jarrabawa sai ya suke mana N50,000 -NECO

Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandire ta kasa, NECO ta ce wadanda suka zana jarrabawar a yanzu zasu dinga biyan Naira dubu 50 domin sake buga shedar kammala jarrabawar tasu.

Rijistara na hukumar ta NECO, Dantani Wushishi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a garin Minna na jihar Niger.

Acewar sanarwar, an sanya Naira dubu 50 na sakw buga shedar ne bisa tsarin bibiyar kudin da ake yi a duk lokaci bayan lokaci.

Hukumar ta ce za a karbi bukatar sake buga shedar ne a cikin shekara guda na bayar da shedar ta asali. Bayan wannan lokacin hukumar baza ta amince da irin bukatar ba.

Bugu da kari, hukumar ta sanya wa'adin wata guda ga wadanda suka zana jarrabawar don mika bukatar yin gyara a sakamakon jarrabawar tasu.

Lokacin ya fara ne daga ranar da aka fitar da sakamakon a hukumance, inji NECO.