Home Labarai ‘Dalilinmu Na Gudanar da Sallah Ba Ranar da Sarkin Musulmi Ya Aiyana...

‘Dalilinmu Na Gudanar da Sallah Ba Ranar da Sarkin Musulmi Ya Aiyana ba’ 

1
0


 

Malamin addinin musulunci Malam Musa Lukuwa ya ki bin umarnin Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya gudanar da sallah karama tare da mabiyansa a wannan Lahadin sabanin Litinin.



A jiya Assabar Sarkin Musulmi ya sanar cewa watan Shawwal na wannan shekara ta 1443 bai kama ba.
Mabiya malamin sun gudanar da Sallar ne a birnin Sakkwato da karfe Takwas na safe.
A bayaninsa ga manema labarai Lukuwa ya ce ya samu cikakken rahoton ganin jinjirin watan a wasu wurare na Nijeriya da wajenta.



Ya kuma ce ba wata da’a ga kowa wurin saba ubangiji, “duk wanda ya yi azumi a yau ya yini ne da yunwar banza ba wanda ya sa shi domin wata azumi ya wuce” a cewarsa.  

Al’ummar kasar Nijar sun yi sallah a yau Lahadi suma domin wata ya bayyanu a kasarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here