Dalilinmu Na Goyon Bayan Takarar Lamido---Shugabar Matan APC

“Muna son in ya samu nasara ya taimakawa jama’a da talakawa, ya kara ba da gudunmuwa mu samu tsaro domin ba mu da tsaro a yankin nan kowa ya sani, ya kara bude hanayensa wurin  magance mana yunwa domin mutane suna cikin wahala da taimakon Allah cikin gudunmuwarsu mutane za su samu walwala domin Lamido mai yi ne, ya yi an gani tun ba a tsayar da shi takarar Sanata ba,”

Dalilinmu Na Goyon Bayan Takarar Lamido---Shugabar Matan APC

Shugabar Matan jam’iyar APC a karamar hukumar Illela Hajiya A’i Argungu ta bayyana karfin jam’iyar APC a Sakkwato wani abin tinkaho ne da karfin guiwa da zai sanya nutsuwa ga dukkan magoya bayanta a jihar Sakkwato.

Hajiya A’i a hirarta da wakilinmu a lokacin da dan takarar Sanata a yankin Sakkwato ta gabas Honarabul Ibrahim Lamido  ya ziyarci karamar hukumarsu a ranar Assabar ta ce “mu nan mutanen Illela abin da muke gani duk Sakkwato ba jam’iya kamar APC saboda tana da mutane masu taimako da kirki da mutunci, ba mu da mutanen banza, da ikon Allah za mu samu nasara a 2023 daga kan shugaban kasa har zuwa kansila jam’iyarmu ce za ta samu nasara,” a cewar shugabar mata.

Wadanne dalilai ne ya sa kuke goyon bayan takarar Lamido? Ta ce “Lamido muna goyon bayansa saboda mutuncinsa da kirkinsa da taimakon jama’a da yake yi, yana da mutunci gare mu, saaboda duk yanda kake yana girmama ka ya jawo ka a jiki, shi bai san nuna wariya ba; shi ne ya sa muke sonsa kuma da yardar Allah zai yi nasarar samun kujerar Sanata da yake nema.

“Muna son in ya samu nasara ya taimakawa jama’a da talakawa, ya kara ba da gudunmuwa mu samu tsaro domin ba mu da tsaro a yankin nan kowa ya sani, ya kara bude hanayensa wurin  magance mana yunwa domin mutane suna cikin wahala da taimakon Allah cikin gudunmuwarsu mutane za su samu walwala domin Lamido mai yi ne, ya yi an gani tun ba a tsayar da shi takarar Sanata ba,” kalaman Hajiya  A’i.