Home Labarai Dalilin Kotu na bayar da belin Malami da Matarsa da ɗansa kan...

Dalilin Kotu na bayar da belin Malami da Matarsa da ɗansa kan miliyan 200

8
0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba belin tsohon ministan shari’a kuma Babban Lauyan Tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, akan kudi naira miliyan 200, tare da matarsa Asabe Bashir da kuma ɗansu Abdulaziz Malami, a wata shari’ar zargin wanke kuɗi da ake yi musu.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin ba da belin na naira miliyan 200 kowannensu, tare da gabatar da mutun biyu da zasu tsaya musu.

A cikin sharuɗɗan belin, kotu ta umarci cewa ɗaya daga cikin masu tsaya musu dole ne ya miƙa takardun mallakar gida da ke yankunan Maitama ko Asokoro a Abuja.
Kotun ta kuma umarci waɗanda ake tuhuma su miƙa fasfo dinsu na ƙasashen waje ga kotu.

Har sai sun cika dukkan sharuɗɗan belin, Malami, matarsa da ɗansu za su ci gaba da kasancewa a hannun Nigerian Correctional Service.

Daga baya mai shari’a Abdulmalik ta ɗage shari’ar zuwa ranar 16 ga Maris, 2026, domin fara sauraron shari’ar.

Ana zargin Malami tare da matarsa da ɗansa da almundahanar kuɗi kimanin naira biliyan 8.7, ta hanyar amfani da wasu kamfanoni da kuma sayen kadarori.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here