Dan takarar Gwamanan Sakkwato a jam’iyar ADC ta tsallake rijiya da baya
Dan takarar gwamnan Sakkwato a jam’iyar ADC Honarabul Manir Muhammad Dan’iya ya koka kan yunkurin salwantar da rayuwarsa a wani hari da jami’an tsaro mallakar jihar Sakkwato(community Guard) da Marshall suka kaiwa tawagarsa a uguwar Airport da karfe 9:00 na daren Jumu’a.
A bayanin da mai magana da yawun dan takarar Gwamnan Alhaji Aminu Abdullahi ya fitar ya bayyana cewa bayan sun yi rakiya ga Sanata Aminu Waziri Tambuwal zuwa filin jirgi a hanyarsu ta dawowa suka ci karo da wani cinkoso wanda suka tsaya anan fa dan takarar ya yi fitar kutsu in da aka yi yunkurin hallaka shi.”Wannan lamari ne mai hadari wanda aka yi yunkurin halaka rayuwa ta, jami’an tsaro mallakar jiha rukuni biyu sun rufe hanya sun hanani wucewa, suna fadar umarni ne aka ba su daga sama kar su bari na koma cikin garin Sakkwato.
“A kokarin da masu tsaron lafiya ta suka yi na tseratar dani ne aka samu musayar halbi, an lalata min mota jami’an tsaron farin kaya(DSS) da ke tare dani sun tsare su,” kalaman Dan’iya.
Dan takarar Gwamnan ya nemi jami’an tsaron jiha su yi bincike kan lamarin da ya sanya rayuwwarsa cikin hadari. ya ziyarci kwamishinan ‘yan sanda na jiha don sanar da shi lamarin ya kuma ga barnar da aka yi masa.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da majalisar tarayya da kungiyoyin kare hakkin dan aadam da su mayar da hankali kan abubuwan da ke faruwa a jiha domin daukar matakin kare dimukuradiyya.
Ya nemi mutanen Sakkwato musamman magoya bayansu da su kwantar da hankalinsu a bar jami’an tsaro su yi aikinsu domin hakkin gwamnati ne ta kare mutanen kasa, “a bincike lamarin, a kuma tabbatar da Sakkwato ba ta koma cikin harkar bangar siyasa ba,” ya bayyana.
Mai baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan harkokin jami’an tsaron marshal Alhaji Almustafa Kwandawa jin ta bakinsa kan lamarin ya ci tura domin wakilinmu ya kasa samunsa a waya.






