Dole Fa Gwamnati Ta Yi Dokokin Aure A ƙasar Hausa— Dakta Mus’ab Isah Mafara
Sannan gwamnati da ƙungiyoyi ma su zaman-kan-su da ma ɗaiɗaikun mutane ya kamata su ɗauki nauyin shirye-shirye a gidajen radiyo da wasu kafafen kamar irin wasan kwaikwayo, ko sanarwowi, ko wa’azi, ko waƙoƙi, ko tallace-tallace, ko wanin su, waɗanda kacokan za a gina su ne a kan illar aurarraki waɗanda ba su da ƙaidi da illar da ke tattare da tara yara ga wanda sam bai da ikon ɗaukar nauyin su. Sannan a gargaɗi iyaye da waliyyai a kan munin ba da diyar su ga irin waɗannan mazajen wai kawai don ka da a ce su na da budurwa a gida sun ƙi yi ma ta aure.
Rubutawa: Dakta Musab Isah Mafara.
Ba labaran da ke baƙanta min rai ko yaushe na ziyarto Najeriya irin yadda
bahaushe ke walaƙanta al’amarin iyali. Daga ka ga direba wanda albashi nai
bai kai dubu talatain ba, amma ya na da mata ukku da ɗiya fiye da ishirin
sai ka ji ma’aikacin gwamnati kuma wai ‘mai ilmi’ mai hali amma ya wohintar
da jin-daɗin iyali nai. Wai ya za a yi al’umma ta ci gaba alhali mu na
kallo mazaje matalauta su na aurarraki su na zubo yara ba kan-gado bayan
mun kwan da sanin cewa ba za su iya ɗaukar nauyin yaran nan ba.
Ya za a yi a zuba ido a bar al’umma ta ci-gaba da taɓarɓarewa haka. Sannan ga wasu
‘masoya addini’ ‘yan-birni da yaran su ba su wuce ukku ko hudu ba ga tazara
ta shekara akallau ukku tsakanin yaran amma da ka ce a taƙaita haihuwa da
aure-aure sai su fara kunfan baki wai a na faɗa da addini.
Wallahi ba yadda za a yi Musulunci ya umurce mu da irin wanga tara iyali da
mu ke yi a ƙasar Hausa na ba gaira ba sabat. Ka na da albashi da bai kai ya
kawo ba amma wai da ka samu wasu ‘ƴan kuɗin hutu ko kasuwa ta yi kyau sai
ka je ka ƙara aure ka yi ta haihuwa ka sako ma al’umma yara ta san yadda za
ta yi da su. Ga matar ka — ko matan ka — da yaran ka gida su na cikin
wahala amma kai jin-dadin gaban ka kawai shi ka ke kallo ba maslahar iyalin
ka ba. Mu na zaune ba wata doka ko tsari ko al’ada da za ta bincika ta gani
ko mai son ƙara aure ya kai munzalin a bar shi ya ƙara aure ko kuma a’a. Mu
na zaune mu na kallo mutane su na haiho yara su bar su ga titi su na
gararamba, ba su san cin su ko shan su ko wurin kwanan su ba? Yara su zo su
addabi mutanen unguwa da sace-sace da dabanci, ba su ganin girman kowa ba
su jin maganar kowa Kai! Wallahi akwai haɗari!
Rashin fahimtar tawakkali ne ka yi ta haihuwa ba tare da ka yi wani tanadi
ma yaran ba kawai kai ka na da tunanin cewa bakin da Allah Ya tsaga to zai
ba shi abun da zai ci. E, za su ci gidan maƙwabta, za su ƙwato, za su sato,
za su barato. Kai kuma ku je lahira Allah Ya yi ma ka hisabi na cin-haƙƙin
yaran da ba su ji ba ba su gani ba. Wai in ba jahilci da son-rai irin na
bahaushe ba ya za a yi ka taƙarƙare kan sunnar aure ka watsar da farilla ta
takalihun iyali. Kai bagidajen ina ne! An san Allah Ya na talauta attajiri
ya azurta talakka amma mazon Allah (SAW) ma cewa ya yi wanda ke da HALI ya
yi aure. Wallahi irin bala’in da ke fuskantar ‘kasar Hausa — ba fata ni ke
yi ba — ya dama matsalar boko-haram da bandits ya shanye in a ka ci-gaba da
tafiya haka .
Dole fa gwamnati ta yi dokoki na aure a ƙasar Hausa kwatankwacin waɗanda
Maigirma Sarki Sanusi II ya nemi da a yi can baya. Na san ba mutane mu ke
ma su bin doka ba kuma gwamnatocin mu ko dokar da za ta kawo mu su ƙarin
kuɗin-shiga ba su tabbatar ba balle doka ta inganta zamantakewar al’umma.
Duk da haka dai mu na roƙon gwamnatocin arewa da su yi dokokin su kuma yi
ƙoƙari na tabbatar da su. A kuma ba al’umma ilmi gwargwadon hali saboda
duhun jahilci ke sa wasu mutanen ke gudanar da rayuwar su ta iyali kamar
dabbobi. Sannan mu na roƙon malaman mu da su wa Allah su gargaɗi mutane a
kan illar tara mata da zubo yara ga wanda bai da abun takalihun su. Mutanen
mu su na girmama magana in a ka biyo da ita ta addini. A nuna mu su irin
haƙƙin da Allah Ya aza mu su na kula da mata da yaran su.
Sannan gwamnati da ƙungiyoyi ma su zaman-kan-su da ma ɗaiɗaikun mutane ya
kamata su ɗauki nauyin shirye-shirye a gidajen radiyo da wasu kafafen kamar
irin wasan kwaikwayo, ko sanarwowi, ko wa’azi, ko waƙoƙi, ko
tallace-tallace, ko wanin su, waɗanda kacokan za a gina su ne a kan illar
aurarraki waɗanda ba su da ƙaidi da illar da ke tattare da tara yara ga
wanda sam bai da ikon ɗaukar nauyin su. Sannan a gargaɗi iyaye da waliyyai
a kan munin ba da diyar su ga irin waɗannan mazajen wai kawai don ka da a
ce su na da budurwa a gida sun ƙi yi ma ta aure.
Wallahi dole mu ja daga mu yaƙi wasu mugayen ɗabi’u na alummar mu. Kuma mu
rufe idanu da kunnuwan mu ga duk mai suka da waɗanda za su yi zargin cewa
faɗa da zubo yara barkatai irin na bahaushe kamar faɗa da addini ne. Haba!!!