Home Siyasa Dattawan Jihar Rivers sun yi gargaɗi kan yunkurin tsige Gwamna Fubara

Dattawan Jihar Rivers sun yi gargaɗi kan yunkurin tsige Gwamna Fubara

16
0

Ƙungiyar Dattawa da shugabannin Jihar Rivers, ta nuna damuwa kan sanarwar neman tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Ordu.

Shugaban riƙon ƙungiyar, Dr. Gabriel Toby, wanda tsohon mataimakin gwamnan jihar ne, ya soki wannan yunkuri a cikin wata sanarwa da aka fitar a Port Harcourt ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa ‘yanmajalisar dokokin jihar Rivers sun bayyana shirinsu na tsige Fubara bayan wani taron gaggawa da suka yi ranar Laraba.

Mr Toby ya ja hankalin cewa tsigewa wani muhimmin tsari ne a kundin tsarin mulki, bai kamata a yi amfani da shi don biyan bukatun siyasa ko rikicin ɓangaranci ba.

A cewarsa, dalilan da ‘yan majalisar suka bayar don yunkurin tsige gwamnan ba su da ƙarfi, ba su da inganci kuma babu wani uzurin da ya shafi muradun jama’a ko kuma da ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here