Dayawan  Mayakan Boko Haram A Yunkurin Kaucewa Yawaitar Hare-haren Sojoji Suna  Neman Mafaka Najeriya

Dayawan  Mayakan Boko Haram A Yunkurin Kaucewa Yawaitar Hare-haren Sojoji Suna  Neman Mafaka Najeriya
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
 
Daruruwan mayakan kungiyar Boko Haram ne ke tserewa daga da dazukan da ke shiyar Arewa Maso Gabashin Najeriya don kaucewa hare-haren sojoji ta sama da kuma ambaliyar ruwa don neman mafaka a yankunan Niger kamar yadda wata majiya ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP,
 
Wata majiyar tsaro ta ce tun daga watan daya gabata ne yan Boko Haram din ke tserewa daga dajin Sambisa bayan kaddamar da hare-haren da sojoji sukayi a mafakar su ga kuma mamakon ruwan saman da ake yi da ya haifar da ambaliyar ruwa, 
 
Al'ummar da ke zaune a yankin sun ce a ranar Litinin din data gabata sunga manyan motoci sama da 50 dauke da mayakan Boko Haram da iyalansu da ke kyautata zaton masu biyayyane ga tsagin bakura Buduwa, 
 
Shiyar arewa maso gabashin Najeriya dai ya kwashe shekaru 13 yana fama da matsalar masu tada kayar baya da suka yi sanadiyar mutuwar samada mutane dubu 40 da kuma raba wasu samada miliyan 2 da muhallansu.