DSS ta bukaci X ta rufe shafin Sowore saboda sakon sukar Tinubu da ya wallafa
Hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasa (DSS) ta rubuta wasiƙa ga kamfanin X, tsohon shafin Twitter, tana neman a gaggauta rufe shafin Omoyele Sowore.
TheCable to rawaito cewa hukumar ta bayyana cewa ɗaya daga cikin sabbin sakonnin da Sowore ya wallafa kan Shugaba Bola Tinubu na iya haddasa tashin hankali da kuma barazana ga tsaron ƙasa.
DSS ta nuna cewa Sowore, wanda shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, a ranar 25 ga watan Agusta ya kira Tinubu da “ɓarawo” yayin da yake mayar da martani kan maganganun shugaban ƙasar game da cin hanci da rashawa a wani ziyarar aiki zuwa ƙasar Brazil.
A cikin wasiƙar mai dauke da kwanan wata na ranar 6 ga watan Satumba, wacce B. Bamigboye ya sanya hannu a madadin darakta-janar na hukumar, DSS ta ce “Sakon da aka wallafa” ya raina shugaban ƙasa a gaban al’ummar duniya.
“Wannan sakon har yanzu yana yawo a intanet kuma ya jawo suka daga mafi yawan ‘yan Najeriya, wasu daga cikinsu na iya ɗaukar matakai marasa kyau domin nuna ƙin amincewarsu da shi, musamman magoya bayan shugaban ƙasa da suka fara fitowa kan titi suna zanga-zanga, abin da zai iya haifar da matsin lamba na siyasa da kuma barazanar tsaron ƙasa,” in ji wasikar.
Hukumar ta danganta sakon da wasu sassan kundin laifuffuka, dokar laifukan yanar gizo da kuma dokar hana ta’addanci, tana cewa abin na iya zama laifi da za a iya haɗa shi da “ta’addanci na cikin gida.”
DSS ta dage cewa dole X Corp ta goge sakon kuma ta rufe shafin na Sowore, tare da gargadin cewa idan ba a yi hakan ba cikin awanni 24, gwamnatin tarayya za ta ɗauki “matakai masu tsanani.”
managarciya