Dauda Lawal Na PDP Ya Kayar Da Gwamnan Zamfara

Dauda Lawal Na PDP Ya Kayar Da Gwamnan Zamfara

Dan takarar Jam’iyyar PDP, Dauda Lawal-Dare ya ci zaben Gwamnan Jihar Zamfara, inda ya kayar da gwamna mai ci, Bello Muhammad Matawalle da ke neman tazarce.

A wannan Talatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa Dauda Lawal-Dare na ya zama zababben Gwamnan Jihar Zamfara bayan ya samu kuri’u 377,726 daga kananan hukumomi 14 da ke jihar.

Baturen zaben da aka gudanar ranar Asabar kuma Shugaban Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, Farfesa Kassimu Shehu, ya ce Gwamna mai ci Bello Matawalle na APC ne ya zo na biyu a zaben da kuri’u 311,976.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Matawalle ya ci zaben wa’adinsa na farko ne a Jam’iyyar PDP, amma daga bisani ya sauya sheka zuwa APC mai mulki a matakin kasa.

Shi dai Dauda Lawal zaben sa a matsayin dan takarar PDP ya kasance mai cike da rudani, inda tun aka yi ta takaddama bayan da ya yi nasara a zaben farko.

Daga baya abokan takararsa suka je kotu, ta soke zaben, ta ba da umarnin a sake wani sabo, amma duk da haka ya sake yin nasara.