Tsohon gwamnan Sakkwato Malam Yahaya Abdulkarim ya bayyana cewa matukar 'yan siyasa a wannan zamani ba su dauki matakin hana yawo da makami da matasa ke yi a wuraren yakin neman zabe ba tau ba za a samu zaman lafiya a yayin gudanar da zabe ba.
Tsohon gwamnan a wurin taron Majalisar Hadin guiwar musulmi ta jihar Sakkwato mai taken
Gudunmuwar shugabannin siyasa a wajen wanzar da zaman lafiya:kafin da lokaci da kuma bayan zaben 2023, wanda aka gudanar a dakin taro na kasa dake Kasarawa a birnin jiha a Lahadin da ta gabata, ya ce 'yan siyasa su hana yawo da makami shi ne kawai abin da zai kawo zaman lafiya,' a cewarsa.
Ya cigaba da cewa yakamata gwamnati ta sani rashin aikin yi ke sanya matasa daukar makami kan haka a fito da hanyoyin da za su samu abin dogaro domin su jingine bangar siyasa.
"'yan takarar su daina fita hayancinsu domin bokaye sun fada masui za su ci zabe, bayan sun salwantar da dukiyarsu gaba daya ba a samu nasara ba sai su so kowa ma ya mutu, hakan ba daidai ba ne.
"'Yan siyasa su ji tsoron Allah kar su wahalar da kansu domin abin da Allah ya kaddara shi zai tabbata" a ceawar Malam Yahaya.
Ya bayarda shawara hanaya mai sauki da za a gudanar da harkokin zabe lafiya, ya ce a yi kwamiti mai karfi da kowane dan takara na girmama mutanen kwamitin a jiha su rika bibiyar aiyukkan kamfen na jam'iyu don samar da gyara a duk sanda aka an yi ba daidai ba.
Ya ce 'yan takara da shugabbanni kuna da aiki gaban ku don mai ci ya sani wanda bai ci ya sani, don haka a bari kowa ya zauna lafiya.
Tsohon gwaman ya kalubalanci hukumar zabe kan kudin da jam'iyu da 'yan takara za su kashe ya ce hukumar zabe ba ta iya daidaita yanda za a kashe kudi a zabe magana ce kawai take yi dan siyasa ne kadai ke sani adadin abinda ya kashe a wurin kashin ba su la'akari da kudin da aka kayyade masu domin suna neman nasara ne ido rufe.
Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal a wurin taron ya ce yakamata 'yan siyasa su mayar da hankali kan abin da za su yi wa mutane ba sukar juna ba, 'yan takara su guji baiwa kansu nasara tun kafin sanrwar hukumar zabe.
Ya ce yin aiki da adalci su ne ke kawo zaman lafiya, in Allah ya ba ka kar ka waiwayi baya a cikin jagorancinka, 'in zamu dauki abubuwan da aka fada a wannan dakin taro a jihar Sakkwato za a yi saiyasa mai tsafta da zaman lafiya,' a cewar Tambuwal.
Sarkin musulmi ya nuna gamsuwarsa kan wannan hobbasar da 'yan kishin jiha suka yi na hada dukkan jam'iyun siyasa wuri daya don samar da matsaya daya kuma a bangarensa masarauta za ta rika gudanar da addu'o'in samun zaman lafiya duk wata, a daya daga cikin masallatan jumu'a na jiha, har a kammala zaben 2023.
Farfesa Mansur Sa'id ne ya gabatar da kasida, malamai uku suka yi masa taliki.