Dawo da dalibbai 88 daga jami'ar Cyprus uwaye sun baiwa gwamnatin Zamfara shawara
Kungiyar uwayen dalibai dake karatu Cyprus sun nuna rashin gamsuwarsu kan kudirin gwamnatin Zamfara na dawo da dalibbai 88 gida ba tare da sun kammala rubuta jarabawar karshen zangon karatunsu a can ba.
Bayanin wanda shugaban kungiyar Ambasada Ibrahim Tudu ya fitar ya ce uwaye da maga'isan dalibban ba su goyon bayan kudirin a dawo da yaran gida ba su kammala rubuta jarabawarsu ta karshe ba.
"Zangon da ya rage su kammala karatunsu na Digiri ba su kare shi ba, ka ko ga dawo da su gida ba su kare ba, ba abin amincewa ba ne."
A cewarsa uwaye sun yi matsaya a tuntubi wadanda abin ya shafa tare da kira gare su kar su siyasantar da lamarin abar yaran su ci moriyar karatun da suka soma, kan haka gwamnatin Zamfara da jami'ar Cyprus su fahimci hakan.
Ya yi bayanin cewa a farko Gwamnatin Zamfara ta yi alkawalin shiga cikin lamarin amma har yanzu ba abin da aka yi, sun fahimci jan kafar yana kara haifar da cikas.
"Mu uwayen dalibban 88 'yan asalin Zamfara dake karatu a can, muna fadi da babbar murya ba mu aminta da a dawo mana da yaranmu ba tare da sun kammala karatunsu na digiri ba.
"Kungiyarmu tana kira ga Gwamna Dauda Lawal da gwamnatinsa ta sake nazari kan dawo da dalibban gida a dubi cigaban jiha da kuma yaran."
A bayanin suna bukatar gwamnati ta biya bashin da ake bi a samar da takardar yarjejeniya da jami'ar Cyprus da za ta bayar da dama ga dalibban su kammala karatun su.
managarciya