Ministan aiyukka David Umahi ya ƙaddamar da wani ɓangaren soma hanya mai tsawon kilomita 258, Sokoto 120 daga cikin kilomita 1000 na hanyar Sokoto zuwa Badagari a Birnin Kebbi.
An kaddamar da aikin ne a masaukin shugaban ƙasa dake Birnin Kebbi, ministan ya ce in an kammala aikin zai bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Wane dalili ne zai sa a kaddamar da irin wannan aikin ba a jihar Sakkwato ba, bayan kuma ita ce ake maganar tushen aikin.
A wurin bukin hoton Gwamnan Sokoto ne kawai amma Gwamna da mataimakinsa ba su halarci taron ba, bayan dimbin muhimmancin da yake da shi, ta hakan ne za su tabbatar da an yi wa Sakkwatawa adalci, akwai bukatar sanin dalilin da ya sa ba a kaddamar da aikin a cikin jihar Sakkwato ba, domin hanayar Lagos zuwa Sakkwato ne, ba Lagos zuwa Birnin Kebbi ba.