Dalilin Da Ya Sanya Hukumar Kawar Da Fatara Ta Karrama Ma’aikatanta A Sakkwato
“Kulum za ka samu Hajiya tana ofis ana ta fitowa da shiratuwa da za su taimaki talaka da kawar masa da radadin talauci, na tabbata duk aka fara aiwatar da tsare-tsarenta lalle talaka a Sakkwato zai kara tabbatar da ya zabi gwamnatinsa da ke tausayinsa sabanin in da aka fito a baya da ake daukar mukami a baiwa wadanda ba su cancanta ba, kuma a barsu da dubararsu,
A kokarin da hukumar kawar da fatara ta jihar Sakkwato ke yi na ganin ma’aikatan hukumar sun tsare aiki tare da sadaukarwa, mai baiwa gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu Sokoto Shawara a hukumar rage radadin talauci Barista Sa’adatu Yanusa Muhammad ta gabatar da kyautar karramawa ga mutanen da suka fi fitowa aiki a hukumar.
Mutanen sun hada da Lawali Sani da Aminu Abubakar da Umar Muhammad kowanensu ya samu gwargwardon karramawar da ta dace da kwazonsa, a lokacin gabatar da karramawar Barista ta fahimci irin wannan hobbasar za ta zaburar da ma’aikatan ga samar da biyan bukatar da ake da ita a wurin aiki.
A cewar Barista Sa’adatu Gwamnatin Dakta Ahmad Aliyu ta himmatu wurin dawo da karsashin aikin gwamnati da aka rasa a jiha domin ganin an samar da cigaba kan haka ake biyan albashin ma’aikata kan kari.
Barista kan haka ta bukaci ma’aikata a hukumarta da su zama masu tsare aiki a koyaushe domin wannan karramawar da aka soma ta ma’aikata za a cigaba da yinta lokaci bayan lokaci.
Lawali Sani ma’aikaci ne a hukumar kuma yana cikin wadanda suka ci gajiyar karramawar ya yabawa hobbasar mai baiwa Gwamna shawara, kan wannan tunani da ta zo da shi domin hakaan ya dawo da martabar aiki a wurin, don a yanzu mutane na fitowa aiki tun 7:30 sabani baya da suke zuwa aiki karfe 10 na safe.
Ya ce Hajiya ta zo ne domin ta yi aiki in har ta samu goyon bayan gwamna dari bisa dari ba karamin cigaba za a samar a wurin ba.
Sanusi Abubakar E.O ya ce wannan abin ya kara karfafa ma’aikata, fito da tsarin tantance zuwan ma’aikata aiki ta hanyar na’ura da littafi abin yabawa ne ga wannan gwamnati, abin da ake bukata a yanzu a fito da Karin wasu hanyoyi na kyautatawa ma’aikata.
Yusuf Mode ya bayyana farincikinsa da suka samu jajirtarta mace da ta zo domin kawo sauyi da gyara a hukumar domin kafin ta zo wurin ya mutu ba komai kamar in da gwamnati ta manta da shi.
Ya yi kira ga Gwamnan jiha Ahmad Aliyu da ya karfafi Barista Sa’adatu domin sun tabbata in aka ba ta damar aiki lalle za a yi alfahari da damar da aka ba ta domin ta sauya hukumar nan gaba daya ba wani abu da baya aiki a yanzu.
“Kulum za ka samu Hajiya tana ofis ana ta fitowa da shiratuwa da za su taimaki talaka da kawar masa da radadin talauci, na tabbata duk aka fara aiwatar da tsare-tsarenta lalle talaka a Sakkwato zai kara tabbatar da ya zabi gwamnatinsa da ke tausayinsa sabanin in da aka fito a baya da ake daukar mukami a baiwa wadanda ba su cancanta ba, kuma a barsu da dubararsu,”kalaman Yusuf.