Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Dan Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasar

Dubai Ta Hana Duk Wani Dan Najeriya Dan Kasa Da Shekaru 40 Shiga Kasar

 

Gwamnatin Tarayya ta yi tsokacin kan halin da wasu yan Najeriya suka shiga yayinda aka tare su a tashar jirgin Dubai, haddadiyar daular Larabawa kuma aka hanasu shiga. 

A faifan bidiyon, 'yan Najeriyan na kukan yadda aka hanasu shiga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa duk da mallakar bizar da suka yi.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da jawabi kan wannan lamari. 
Kakakin ma'akatar, Francisca Omayuli, yace laifin yan Najeriyan ne hana su shigar. 
"Ofishin Jakadancin Najeriya dake Dubai ta yi fashin baki cewa 'yan Najeriyan da aka hana shiga sun amshi bizar za su shiga da iyalansu ne, amma suka isa Dubai su kadai ba tare da iyalansu ba." 
"Saboda haka aka korasu su koma Najeriya su nemi Bizan da ya kamata." 
"Ya kamata jama'a su sani cewa gwamnatin UAE daga yanzu ta daina baiwa duk dan Najeriya mai kasa da shekaru 40 bizar yawon ganin ido, sai dai wanda zai tafi da iyalinsa." 
Ma'aikatar ta yi kira ga duk mai son zuwa Dubai ya fahimci hakan gudun abinda ka iya biyo baya.